languageIcon
search
search
beforeFajronColorIcon / Gabatarwa/ ( Adadinsu 3 Sunnoni )
brightness_1 Misalan Irin Yabba Magabata Suke Kwaxayin Raya Sunna

1/ Imamu Muslimu a cikin ingataccen littafinsa, ya riwaito  Hadisin Nu’umanu xan Salimu, daga Amru xan Ausin raliyallahu anhuma. Ya ce: Anbusatu xan Abu Sufyanu ya ba ni labara, ya ce: Na ji Ummu Habiba tana cewa: Na ji Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Duk wanda ya sallaci raka’a goma a cikin yi da dare, Allah Maxaukakin Sarki zai gina masa gida a cikin Aljanna saboda su.”  [Muslimu: 1727]. Ummu Habibah ta ce: Tun lokacin da na ji wannan magana daga bakin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ban tava ketare rana ban yi waxannan raka’o’i ba. Unbusatu kuma ya ce: Ni kuma tun lokacin da na yi wannan magana daga bakin Ummu Habibah ban tava ketare rana ban yi waxannan raka’o’i ba.

Amru xan Ausin kuma ya ce: Ni ma tun lokacin da na ji wannan magana daga bakin Anbasatu, ban tava ketare rana ban yi waxannan raka’o’i ba.

Nu’umanu xan Salimu kuma ya ce: Ni ma tun lokacin da na ji wannan magana daga bakin Amru xan Ausin, ban tava ketare rana ban yi waxannan raka’o’i ba.

2/ Hadisin Sayyadi Ali raliyallahu anhu, inda ya ce: Wata rana Sayyidah Faximah raliyallahu anha ta je waurin Annabi sallallahu alaihi wa sallam don ta koka masa kantar igiyar guga a hannunta har tana salunta. Ta kama hanya ta tafi, amma ba ta same shi ba sallallahu alaihi wa sallam,  sai ta taras da Sayyidah Aisha raliyallahu anha, ta kuma bat a kabarin abin da yake tahe da ita. Bayan da Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya dawo, sai Sayyidah A’isha raliyallahu anha ta ba shi labarin cewa Faximah kuwa ta zo. Sayyadi Ali raliyallahu anhu y ace gaba da bayar da labara, ya ce: Sai kuwa Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya taso takanas ta kano ya iske mu gida, har mun shiga barci. Mun zabura za mu tahsi, sai Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: Ku yi kwancinku. Sai kuma ya shiga tsakanina da ita ya zauna, har na ji sanyin qafarsa a qirjina. Sa’annan ya ce: “Ko kuna son in karantar da ku abin da ya fi abin kuka tambaye ni zama alhairi? Idan kuma kwanta bacci, ku ce: ‘Allahu Akbar’ qafa talatin da huxu. ‘Subhanallahi’ qafa talatin da uku. ‘Alhamdu lillahi’ qafa talatin da uku. Wannan shi ya fi alhairi a gare ku bisa gab a ku xan aiki.”  [Buhari:3705/ Muslimu:2727]

A cikin wata riwaya kuma aka ce, Sayyadi Ali raliyallahu anhu ya qara da cewa: Tun lokacin da na ji wannan magana daga bakin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, bantava ketare rana ban yi wannan zikiri ba. sai aka tambaye shi cewa, hard a ranar da aka gwabza yaqin basasr Siffain? Ya ce: Tabbas! har da ranar da aka gwabza yaqin Siffain kuwa; ba qetare ba. [Buhari:5362/ Muslimu:2727]

Sanannen abu ne kuwa cewa, wannan rana ta Siffaini a cikinta ne aka gwabza matsanancin yaqin nan na na basasa, wanda kuma shi Sayyadi Ali raliyallahu anhu, shi ne shugaban yaqin, amma. Tattare da haka bai kasa raya wannan Sunna ba.

3/ Xan Umar raliyallahu anhu ya kasance idan ya sallaci gawa, sai kawai ya juya ya tafi abinsa; ba yakan raka ta a rufe ba. A zatonsa yin haka shi ne matuqar raya Sunna, saboda ba shi da labarin irin ladar da take akwai a cikin raka gawa har inda za a rufe ta. To, a daidai lokacin da ya ji Hadisin Abu Hurairata fa raliyallahu anhu, sai ya sami kansa a cikin nadamar kucce masa da wannan Sunna ta yi. Bari ka ji abin day a qara da shi da kyau, ka kuma xan yi batun zuci a kan haka.

Jin wannan Hadisi yake da wuya, sai xan Umar raliyallahu anhu ya daki qasa da tsakuwar da take hannunsa. Sa’annan ya ce: Ashe dai wallahi mun yi sakaci mai tarin yawa. [Buhari:1324/ Muslimu:945]

Imamun-Nawawi rahimahullahu ya ce: “Wannan Hadisi yana karantar da irin yadda Sahabbai suke matuqar kwaxayin xa’a da biyayya tare da raya Sunnar Annabi sallallahu alaihi wa sallam a duk lokacin da suka sami labarinta, da kuma matuqar nuna damuwa da vacin ransu a kan Sunnar duk da ta kuvuce musu, ba su aikata ba, tattare da cewa, ba su da masani da ita, balle matsayinta.” Din qarinj bayani sai a duba littafin ‘Alminhaju, (7:15)

brightness_1 Wasu Daga Cikin Kyawawan Sakamakon Raya Sunna

Biyayya da raya Sunna, ya kai xan’uwana musulmi! Yana da kyawawan sakamako masu yawa. Ga kaxan daga cikinsu:

1/ Taka Matakin Soyayya:  Neman kusanci ga Allah Maxaukakin Sarki ta hanyar raya Sunnar ayyukan nafila, na sa Allah Maxaukakin ya so, ya kuma qaunaci bawansa.

