Idan Aka ce Wane Lokaci ne Mafifici ga Mai Sallar Dare? Amsa ita ce: Kamar yadda aka sani
cewa, lokacin sallar Wuturi yana faraway ne daga bayan sallar Isha’i har zuwa hudowar alfijiri. Kenan lokacin sallar Wuturi shi ne tsakanin sallar Isha’i da sallar Asuba. Hujja a Kan Wannan Magana: Hujja a kan wannan magana ita ce, Hadisin Sayyida A’isha raliyallahu anha, da ta ce: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yana sallatar raka’a goma sha xaya, tsakanin lokacin da ya qare sallar Isha’I zuwa sallar Asuba, inda yakan sallame bayan kowace raka’a biyu, sa’annan ya yi raka’a xaya a matsayin Wuturi.” (Buhari:2931/ Muslimu:736). Amma Lokacin da ya fi dacewa da Yin Sallar Dare Shi ne Tsakiyar Sulusin Dare na Biyu. Abin da ake nufi a nan shi ne, mutum ya raba dare kahsi biyu, ya yi sallalrsa a cikin sulusin kasha na biyu. Qarshen dare kuma sai ya kwanta ya yi bacci abinsa. Ma’ana, zai yi sallar kenan a cikin kasha xaya daga cikin shida na dare; a cikin kasha na huxu da na shida. Kasha na shida kuma ya yi ta bacci abinsa. Hujja a kan wannan Sunna kuwa, ita ce Hadisin Abdullahi xan Amru raliyallahu anhuma, wanda ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Haqiqa, mafi soyuwar azumi a wurin Allah, shi ne azumin Annabi Dawuda. Mafi soyuwar sallah kuma a wurin Allah, ita ce sallar Annabi dawuda alaihissalamu. Domin ya kasance yana kwantawa tsawon rabin dare ya yi bacci. Sa’annan ya tashi ya yi salloli a cikin sulusinsa. A cikin sauran sudusinsa kuma ya sake kwantawa ya qara yin bacci. Ta vangaren azumi kuma, yana yi ne yau ya sha ruwa gobe.” (Buhari:3420/ Muslimu:1159). - To, idan mutum yana son ya raya wannan sunna, ya zai gane wannan lokaci na dare? Zai fara lissafi da neman gane wannan lokaci ne, daga lokacin da rana ta faxi, zuwa lokacin da alfijiri ya keto. Sa’annan ya karkasa wannan tsakani zuwa gida shida. Kashi uku na farko su ne matsayin bain wannan dare na farko. Sai ya tashi ya yi sallolinsa a cikin kashin da yake bi ma wannan, wato, na huxu da na biyar, domin matsayin kasha xaya bisa uku suke na daren. Sa’annan ya sake kwantawa ya qara yin bacci a cikin kasha na shida; na qarshe. Saboda haka ne Sayyida A’ishatu ta ce: “Ban tava ganin rashin bacci ya tuqaqe Annabi sallallahu alaihi wa sallam ba, domin yana bacci isasshe.” (Buhari:1133/ Muslim:742). Idan musulmi ya kiyaye wannan hanya ta qididdiga, to, babu lokacin da zai tashi cikin dare domin yin salla, face ya dace da lokaci mafifici, kamar dai yadda Hadisin can na Abdullahi xan Amru raliyallahu anhu, da ya gabata, ya bayyana. A taqaice dai, zancen fifiko a cikin lokacin yin sallar dare, da yadda aka fi son musulmi ya yi, mataki uku yake: Mataki Na Farko: Abin da ake so a wannan mataki na farkon rabin dare, shi ne mutum ya kwanta ya yi bacci abinsa. Sa’annan ya kuma sake kwantawa a cikin kashi aya na qarshe daga cikin shida, ya yi wani baccin, kamar dai yadda bayani ya gabata. Hujja a kan wannan Sunna kuwa ita ce, Hadisin Amru xan Asi raliyallahu anhu, wanda ya gabata xazu kaxan. Mataki Na Biyu: A wannan mataki kuma