brightness_1
Wasu Daga Cikin Kyawawan Sakamakon Raya Sunna
Biyayya da raya Sunna, ya kai xan’uwana musulmi! Yana da kyawawan sakamako masu yawa. Ga kaxan daga cikinsu:
1/ Taka Matakin Soyayya: Neman kusanci ga Allah Maxaukakin Sarki ta hanyar raya Sunnar ayyukan nafila, na sa Allah Maxaukakin ya so, ya kuma qaunaci bawansa.
Malam Ibn Qayyimu Aljauziyyah rahimahullahu ya ce: Allah Maxaukakin Sarki ba zai so bawa ya kuma qaunace shi ba, sai idan ya yi biyayya ga masoyinsa sallallahu alaihi wa sallam zahiri da baxini, ya kuma gaskata duk labarin da ya bayar. Sa’annan ya yi biyayya ga duk umarnin da ya yi; ya kuma karva duk kiran da ya yi; ya kuma fifita shi sallallahu alaihi wa sallam, a kan komai, cikin daxin rai. Sa’annan ya ajiye hukuncin kowa, da sonsa da xa’a gare shi, saboda hukuncin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, da so da kuma xa’arsa. Matuqar kuwa ba haka bawa ya zama ba, to, kar ma ya wahalar da kansa. Mafi zama alhairi a gare shi, shi ne tsayawa inda yake. Sa’annan ya nemi wani hasken na daman ba wabbab ba, saboda shi, ba kowa ne ba a wannan halarah.
2/ Samun Kusanci Ga Allah Maxaulalkin Sarki: raya Sunnonin Annabi sallallahu alaihi wa sallam, na sa Allah Maxaukakin Sarki ya yi wa bawansa gamon katari da kowane irin alhairi. A haka sai a wayi gari, babu wani aiki da gavovinsa za su aikata, face wanda yake faranta ran Ubangijinsa mai girma da xaukaka. Dalili kuwa shi ne, duk inda soyayya ta samu gindin zama, to, za a sami matuqar kusanci.
3/ Karva Addu’ah: Raya Sunna na sa Allah Maxaukakin Sarki ya so musulmi, matuqar so, ta yadda duk lokacin da ya xaga hannu, ya roqe shi subhanahu wa ta’alah zai sami biyan bukata. Duk wanda ya nemi kusanci ga Allah Maxaukakin Sarki ta hanyar raya wasu Sunnoni na nafila, allah Maxaukakin Sarki zai so shi. Wanda kuma duk ya sami taka wannan matsayi, to, addu;arsa ba za ta tava faxuwa qasa banza ba.
Hujja a Kan Waxannan Nasarori Guda Uku:
Hadisin Abu Hurairata raliyallahu anhu, inda ya ce: Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Tabbas! Allah Maxaukakin Sarki ya ce: Duk wanda ya qulla yaqi da masoyina, to, na umarce shi da ya yi shirin yaqi da ni. Bawana ba zai nemi kusanci zuwa gare ni ba, ta hanyar wani abu kamar abubuwan da na farlanta masa. Haka nan bawana ba zai gushe ba yana neman kusanci zuwa gare ni ta hanyar nafilfili, har sai na so shi. To, idan fan a so shi, zan zama jinsa wanda yake ji da shi; da ganinsa wanda yake gani da shi; da hannunsa wanda yake riqo da shi; da qafarsa wadda yake tafiya da ita. Idan kuma ya roqe ne, wallahi zan ba shi. Idan kuma ya nemi tsarina, wallalhi zan tsare shi. Ba na kuma tava kaiwa da komowa; in fasa aikata wani abu kamar yadda nake kaiwa da komowa daga tava ran wani mumini, da yake tsoron mutuwa kamar yadda nake qin in sava masa.” [Buhari:6502]
4/ Cike Gurbin Givin Farilloli: Raya Sunnar Annabi sallallahu alaihi wa sallam ta hanyar tsare aikata nafilfili yana cike gurbin givin da aka samu a cikin ayyuka na farilla.
Hujja a Kan Wannan Nasara Ita ce:
Hadisin Abu Hurairata raliyallahu anhu, inda ya ce: Na ji Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Ko shakka babu! Farkon abin da za a yi wa bawa hisabi a kansa ranar Qiyama, daga cikin ayyukansa, shi ne sallarsa. Idan ta inganta, to, ya tsira ya kuma yi nasara. Idan kuwa ta vaci, to, ya tave ya kuma yi hasara. Idan kuma aka sami wani givi a cikin ayyukansa na farillah, sai Allah Maxaukakin Sarki ya ce wa makal’iku: Ku buda ko bawan nan nawa yana da wasu ayyuka na nafila? Domin a cika masa givin da yake da shi a cikin ayyukansa na farilla. Sa’annan a bi gaba xayan ayyukansa kamar haka.” [Ahmad:9494/ Abu dawuda:864/ Tirmizi:413] Albani kuma ya inganta wannan Hadisi. [Sahihul-Jami’u: 1/405]