brightness_1
Idan irin wannan lokaci ya kama, na sallar Walha, Sunna ta yi matuqar kwaxaitar da owane bawa musulmi a kan yin wannan sallal ta Walha
Hujja a kan wannan Sunna:
a) Hujja ta farko a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abu Hurairah raliyallahu anhu, inda ya ce: “Masoyina manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya yi mini wasicci da abubuwa guda uku. Na farko azumin kwanaki uku a cikin kowane wata. Na biyu sallar raka’o’i biyu na Walha. Na uku kuma, kada in kuskura in shiga bacci ban sallaci Wuturi ba. Haka nan kuma Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya yi wa Abud-darda’i raliyallahu anhu irin wannan wasicci a wani Hadisi da Imamu Muslimu ya riwaito:722. Ya kuma tava yi wa Abu Zarrin raliyallahu anhu irinsa a wani Hadisin da Imamun- Nasa’i ya riwaito a cikin: As- Sunanulkubra:27112, albani kuma ya inganta shi a cikin: As- Sahíhah:2166).
b) Hujja ta biyu ita ce, Hadisin Abu Zarrin raliyallahu anhu daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam, cewa ya ce: “Babu wata gava ta xayanku, face an wayi gari akwai aikin sadaqa da take iya yi. Kowane tasbihi (subhánalláh) sadaqa ne; kowane tahmidi (alhamdu lilláh) sadaqa ne; kowane tahlili (lá iláha illalláh) sadaqa ne; kowane takbiri (alláhu akbar) sadaqa ne; horo da kyakkyawan aiki sadaqa ne. hani da mummunan aiki sadaqa ne. Ko ba a sami damar kuma yin ko xaya daga cikin waxannan ba, aka yi sallar Walha, ta wadatar.” (Muslimu720).
Kalimar ‘sulámá’ ta Larabci a cikin wannan Hadisi, ita ce muka fassara da ‘gava.’
Ya kuma zo a cikin wani Hadisi na Imamu Muslim daga Sayyida A’sha raliyallahu anha cewa Allah Maxaukakin Sarki ya gina halittar kowane mutum a kan gavovi xari uku da sittin. To, duk wanda ya yi nau’ukan sadaqa har kwatankwacin wannan adadi, za ta fanshi gangar jikinsa daga shiga wutar jahannama a ranar Qiyama.