sai ya tashi ya yi sallolinsa a cikin kashi xaya bisa uku na qarshen dare. Hujja a kan wannan Sunna: Hujja a kan wannan Sunna kuma, ita ce Hadisin Abu Hurairata raliyallahu anhu, cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Ubangijinmu mai girma da xaukaka yakan sauko zuwa samar nan ta duniya a cikin kowane dare, daidai lokacin da sulusin dare na qarshe ne ya rage. Sai ya ce: Ina wanda yake da bukata, ya roqe ni, in karva masa? Ina wanda yake son wani abu, ya koka mani, in share masa hawaye? Ina wanda yake neman gafarata, in gafarta masa?” (Buhari:1145/ Muslim:758). Haka nan kuma Hadisin Jabiru raliyallahu anhu, wanda za zo nan gaba. Shi ma hujja ne a kan wannan Sunna. Idan kuma mutum yana tsoro da fargaban, kada ya kasa tashi a qarshen dare. To, yana iya yi sallarsa a farkonsa, ko a cikin kowane yanki ma na daren ya sami dammar hakan. Wannan shi ne mataki na uku. Mataki Na Uku: Kamar yadda aka faxa a sama, wannan mataki ya qunshi, yin sallar a farkon dare, ko a cikin duk lokacin da dama ta samu ga mutum. Hujja a kan wannan Uzuri: Hujja a kan wannan uzuri da dama kuwa ita ce, Hadisin Jabiru raliyallahu anhu, inda ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Duk wanda ya ji tsoro ba zai iya tashi qarshen dare domin yin Wuturoba, to, ya yi abinsa tun a farkon dare. Wanda kuma yake da tabbacin zai iya tashi a qarshen nasa, to, ya bari sai qarshen dare, sa’annan ya yi. Saboda salla a qarshen dare abar halarta ce. Wannan kuwa shi ne mafifici.” (Muslim:755). Wani dalili kuma da yake iya zama hujja a kan wannan uzuri, shi ne wasiccin da Annabi sallallahu alaihi wa sallam, ya yi wa Abi Zarrin, wanda Imamun-Nasá’í ya riwaito a cikin: Sunann-Kubra(2712), Nsiruddil-Albáni kuma ya ainganta shi a cikin: Assahíhah (1433), da kuma Abud-Darda’i, riwayar Ahmad: 27471, wadda kuma Albáni ya ingantata ta (Sahihu Abu Dawuda: 5/177), da Abu Hurairata raliyallahu anhu, riwayar Muslim: 737). Kowacce daga cikin waxannan riwayoyi cewa suke yi: “Badaxayina ya yi mini wasicci da abubuwa guda uku…” daga cikinsu ya ambaci cewa: “… da kuma in sallaci Wuturi kafin in shiga bacci.”
Yin raka’a goma sha xaya xin nan, shi ne mafi cika da kamalar mizanin sallar dare. Hujja kuwa a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Sayyidah A’isha raliyallahu anha, da ta tabbata cewa, ta ce: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam bai tava wuce raka’a goma sha xaya ba, a cikin watan Ramalana ko waninsa.” (Buhari:1147/ Muslim:738). An kuma samo a wata riwaya ta Imamu Muslimu a cikin ingantaccen littafinsa, daga cikin hadisan Sayyidah A’isha raliyallahu anha cewa, Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya tava yin raka’a goma sha uku. Waxannan riwayoyi guda biyu kuma, ba komai suke nunawa ba, illa halascin qin tsayawa a kan adadi xaya na sallar wuturi. Amma dai, mafi rinjayen adadin da Annabi sallallahu alaihi wa sallam yakan sallata shi ne raka’a goma sha xaya. An kuma sami wani lokaci da ya yi raka’a goma sha uku. Da wannan bayani, mun haxa hancin waxannan riwayoyi biyu kenan.
