Idan irin wannan lokaci ya kama, na sallar Walha, Sunna ta yi matuqar kwaxaitar da owane bawa musulmi a kan yin wannan sallal ta Walha
Hujja a kan wannan Sunna:
a) Hujja ta farko a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abu Hurairah raliyallahu anhu, inda ya ce: “Masoyina manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya yi mini wasicci da abubuwa guda uku. Na farko azumin kwanaki uku a cikin kowane wata. Na biyu sallar raka’o’i biyu na Walha. Na uku kuma, kada in kuskura in shiga bacci ban sallaci Wuturi ba. Haka nan kuma Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya yi wa Abud-darda’i raliyallahu anhu irin wannan wasicci a wani Hadisi da Imamu Muslimu ya riwaito:722. Ya kuma tava yi wa Abu Zarrin raliyallahu anhu irinsa a wani Hadisin da Imamun- Nasa’i ya riwaito a cikin: As- Sunanulkubra:27112, albani kuma ya inganta shi a cikin: As- Sahíhah:2166).
b) Hujja ta biyu ita ce, Hadisin Abu Zarrin raliyallahu anhu daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam, cewa ya ce: “Babu wata gava ta xayanku, face an wayi gari akwai aikin sadaqa da take iya yi. Kowane tasbihi (subhánalláh) sadaqa ne; kowane tahmidi (alhamdu lilláh) sadaqa ne; kowane tahlili (lá iláha illalláh) sadaqa ne; kowane takbiri (alláhu akbar) sadaqa ne; horo da kyakkyawan aiki sadaqa ne. hani da mummunan aiki sadaqa ne. Ko ba a sami damar kuma yin ko xaya daga cikin waxannan ba, aka yi sallar Walha, ta wadatar.” (Muslimu720).
Kalimar ‘sulámá’ ta Larabci a cikin wannan Hadisi, ita ce muka fassara da ‘gava.’
Ya kuma zo a cikin wani Hadisi na Imamu Muslim daga Sayyida A’sha raliyallahu anha cewa Allah Maxaukakin Sarki ya gina halittar kowane mutum a kan gavovi xari uku da sittin. To, duk wanda ya yi nau’ukan sadaqa har kwatankwacin wannan adadi, za ta fanshi gangar jikinsa daga shiga wutar jahannama a ranar Qiyama.
Lokacin yin sallar Walha
Wannan lokaci na yin sallar Walha yana farawa daga lokacin da rana ta xaukako sama gwargwadon tsawon gorar mashi, bayan lokacinj da aka haramta yin sallar nafila a cikinsa, ya wuce.
Wannan lokaci kuma yana qarewa gab da lokacin da rana za ta bar tsakiyar sararin samaniya; gab da shigowar lokacin sallar Azahar; minti kamar goma kafin haka.
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Amru xan Absa raliyallahu anhu, wanda ke cewa: “Ka yi sallar, sa’annan ka saurara daga yin kowace irin salla a daidai lokacin da rana take vullowa, har zuwa lokacin da ta gama xaukakowa. To, daga nan kana iya yin salla, saboda salla abar shaida da halarta ce. Daga nan har zuwa lokacin da inuwa ta gota da gorar mashi. Daga nan kuma sai ka sake saurarawa daga kowace irin salla, saboda a daidai wannan lokaci ne ake yi wa wutar Jahannama zuga-zugi.” (Muslimu:832).
Lokaci mafi falala ga sallar Walha
Lokaci mafi falala ga wannan salla ta Walha shi ne, qarshen lokaci da aka qayyade mata, wato daidai lokacin da raha ta fara gasa bayan ‘ya’yan raqumma.
Hujja a kan wannan Sunna ita ce: Hadisin Zaidu xan Arqam raliyallahu anhu, cewa, Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Masu neman kusanci ga Allah Maxaukakin Sarki suna yin sallar Walaha ne a daidai lokacin da rana ta fara gasa bayan ‘ya’yan raqumma.”
Malam Ibn Báz rahimahullahu ya ce: “Abin da ake nufi da ‘rana ta fara gasa bayan ‘ya’yan raquma’ shi ne daidai lokacin da zafin rana ya fara tsanani yana dama musu lissafi suna neman mafaka. Sallar Walha tana daga cikin sallolin da yin su a qarshen lokaci ya fi lada. Don qarin bayani sai a duba: Fatáwá Islámiyyah (1/5150.
Adadin raka’o’in sallar Walha
Mafi qarancin adadin raka’o’in sallar Walha su ne raka’a biyu. Hujja a kan wannan adadi kuwa ita ce, Hadisin Abu Hurairah raliyallahu anhu, wanda yake a cikin ingantattun littafan Buhari da Muslimu, cewa: “Badaxayina ya yi mani wasicci da abubuwa guda uku..” daga cikinsu ya ambaci: “raka’a biyu na sallar Walha.” (Buhari:1981/ Muslimu:721).
Amma dangane ko meye mafi yawan adadin raka’o’in wannan salla ta Walha? Amsa ita ce, Sunna ba ta iyakance ba. Duk da yake an samu Malaman da suka ce mafi yawansu shi ne ‘raka’a takwas.’ To, bisa wannan ingantaccen zance da yake hannu a halin yanzu, mutum yana iya qarawa fiye da takwas xin nan gwargwadon ko ma nawa Allah Maxaukakin Sarki ya bas hi ikon iya yi. Hujja a kan rashin iyaka ga wannan a dadi kuwa ita ce, Hadisin Sayida A’isha raliyallahu anha, inda ta ce: Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yana yin raka’a huxu a matsayin sallar Walha. Yakan kuma qara gwargwadon abin da Allah Maxaukakin Sarki yah ore masa.” (Muslimu:719).
Don Saduwa Da Mu
Da Mu
Muna Farin Ciki Da Samun Kiranka Da Tambayoyinka A Kowane Lokaci