brightness_1
Shafa turare Sunna ne
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Anas raliyallahu anhu, wanda ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “An qawata mani abubuwa uku daga cikin qawar duniya: mata da turare; babu kuma lokacin da nake jin daxi kamar lokacin da nake salla.” (Ahmad:12293/ Nasa’i:3940). Albani kuma ya faxa a cikin: Sahíhun- Nasa’i, cewa Hadisi ne kyakkyawa ingantacce.
Amma lafazin Hadisin da ake ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “An qawata mani abubuwa guda uku daga cikin duniyarku,” lafazi ne mai rauni.
Kuma Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yana qyamar aji qanshin wani abu na tashi a jikinsa, wanda ba turare ba. Hujja a kan wannan Sunna kuwa, ita ce, Hadisin nan mai tsawo, wanda Buhari ya fitar, daga Sayyida A’isha raliyallahu anha, inda ta ce: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yana matuqar qyamar aji qanshin wani abu yana tashi daga jikinsa, wanda ba turare ba.” (Buhari:6972). Wato, ya fison duk lokacin da isaka ya bi ta kansa, sallallahu alaihi wa sallam, aji qanshi na tashi
Maruhi ne qin karvar kyautar turare:
Hujja a kan wannan karhanci ita ce, Hadisin Anas raliyallahu anhu, inda ya ce: “Tabbas! Annabi sallallahu alaihi wa sallam bay a mayar da kyautar turare idan an yi masa.” (Buhari:2582).