Fara sallar dare da addu’ar da Annabi yake farawa da ita, yana daga cikin Sunna: Daga cikin waxannan addu’o’i akwai: i. Wadda ta zo a cikin ingantaccen littafin Imamu Muslim daga cikin Hadisan Sayyidah raliyallahu anha, inda ta ce: Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance, idan ya tsahi zai yi salla a cikin dare, yakan buxe sallar da wannan du’a’i: “Alláhumma rabba Jibríla, wa Míká’íla, wa Isráfíla. Fáxiras-samáwáti wal-ardhi, álimal-gaibi wash-shahádati. Anta tahkumu baina ibádika fímá kánú fíhi yakhtalifúna. Ahdiní limakh-tulifa fíhi minal-haqqi bi’iznika. Innaka tahdí man tashá’u ilá siráxil-mustaqíma.” (Ya Ubangijina! Ubangijin Jibrila, da Mika’ila, da Israfilu, mahaliccin sammai da qasa, Masanin voye da bayyane. Kai kake hukunci tsakanin bayinka a cikin abin da suka kasance suna savawa a cikinsa. Ka shiryar da ni kar in faxa a cikin abin da suka sava a cikinsa na gaskiya. Lalle haqiqa, kai, kana shiryar da duk wanda ka so zuwa ga tafarki madaidaici.” (Muslim:770). ii. Wata hujjar kuma ita ce, abin day a zo a cikin ingantattun littafan Buhari da Muslim, daga cikin Hadisan xan Abbas raliyallahu anhuma, ya ce: Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance ida zai yi sallar tahajjudi a cikin dare, yakan farad a karanta wannan du’a’i: “Allahumma lakal-hamdu. Anta nurus-samáwáti wal’ardhi. Wa lakal-hamdu, anta Qayyimussamáwáti wal-ardh. Wa lakal-hamdu anta rabbussamáwáti wal’ardhi wa man fí hinna. Antal-haqqu, wa wa’adukal-haqqu, wa qaulukal-haqqu, wa liqá’ukal-haqqu, wal-jannatu haqqun, wan-náru haqqun, waninabíyúna haqqun, was-sá’atu haqqun. Alláhumma laka aslamtu, wa bika ámantu, wa alaika tawakkaltu, wa ilaika anabtu, wa bika khásamtu, wa ilaika hákamtu. Fagfirlí má qaddamtu wa má akkhartu, wa má asrartu, wa má a’alantu. Anta iláhí lá iláha illá anta.” (Ya Ubangijina! Godiya ta tababata gare ka. Kai ne shaken sammai da qasa. Kuma godiya ta tabbata gare ka, kai ne qashin bayan sammai da qasa. Gosiya kuma ta tabbata gare ka, kai ne Ubangijin sammai da qasa da abin da yake a cikinsu. Kai gaskiya ne, alqawalinka kuma gaskiya ne, zancenka kuma gaskiya ne, haxuwa da kai kuma gaskiya ne. Aljanna gaskiya ce, Wuta kuma gaskiya ce. Annabawa gaskiya ne, tashin Qiyama gaskiya ne. Ya Ubagijina! Zuwa gare ka na miqa wuya, da kai kuma na yi imani, gare ka kuma na dogara, wurinka kuma na sami mafaka. Kai ne tsakanina da duk wanda nake jayayya da shi. A kutunka nake kai qara. Ka gafarta mani laifukan da na gabatar, da waxanda na jinkirtar, da abin da na voye da wanda na bayyana. Kai ne Ubangijina! Babu wani abin bauta bayan kai.” (Buhari:7499/ Muslim:768 ).
