brightness_1
Abin da aka fi so a Sunna, shi ne idan za a yi wannan nafila ta kafin sallar Asubah, bayan an qare karantun Fatiha a cikin raka’a ta farko, to, a karanta: {Qul ya ayyuhal-káfiruna}, a cikin ta biyu kuma: {Qul Huwalláhu Ahad}
Raka’o’in kafin sallar safe suna tattare da abubuwa masu yawa:
Karatunta: Abin da aka fi so a Sunna, shi ne idan za a yi wannan nafila ta kafin sallar Asubah, bayan an qare karantun Fatiha a cikin raka’a ta farko, to, a karanta: {Qul ya ayyuhal-káfiruna}, a cikin ta biyu kuma: {Qul Huwalláhu Ahad}. Hujja a kan wannan Sunna kuwa ita ce, Hadisin Abu Hurairata raliyallahu anhu na wajjen Imamu Muslimu. Ko kuma bayan Fatiha xin nan, a cikin raka’ar farko xin, ya karanta: {Qúlú ámanná billáhi, wa má unzila ilainá, wa má unzila ilá Ibráhima, wa Ismá’ila, wa Ya’aqúba, wal’asbáxi, wa má útiya Musa wa Isah, wa má útiyan-nabíyúna min Rabbihim. Lá nufarriqu baina ahadin minhum, wa nahnu lahú muslimúna.” [Taubah:136].
A cikin raka’a ta biyu kuma ya karanta: {Qul ya ahlal-kitábi ta’álau ilá kalimatin sawá’in bainaná wa bainakum, allá na’abuda illalláh, wa lá nushrika bihí shai’an, wa lá yattakhiz ba’adhaná ba’adhan arbában min dúnilláh. Fa in tawallau faqúlush-hadú bi’anná muslimún.} [Áli-imran:52]. Hujja a kan wannan Sunna kuwa ita ce, Hadisin xan Abbas raliyallahu anhu, a wajen Imamu Muslimu. Wannan Sunna tana daga cikin Sunnonin da suka tuzgo a cikin sigogi daban-daban a kuma lokuta daban-daban.