Yana daga cikin Sunna, idan musulmi zai saka takalminsa ya farad a qafar dama. Haka kuma yana daga cikin Sunna idan zai cire takalmin ya fara cire qafar hagu
Hujja a kan wannan Sunna, ita ce: Hadisin Abu Hurairah raliyallahu anhu da ya ce: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Idan xayanku zai sanya takalmi, to, ya farad a qafar dama. Idan kuma ai cire, ya farad a qafar hagu. Wato, qafar dama ta zama farko sakawa, qarshen kuma cirewa.” (Buhari:5856).
A wata riwayar kuma, ta Imamu Muslimu, cewa ya yi: “Kada xayanku ya kuskura ya yi tafiya da takalmi xaya a qafa. Ko dai ya saka biyun gaba xaya, ko kuma ya cire su gaba xaya.” (Muslimu:2097).
Waxannan Hadisai sun qunshi Sunnoni guda uku:
1/ Farawa da qafar dama idan za a sanya takalmi.
2/ Farawa da qafar hagu idan za a cire takalmi.
3/ Sanya ta kalmi gaba xaya, ko cirewa gaba xaya, ta yadda ba za a yi tafiya da takalme xaya a qafa ba.
Sanya fararen tufafi Sunna ne
Abin da ake nufi da wannan Sunna, shi ne a duk lokaci da mutum zai saka sutura, to, ya fifita fafa. Yin haka Sunna ne. hujja a kan wannan Sunna kumaa, ita ce, Hadisin Abbas raliyallahu anhuma, wanda ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Ku riqa sanya fafare daga cikin tufaffinku, saboda su ne mafifita alhairi daga cikin tufafin naku. Ku kuma ariqa yi wa amamatanku likkafani da su.” (Ahmad:2219/ Abu Dawuda:3878/ Tirmizi:994). Albani kuma ya inganta shi a cikin: “Sahíhul- Jámi’i: (1/267).
Malaminmu Ibn Usaimin rahimahullahu ya ce: “Wannan umarni na Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya shafi gaba xayan nau’ukan tufafin da musulmi zai saka a jiki; Sunna ta fi son fari. Daxa rig ace, ko taguwa, ko wando. Ko ma dai mene ne, matuqar sunansa tufa, to, amfani da fari shi ne Sunna. Yin haka shi ne abu mafifici. Sai dai ko musulmi ya yi amfani da tufan dab a fari xin ba, babu wani laifi a kansa. Sharaxi kawai shi ne, kada ya kasance xaya daga cikin tufafin da Shari’a ta kevance wa mata.” Don qarin bayani ana aiya duba: Sharhu Riyádhus- Sálihína, na Malamin namu: (2/1087)
Shafa turare Sunna ne
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Anas raliyallahu anhu, wanda ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “An qawata mani abubuwa uku daga cikin qawar duniya: mata da turare; babu kuma lokacin da nake jin daxi kamar lokacin da nake salla.” (Ahmad:12293/ Nasa’i:3940). Albani kuma ya faxa a cikin: Sahíhun- Nasa’i, cewa Hadisi ne kyakkyawa ingantacce.
Amma lafazin Hadisin da ake ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “An qawata mani abubuwa guda uku daga cikin duniyarku,” lafazi ne mai rauni.
Kuma Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallamya kasance yana qyamar aji qanshin wani abu na tashi a jikinsa, wanda ba turare ba. Hujja a kan wannan Sunna kuwa, ita ce, Hadisin nan mai tsawo, wanda Buhari ya fitar, daga Sayyida A’isha raliyallahu anha, inda ta ce: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yana matuqar qyamar aji qanshin wani abu yana tashi daga jikinsa, wanda ba turare ba.” (Buhari:6972). Wato, ya fison duk lokacin da isaka ya bi ta kansa, sallallahu alaihi wa sallam, aji qanshi na tashi
Maruhi ne qin karvar kyautar turare:
Hujja a kan wannan karhanci ita ce, Hadisin Anas raliyallahu anhu, inda ya ce: “Tabbas! Annabi sallallahu alaihi wa sallam bay a mayar da kyautar turare idan an yi masa.” (Buhari:2582).
Fara taje gashin kai ta hannun dama Sunna ne
Abin da ake nufi da ‘taje’ gashin kai a wata Hausa, shi ne ‘shacewa.’ To, idan mutum zai yi, Sunna ta ce, ya fara ta hannun dama, sa’annan ya je hagu.
Hujja a kan wannan Sunna:
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Sayyida A’isha raliyallahu anha, inda ta ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance, yana matuqar sha’awar faraway ta dama idan zai sanya takalmi, ko taje kansa, ko tsarki, da sauran gaba xayan sha’anonan rayuwarsa.” (Buhari:168/ Muslimu:267).
Don Saduwa Da Mu
Da Mu
Muna Farin Ciki Da Samun Kiranka Da Tambayoyinka A Kowane Lokaci