i. An so mutum ya karanta ayoyin Alqur’ani daki-daki; yana yi yana shexawa. Ma’ana, kada ya shiga korawa da kwarara su kamar jirgin qorai, ko ya yi ta firgar su kamar ana figar gashin xan tsako. ii. An so ya riqa yi yana yanke tsakanin aya da aya. Wato, idan ya karanta aya xaya, ya saurara kaxan, sa’annan ya xauki ta gaba gar eta; kada yah axe ayoyi biyu ko uku ya karanta su da shexa xaya; ba tare da ya ya da zango a kan gavovinsu ba. A maimakon haka, so ake yi, lalle, sai ya tsaya a kan gavar kowace aya. iii. An so kuma idan yah au kan wata aya ya sauka, wadda magana a kan tasbíhí, to, ya xan dakata kaxan ya yi shi. Idan kuma wadda take magana ne a kan wata siga ta tambaya, to, ita ma ya xankarva wannan tambaya. Idan kuma ya shuxe a kan ayar da take qunshe da neman tsari, to, an so ita ma, ya xanfurka kalmomin neman tsarin. Hujja a kan Waxannan Sunnoni: Hujja a kan gaba xayan waxannan Sunnoni da suka gabata ita ce, Hadisin Huzaifa raliyallahu anhu, inda ya ce: “Wata dare na yi salla bayan Annabi sallallahu alaihi wa sallam, sai kawai na ji ya farad a Surar Baqara. Na ce, to, wata qil idan ya canye aya xari a cikinta, zai yi ruku’u. Sai kawai na ji ya wuce. Na ce, to, wata qil yana nufin ne zai karance ta a cikin wannan raka’a. Sai kuma ya wuce abinsa. Na ce, to qila har cikin ruku’u ita zai ci gaba da karantawa. Ah! Kaiwa qarshenta yake da wuya sai kawai kuma na ji ya yaye kallabin SuratunNisá’i, ya kuma karance ta duka. Sa’annan ya buxe Ali-imrána, ita ma ya kamala ta; yana yi yana karantawa daki-daki. Idan kuma ya kawo kan wata aya, wadda take qunshe da tasbíhí, sai in ji ya yi tasbihi xin. Idan kuma ya kai kan wadda ke qunshe da wata tambaya, sai kuma na ji ya karva tambayar. Idan kuma wadda take qunshe da wata siga ta neman tsar ice, sai in ji ya nemi tsarin. Sa’annan sai ya sunkuya zuwa ruku’i. cana a cikin ruku’in kuma, sai na ji yana cewa: “Subhána rabbiyal’azim wa bi hamdihi.” Da rukun nan nasa sallallahu alaihi wa sallam, da tsayuwar karatun can, ban san wanda ya fi wani tsawo ba. Sa’annan can, sai na ji ya ce: “Sami’alláhu liman hamidah.” Da ya taso xin kuma, said a ya xauki lokaci mai tsawo kwatankwacin tsawon ruku’un can nasa sallallahu alaihi wa sallam. Sa’annan ya surmuya ya rungumi qasa domin yin sujada, ya kuma karanta: “Subhána Rabbiyal a’alá.” Ita ma sujudar nan tasa, kaxan ya rage tsawonsu ya zo daidai da na tsayuwarsa sallallahu alaihi wa sallam” (Muslimu:772). Wata hujjar kuma ita ce, abin da Imamu Ahmad raliyallahu anhu ya riwaito a cikin musnadinsa, daga cikin Hadisan Ummu Salma raliyallahu anha, cewa, an tava tambayarta a kan yadda Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yake karanta Alqur’ami mai girma. Sai ta bayar da amsa da cewa: Ya Kasance yana ya da zango a qarshen kowace aya idan yana karatun Alqur’ani, kamar haka: [Bismilláhir-Rahmánir-Rahím @Alhamdu Lilláhi Rabbil-álamín@ Ar-Rahmánir-Rahím@ Máliki Yaumid-dín] (Ahmad:26583). Imamul-qurxabi kuma ya bayar da shaidar cewa, danganen wannan Hadisi ingantacce ne, saboda gaba xayan mazajensa amintattu ne. Sa’annan kuma Imamun-nawawi ya ainganta shi a cikin: (Almajmú’u:3/333).
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, abin da aka samo daga xan Umar, wanda ya ce: “Wata rana wani mutum ya tashi, ya ce: Ya Manzon Allah! Yaya ake yin sallar cikin dare? Sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya karva masa da cewa: “Ana sallar dare ne raka’a biyu-biyu. Idan kuma kana cikin yi, ka ji tsoro ketowar alfijiri, to, sai ka sallame bayan raka’a xaya.” (Buhari:990/ Muslimu:749). Abin da ake mufi da ‘raka’a biyu-biyu’ xin nan kuma shi ne, zuba raka’ao’in sallar a cikin tsari na sallamewa duk bayan raka’a biyu. Ba a son a haxa hancin raka’o’i huxu cir a lokaci xaya, sa’annan a sallame.