Malam Ibn Qayyimu Aljauziyyah rahimahullahu ya ce: Allah Maxaukakin Sarki ba zai so bawa ya kuma qaunace shi ba, sai idan ya yi biyayya ga masoyinsa sallallahu alaihi wa sallam zahiri da baxini, ya kuma gaskata duk labarin da ya bayar. Sa’annan ya yi biyayya ga duk umarnin da ya yi; ya kuma karva duk kiran da ya yi; ya kuma fifita shi sallallahu alaihi wa sallam,  a kan komai, cikin daxin rai. Sa’annan ya ajiye hukuncin kowa, da sonsa da xa’a gare shi, saboda hukuncin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, da so da kuma xa’arsa. Matuqar kuwa ba haka bawa ya zama ba, to, kar ma ya wahalar da kansa. Mafi zama alhairi a gare shi, shi ne tsayawa inda yake. Sa’annan ya nemi wani hasken na daman ba wabbab ba, saboda shi, ba kowa ne ba a wannan halarah. 

2/ Samun Kusanci Ga Allah  Maxaulalkin Sarki: raya Sunnonin Annabi sallallahu alaihi wa sallam,  na sa Allah Maxaukakin Sarki ya yi wa bawansa gamon katari da kowane irin alhairi. A haka sai a wayi gari, babu wani aiki da gavovinsa za su aikata, face wanda yake faranta ran Ubangijinsa mai girma da xaukaka. Dalili kuwa shi ne, duk inda soyayya ta samu gindin zama, to, za a sami matuqar kusanci.

3/ Karva Addu’ah: Raya Sunna na sa Allah Maxaukakin Sarki ya so musulmi, matuqar so, ta yadda duk lokacin da ya xaga hannu, ya roqe shi subhanahu wa ta’alah zai sami biyan bukata. Duk wanda ya nemi kusanci ga Allah Maxaukakin Sarki ta hanyar raya wasu Sunnoni na nafila, allah Maxaukakin Sarki zai so shi. Wanda kuma duk ya sami taka wannan matsayi, to, addu;arsa ba za ta tava faxuwa qasa banza ba.

Hujja a Kan Waxannan Nasarori Guda Uku:

Hadisin Abu Hurairata raliyallahu anhu, inda ya ce: Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Tabbas! Allah Maxaukakin Sarki ya ce: Duk wanda ya qulla yaqi da masoyina, to, na umarce shi da ya yi shirin yaqi da ni. Bawana ba zai nemi kusanci zuwa gare ni ba, ta hanyar wani abu kamar abubuwan da na farlanta masa. Haka nan bawana ba zai gushe ba yana neman kusanci zuwa gare ni ta hanyar nafilfili, har sai na so shi. To, idan fan a so shi, zan zama jinsa wanda yake ji da shi; da ganinsa wanda yake gani da shi; da hannunsa wanda yake riqo da shi; da qafarsa wadda yake tafiya da ita. Idan kuma ya roqe ne, wallahi zan ba shi. Idan kuma ya nemi tsarina, wallalhi zan tsare shi. Ba na kuma tava kaiwa da komowa; in fasa aikata wani abu kamar yadda nake kaiwa da komowa daga tava ran wani mumini, da yake tsoron  mutuwa kamar yadda nake qin in sava masa.” [Buhari:6502]

4/ Cike Gurbin Givin Farilloli:  Raya Sunnar Annabi sallallahu alaihi wa sallam ta hanyar tsare aikata nafilfili yana cike gurbin givin da aka samu a cikin ayyuka na farilla.

Hujja a Kan Wannan Nasara Ita ce:

Hadisin Abu Hurairata raliyallahu anhu, inda ya ce: Na ji Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Ko shakka babu! Farkon  abin da za a yi wa bawa hisabi a kansa ranar Qiyama, daga cikin ayyukansa, shi ne sallarsa. Idan ta inganta, to, ya tsira ya kuma yi nasara. Idan kuwa ta vaci, to, ya tave ya kuma yi hasara. Idan kuma aka sami wani givi a cikin ayyukansa na farillah, sai Allah Maxaukakin Sarki ya ce wa makal’iku: Ku buda ko bawan nan nawa yana da wasu ayyuka na nafila? Domin a cika masa givin da yake da shi a cikin ayyukansa na farilla. Sa’annan a bi gaba xayan ayyukansa kamar haka.” [Ahmad:9494/ Abu dawuda:864/ Tirmizi:413] Albani kuma ya inganta wannan Hadisi. [Sahihul-Jami’u: 1/405]