Nafilar da akan yi kafin sallar Safe, ita ce Sunna ta farko wadda ake musulmi kan raya kullum, tana kuma da Sunnoni da dama a tatter da ita. Kafin mu shiga gadan-gadan a cikin bayanin wannan salla ta nafila, ya zama wajibi mu yi wa hakan shimfixa da bayyana waxansu abubuwa da suka shafi irin waxannan salloli na nafila da akan yi kafi da bayan sallolin farilla. Idan aka ce ‘sunanur-rawátib’ a Larabce, to, ana nufin waxannan salloli na nafila, waxanda ake yi koda yaushe, tare da salloli na farilla, waxanda kuma raka’a goma sha biyu ne.
Hujja a kan waxannan Sunnoni ita ce, Hadisin Ummu Habiba raliyallahu anha, inda tace: “Na ji Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Duk wanda ya sallaci raka’a goma sha biyu tsakanin yini da dare, za a gina masa, a sanadiyyarsu, gida a cikin Aljanna.” (Muslimu:728). Tirmizi kuma ya fitar da Hadisin, ya kuma qara da cewa: “..raka’a huxu kafin sallar Azahar, biyu bayanta, biyu bayan Magariba, biyu bayan Isha’i, da biyu kafin Asubah.” (Tirmizi:415), ya kuma ce: Hadisi ne kyakkyawa kuma ingantacce.”
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Zaidu raliyallahu anhu, inda ya ce, Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Ku yi salla a cikin gidajenku ya ku mutane! Haqiqa, mafificiyar sallar da mutum zai yi, ita ce wadda ya yi a cikin gidansa, amma, ban da ta farilla.” (Buhari:7290/ Muslimu:781).
Mafi qarfi daga cikin waxannan nafilfili ita ce, wadda ake yi kafin sallar Asubah. Hujja a kan haka kuwa ita ce:
i) Hadisin Sayyidah A’isha raliyallahu anha, inda ta ce: “Babu wata salla ta nafila, da na fi tsare alfarma da mutuncinta kamar raka’o’i biyu da ake yi kafin sallar Asubah.” (Buhari:1196/ Muslimu:724).
ii) Hadisin Sayyidah A’isha raliyallahu anha, daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam, ya ce: “Raka’o’in kafin sallar safe sun fi alhairi a kan duniya da abin duk da yake cikinta.” (Muslim:725).
Raka’o’in kafin sallar safe suna tattare da abubuwa masu yawa:
Lokacinta: Shari’a ta xora wa musulmi nauyin yin wannan salla ta nafila a lokacin da yake cikin halin tafiya da na zaman gida. Savanin sauran nafilfilin na Sunna, kamar na sallar azahar, da Magariba, da Isha’i. Su kam waxannan, Sunna cewa ta yi, kada a yi su a lokacin da ake cikin halin tafiya.
Raka’o’in kafin sallar safe suna tattare da abubuwa masu yawa:
Ladarta: Ladar wannan salla ta nafila, ita ce kasancewar ta fi duniya da abin da yake cikinta matsayi a wurin Allah, kamar yadda bayani ya gabata.
Raka’o’in kafin sallar safe suna tattare da abubuwa masu yawa:
Yanayinta: Sunna ce idan za a yi wannan salla ta nafila, kada a tuqaqe raid a kai.
Hujja a kan wannan Sunna ta rashin tsanatawa a cikin wannan nafila, ita ce, Hadisin Sayyidah A’isha raliyallahu anha, inda take cewa: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yana sassauta nafilolin kafin sallar Asubahin, har wata rana nakan ce masa: Shin kana ma ko karance fatiha a cikin wannan salla kuwa, koko?” (Buhari:1181/ Muslimu:724).
Sai dai sharaxi ne: Kada wannan sassautawa da za a yi ta hana wajibban sallar cika da kamala, ta yadda mai sallar zai riqa yin qoton kurciya, har ya faxa a cikin abin da aka hana.
Raka’o’in kafin sallar safe suna tattare da abubuwa masu yawa:
Karatunta: Abin da aka fi so a Sunna, shi ne idan za a yi wannan nafila ta kafin sallar Asubah, bayan an qare karantun Fatiha a cikin raka’a ta farko, to, a karanta: {Qul ya ayyuhal-káfiruna}, a cikin ta biyu kuma: {Qul Huwalláhu Ahad}. Hujja a kan wannan Sunna kuwa ita ce, Hadisin Abu Hurairata raliyallahu anhu na wajjen Imamu Muslimu. Ko kuma bayan Fatiha xin nan, a cikin raka’ar farko xin, ya karanta: {Qúlú ámanná billáhi, wa má unzila ilainá, wa má unzila ilá Ibráhima, wa Ismá’ila, wa Ya’aqúba, wal’asbáxi, wa má útiya Musa wa Isah, wa má útiyan-nabíyúna min Rabbihim. Lá nufarriqu baina ahadin minhum, wa nahnu lahú muslimúna.” [Taubah:136].
A cikin raka’a ta biyu kuma ya karanta: {Qul ya ahlal-kitábi ta’álau ilá kalimatin sawá’in bainaná wa bainakum, allá na’abuda illalláh, wa lá nushrika bihí shai’an, wa lá yattakhiz ba’adhaná ba’adhan arbában min dúnilláh. Fa in tawallau faqúlush-hadú bi’anná muslimún.} [Áli-imran:52]. Hujja a kan wannan Sunna kuwa ita ce, Hadisin xan Abbas raliyallahu anhu, a wajen Imamu Muslimu. Wannan Sunna tana daga cikin Sunnonin da suka tuzgo a cikin sigogi daban-daban a kuma lokuta daban-daban.
Raka’o’in kafin sallar safe suna tattare da abubuwa masu yawa:
Qarshenta: Sunna ne idan mutum ya kammala waxannan raka’o’i na kafin sallar Asuba, ya xan gincira a kan hannunsa na dama, kaxan.
Hujja a kan wannan Sunna:
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Sayyida A’isha raliyallahu anha, inda ta ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance, idan ya qare nafilar kafin sallar Asuba, yakan xan gincira a kan hannunsa na dama.” (Buhari:1160/ Muslimu:736).
Sunna ne mutum ya ci gaba da zama a cikin Masallaci bayan qare sallar Asuba, har zuwa lokacin da rana ta hudo. Akwai tanadin da Sunna ta yi wa irin wannan zama sun haxa. Hujja kuma a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Jabiru xan Sumairata raliyallahu anhu, cewa: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance, idan ya qare sallar Asuba, yakan ci gaba da zama a cikin Masallaci har zuwa lokacin da rana ta hudo sosai.” (Muslimu:670).