Wato, mutum ya karanta: {Sabbisma Rabbikal-a’alá}, a cikin raka’a ta farko daga cikin ukun nan. A cikin raka’a ta biyu kuma, ya karanta: {Qul Yá’ayyuhalikáfirún!}, a cikin ta uku kuma ya karanta: {Qulhuwalláhu Ahad} kawai. Hujja a Kan Wannan Sunna: Hujja a kan wannan Sunna kuma ita ce, Hadisin Ubayyu xan Ka’abu raliyallahu anhu, wanda ya ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yakan karanta: {Sabbisma Rabbikal-a’alá} da {Qul Yá’ayyuhalikáfirún!} da {Qulhuwalláhu Ahad} (Abu Dawuda:1422/ Nasá’í:1732/ Ibn Majah:1171). Imamun-nawawi kuma ya ainganta shi a cikin: Alkhulah:556. Haka nan shi me Albání ya ainganta shi a cikin: Sahíhun-nisá’í:1/273)
Abin da ake nufi da ‘alqanuti’ shi ne ‘addu’a’ a cikin raka’a ta qarshe, wadda ake karanta
Suratul-ikhlási. Yin addu’a a cikin sallar Wuturi xin nan, wato ‘alqanuti’ yana daga cikin Sunna kamar yadda aka ambata a sama. Tarihi ya tabbata da Annabi sallallahu alaihi wa sallam, yakan yi ta wani lokaci, wani lokaci kuma ya share. An kuma sami tabbacin haka ne sakamakon yadda aka sami labarin cewa, wasau daga bakin Sahabbai raliyallahu anhum suna yi. Imamu Ibn Taimiyyah rahimahullahu kuma ya tafi a kan cewa, yin haka shi ne mafifici. Amma, an fi son rashin yin ya fi yin yawa. Mas’alah: To, ko mutum an so mutum ya xaga hannuwansa a yayin wannan du’ai? Ingan tattar magana, wadda aka cirato daga bakunan manyan malamai rahimahumullahu, ita ce, an so mutum ya xaga hannuwansa sama a lokacin da yake wannan du’a’i. An yanke wannan hukunci ne kuma sakamakon yadda ta tabbata Annabi sallallahu alaihi wa sallam yana yin haka, daga bakin xan Umar raliyallahu anhu, kamar yadda yake a wurin Baihaqi, wanda kuma ya inganta shi. Ga abin da Imamul-baihaqin rahimahullahu yake cewa: “Da yawa daga cikin Sahabbai raliyallahu anhum, sukan xaga hannuwansu a lokacin da suke alqunútí. Domin qarin bayani saia duba: As-sunanul-kubrá: 1/211. Mas’alah: Da wane abu ne ya kamata mutum ya fara alqunutinsa na Wururi? Zance karvavve a tsakanin malamai, shi ne farawa da zuba kalmomin yabo da godiya ga Allah Maxaukakin Sarki. Sa’annan a yi wa hakan rakiya da salati ga Annabi sallallahu alaihi wa sallam. Bayan haka mum ya shiga isar da bukatunsa ga Allah Maxaukakin Sarki. Yin haka shi ne mafi zama kusa ga samun biyan bukata. Allah shi ne mafi sani. Hujja a kan wanan Sunna: Hujja a kan wannan Sunna, ita ce Hadisin Fadhalata xan Ubaidu raliyallahu anhu, wanda ya ce: “Wata rana Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ji wani mutum yana roqon Allah a cikin sallarsa, ba tare da ya share wa bukatarsa fage da yin salati gare shi ba sallallahu alaihi wa sallam. Sai Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce masa: “Xan saurara, ka kuma taho nan ina son ganin ka.” Bayan isowarsa sai ya kale shi, tare da sauran Sahabban da suke wurin, ya ce musu: “Daga yau idan xayanku yi addu’a, to, ya farad a miqa godiya ga Allah Maxaukakin Sarki, da yabo a gare shi. Sa’annan ya yi salati ga Annabinsa. Bayan haka sai ya roqi duk abin da yake so.” (Tirmizi:3477), ya