brightness_1
Sunna ce Yin Sallar Dare a Cikin Lokacinta Mafifici
Idan Aka ce Wane Lokaci ne Mafifici ga Mai Sallar Dare? Amsa ita ce: Kamar yadda aka sani
cewa, lokacin sallar Wuturi yana faraway ne daga bayan sallar Isha’i har zuwa hudowar alfijiri. Kenan lokacin sallar Wuturi shi ne tsakanin sallar Isha’i da sallar Asuba. Hujja a Kan Wannan Magana: Hujja a kan wannan magana ita ce, Hadisin Sayyida A’isha raliyallahu anha, da ta ce: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yana sallatar raka’a goma sha xaya, tsakanin lokacin da ya qare sallar Isha’I zuwa sallar Asuba, inda yakan sallame bayan kowace raka’a biyu, sa’annan ya yi raka’a xaya a matsayin Wuturi.” (Buhari:2931/ Muslimu:736). Amma Lokacin da ya fi dacewa da Yin Sallar Dare Shi ne Tsakiyar Sulusin Dare na Biyu. Abin da ake nufi a nan shi ne, mutum ya raba dare kahsi biyu, ya yi sallalrsa a cikin sulusin kasha na biyu. Qarshen dare kuma sai ya kwanta ya yi bacci abinsa. Ma’ana, zai yi sallar kenan a cikin kasha xaya daga cikin shida na dare; a cikin kasha na huxu da na shida. Kasha na shida kuma ya yi ta bacci abinsa. Hujja a kan wannan Sunna kuwa, ita ce Hadisin Abdullahi xan Amru raliyallahu anhuma, wanda ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Haqiqa, mafi soyuwar azumi a wurin Allah, shi ne azumin Annabi Dawuda. Mafi soyuwar sallah kuma a wurin Allah, ita ce sallar Annabi dawuda alaihissalamu. Domin ya kasance yana kwantawa tsawon rabin dare ya yi bacci. Sa’annan ya tashi ya yi salloli a cikin sulusinsa. A cikin sauran sudusinsa kuma ya sake kwantawa ya qara yin bacci. Ta vangaren azumi kuma, yana yi ne yau ya sha ruwa gobe.” (Buhari:3420/ Muslimu:1159). - To, idan mutum yana son ya raya wannan sunna, ya zai gane wannan lokaci na dare? Zai fara lissafi da neman gane wannan lokaci ne, daga lokacin da rana ta faxi, zuwa lokacin da alfijiri ya keto. Sa’annan ya karkasa wannan tsakani zuwa gida shida. Kashi uku na farko su ne matsayin bain wannan dare na farko. Sai ya tashi ya yi sallolinsa a cikin kashin da yake bi ma wannan, wato, na huxu da na biyar, domin matsayin kasha xaya bisa uku suke na daren. Sa’annan ya sake kwantawa ya qara yin bacci a cikin kasha na shida; na qarshe. Saboda haka ne Sayyida A’ishatu ta ce: “Ban tava ganin rashin bacci ya tuqaqe Annabi sallallahu alaihi wa sallam ba, domin yana bacci isasshe.” (Buhari:1133/ Muslim:742). Idan musulmi ya kiyaye wannan hanya ta qididdiga, to, babu lokacin da zai tashi cikin dare domin yin salla, face ya dace da lokaci mafifici, kamar dai yadda Hadisin can na Abdullahi xan Amru raliyallahu anhu, da ya gabata, ya bayyana. A taqaice dai, zancen fifiko a cikin lokacin yin sallar dare, da yadda aka fi son musulmi ya yi, mataki uku yake: Mataki Na Farko: Abin da ake so a wannan mataki na farkon rabin dare, shi ne mutum ya kwanta ya yi bacci abinsa. Sa’annan ya kuma sake kwantawa a cikin kashi aya na qarshe daga cikin shida, ya yi wani baccin, kamar dai yadda bayani ya gabata. Hujja a kan wannan Sunna kuwa ita ce, Hadisin Amru xan Asi raliyallahu anhu, wanda ya gabata xazu kaxan. Mataki Na Biyu: A wannan mataki kuma sai ya tashi ya yi sallolinsa a cikin kashi xaya bisa uku na qarshen dare. Hujja a kan wannan Sunna: Hujja a kan wannan Sunna kuma, ita ce Hadisin Abu Hurairata raliyallahu anhu, cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Ubangijinmu mai girma da xaukaka yakan sauko zuwa samar nan ta duniya a cikin kowane dare, daidai lokacin da sulusin dare na qarshe ne ya rage. Sai ya ce: Ina wanda yake da bukata, ya roqe ni, in karva masa? Ina wanda yake son wani abu, ya koka mani, in share masa hawaye? Ina wanda yake neman gafarata, in gafarta masa?” (Buhari:1145/ Muslim:758). Haka nan kuma Hadisin Jabiru raliyallahu anhu, wanda za zo nan gaba. Shi ma hujja ne a kan wannan Sunna. Idan kuma mutum yana tsoro da fargaban, kada ya kasa tashi a qarshen dare. To, yana iya yi sallarsa a farkonsa, ko a cikin kowane yanki ma na daren ya sami dammar hakan. Wannan shi ne mataki na uku. Mataki Na Uku: Kamar yadda aka faxa a sama, wannan mataki ya qunshi, yin sallar a farkon dare, ko a cikin duk lokacin da dama ta samu ga mutum. Hujja a kan wannan Uzuri: Hujja a kan wannan uzuri da dama kuwa ita ce, Hadisin Jabiru raliyallahu anhu, inda ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Duk wanda ya ji tsoro ba zai iya tashi qarshen dare domin yin Wuturoba, to, ya yi abinsa tun a farkon dare. Wanda kuma yake da tabbacin zai iya tashi a qarshen nasa, to, ya bari sai qarshen dare, sa’annan ya yi. Saboda salla a qarshen dare abar halarta ce. Wannan kuwa shi ne mafifici.” (Muslim:755). Wani dalili kuma da yake iya zama hujja a kan wannan uzuri, shi ne wasiccin da Annabi sallallahu alaihi wa sallam, ya yi wa Abi Zarrin, wanda Imamun-Nasá’í ya riwaito a cikin: Sunann-Kubra(2712), Nsiruddil-Albáni kuma ya ainganta shi a cikin: Assahíhah (1433), da kuma Abud-Darda’i, riwayar Ahmad: 27471, wadda kuma Albáni ya ingantata ta (Sahihu Abu Dawuda: 5/177), da Abu Hurairata raliyallahu anhu, riwayar Muslim: 737). Kowacce daga cikin waxannan riwayoyi cewa suke yi: “Badaxayina ya yi mini wasicci da abubuwa guda uku…” daga cikinsu ya ambaci cewa: “… da kuma in sallaci Wuturi kafin in shiga bacci.”