kuma qara da cewa: “Wannan Hadisi ne kyakkyawa kuma ingantacce.” Malam Ibnl-Qayyim rahimahullahu ya ce: “Abin da ake so ga duk wanda zai roqi Allah Maxaukakin Sarki wani abu, to, ya farad a miqa yabo da godiya gare shi subhanahu wa ta’alah kafin furta bukatarsa. To, sa’annan ssi ya roqi duk abin da yake son roqawa, kamar dai yadda Hadisin Fudhalata xan Ubaidu ya bayyana.” Domin qarin bayani sai a duba: (Alwábilus-Sayyib:110.) Mas’alah: Shin ko mutum na iya shafar fuskarsa da hannuwansa bayan ya qare alqunúti ? Ingantattar magana ita ce, shafa addu’a a fusaka ba Sunna ba ne, saboda babu wani dalili ingantacce da aka samu a kan haka. An tanbayi Imamu Maliku rahimahullahu a kan mutumin da yake shafa addu’a a fuskarsa; meye hukuncin yin haka? Imami Maliku ya ce, yin haka bai dace ba. Ya kuma qara da cewa: “Ban san wannan karatu ba.” don qarin bayani sai a duba: (Alwirtu na Marwazí:236) Shaikhul-Islam rahimahullahu ya ce: “Amma, zancen mutum ya yi addu’a a hannuwansa, sa’annan ya shafa a fuska; babu wani dalili a kan haka, sai wasu Hadisai guda biyu. Babu kuma xaya daga cikinsu da yake iya zama hujja a kan yin haka.
Yin addu’a da roqon Allah Maxaukakin Sarki a lokacin da dare ya kusa kwashe kayansa, yana daga cikin Sunnoni masu qarfi. Idan mutum ya yi addu’a a cikin alqunutinsa na qarshen dare, to, ba sai ya sake yin wata addu’ar ba; wannan ta wadatar. Idan kuwa an yi sa’a bai yi ba, to, sai ya yi, saboda addu’a a irin wannan lokaci, yana daga cikin Sunna, domin lokaci ne da addu’a bat a faxuwa qasa. Saboda, lokaci ne da Allah Maxaukakin sarki yake saukowa zuwa sama ta duniya, sauka irin wadda ta dace da girma da matsayinsa subhanahu wa ta’alah. Wanna, kamar yadda ya ainganta a cikin ingatattun littafan Buhari da Muslimu, daga cikin Hadisan Abu Hurairata raliyallahu anhu, cewa, tabbas! Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Ubangijinmu Maxaukaki yana saukowa a cikin kowane dare zuwa samar duniya; a daidai lokacin da ya rage saura kashi xaya daga cikin uku na lokaci, dare ya kwashe kayansa.Idan ya sauko xin yakan ce: “Wa zai kira ni, in karva masa? Wa zai roqe ni wani abu, in ba shi? Wa zai nemi gafarata in gafarta masa? (Buhari:1145/ Muslimu:758).
Hujja a kan wannan Sunna: Hujja a kan wannan Sunna, ita ce, Hadisin Ubayyu xan Ka’abu raliyallahu anhu, wanda ya ce: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yana karanta: {Sabbihisma Rabbikal-a’alá} da {Qul ya ayyuhal-káfirún} da {Qul Huwalláhu Ahad} a cikin sallarsa ta Wuturi. Idan kuma ya sallame, sai ya ce: “Subhánal-Malikul.Quddús” (Tsarki ya tabbata ga Sarkin Sarakuna mai cikakken tsarki) har sau uku.” (Nasá’í:1702) Albani kuma ya inganta shi kamar yadda a ka bayyana a baya kaxan. A cikin Hadisin Abdurrahman xan Abzí raliyallahu anhu kuma aka ce: “Kuma Annabi sallallahu alaihi wa sallam yana xaga sautinsa idan zai faxi: Subhánal-Malikul.Quddús” xin nan har sau uku. (Ahmad:15354/ Nasa’i:1734) Albani kuma ya ainganta shi. Don qarin bayani sai a duba Tahqíqu mishkátul-masábíhí:1/398).
Kamar yadda aka sunnanta mutum ya tayar da iyalinsa domin yin wannan salla ta dare, haka ita ma mace, sunna ne idan ta tashi domin yin wannan salla, ta tayar da mijinta,da sauran iyalinta domin yin wannan salla. Wannan Sunna tana qarqashin babin taimakon juna a kan aikata alhairi. Hujja a kan wannan Sunna: Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Sayyidah A’isha raliyallahu anha, inda ta ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yakan yi sallalrsa ta bare gaba xaya shi kaxai, a daidai lokacin ni kuma, ina kwance tsakaninsa da alqibla. Idan yi tashi yin sallar Wuturi, sai ya tayar da ni, ni ma in yi.” (Buhari:512/ Muslimu:512). An kuma samo daga Ummu Salmata raliyallahu anha, wadda ta ce: “Wata rana Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya tashi a cikin dare, sai na ji yana cewa: “Subhánalláhi mazá unzila minal-khazá’ini, wa mazá unzila nimal-fitani. Man yúqizu sawáhibal-hujari? Liyusallína. Raubba kásiyátin fid-duniya áriyatun fil-ákhirah.” (Tsaraki ya tabbata ga Allah sarkin day a saukar da taskokin alhairi, a wajje xaya kuma ya saukar da fitintinu! Bari in tayar da masu xakunan nan nawa domin su yi sallah don su yi salla. Da yawa masu sutura a duniya za su wayi gari huntaye a lahira.” (Buhari:6218).
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Anas raliyallahu anhu, inda ya ce: “Wata rana Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya shiga Masallaci ya tarasa da wata igiya an xaura ta tsakanin wani ginshiqi da wani. Sai ya ce: “Mene ne haka?” Sai suka karva masa da cewa: “Ai Sayyidah zainab c eta xaura ta tana salla. Idan ta ji gajiya ko kasala, sai ta kama igiyar ta riqe.” Sai ya ce: “Maza ku kwanace ta. Duk wanda zai yi salla daga cikinku, ya yi ta gwargwadon ikonsa. Da zarar ya ji gajiya ko kasala, to, ya sallame ya zauna abinsa.” (Buhari:11150/ Muslimu:784). - Idan kuma angaje ya kama mutum, to, ya kwanta ya yi bacci domin ya huta. Bayan haka sai ia tashi ya ci gaba da sallar. Hujja a kan wannan Sunnan kuwa ita ce, Hadisin Sayyidah A’isha raliyallahu anha, inda ta ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Idan angaje ya kama xaya daga cikinku yana salla. To, ya kwanta abinsa ya bacci isasshe. Domin tana yiwuwa idan ya ce sai ya yi sallar cikin angajen, ya je neman gafara ya zagi kansa.” (Buhari:212/ Muslimu:786). - Haka nan kuma idan angajen, ko wani abu mai kama da shi, ya kama mutum yana karatun alqur’ani a cikin dare. To, Sunna ta tanadi cewa, ya kwanta ya yi bacci, domin ya sami nishaxi da qarfin jiki. Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abu Hurairata raliyallahu anhu, inda ya ce: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Idan xayanku ya tashi a cikin dare, ya ji ya fara boboci a cikin alqur’ani; bai san abin da yake faxa ba. To, maza ya kwanta abinsa.” (Muslimu:787).
Abin da ake nufi shi ne, idan a al’adar mutum yana raka’a uku ne a matsayin Wuturi. Sai bacci ya kwashe shi, ko rashin lafiya ta addabe shi, bai sami damar yi ba. To, sai ya yi raka’a huxu da rana. Idan kuma raka’a biyar ya saba yi, amma bacci ko rashin lafiya ba su bari ya yi ba. To, idan ya wayi gari sai ya yi raka’a shida; haka-haka. Haka Annabi sallallahu alaihi wa sallam yakan yi. Shi a tasa al’ada sallallahu alaihi wa sallam, yakan yi ra’aka goma sha xaya ne a matsayin Wuturi. Sayyidah A’isha raliyallahu anha ta bayar da labarin cewa: “Idan bacci ko wata rashin lafiya suka rinjaye shi; bai sami dammar yin wannan salla ta dare ba. idan gari yaw aye, sai ya yi raka’a goma sha biyu.” (Muslimu:746).