brightness_1
Maimaita addu’ah da nacewa
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin xan Abbas raliyallahu anhu wanda ya gaba, inda ya ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Ya Ubangiji! Ka cika mani alqawalin da ka yi mani. Ya Ubangiji! Ka kawo mani agajin da ka yi mani alqawali,” Haka ya ci gaba da aika wannan saqo zuwa ga Ubangijinsa, har mayafinsa ya baro kafaxunsa ya sauka qasa ya. Sai Sayyadi Abubakar raliyallahu anhu ya zo ya xauke mayafin ya nayar masa da shi a kan kafaxa, ya kuma ci gaba ada kasancewa a bayansa sallallahu alaihi wa sallam yana cewa masa: “ya Annabin Allah! ya isa haka nan; saqonka ya isa zuwa ga Ubangijin naka. Ko shakka babu, zai cika maka duk alqawulan da ya yi maka a wanan rana….” (Muslim:1763).
Wata hujjar kuma ita abin da ya zo a cikin ingantattun littafan Hadisai guda biyu, daga cikin hadisan Abu Hurairah raliyallahu anhu, a lokacin da Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya tashi yi wa Dausu addu’a, sai ya ce: “Ya Ubangiji! Ka shiryar da Dausu, ka kuma kawo mana su. “Ya Ubangiji! Ka shiryar da Dausu, ka kuma kawo mana su.” (Buhari:2937/ Muslimu:2524).
wata hujjar kuma ita ce, abin day a zo a cikin ingantaccen littafin Imamu Muslimu, a kan: “Mutumin nan da ya yo doguwar tafiya, har gashin kansa ya yi qutuu-qutut da qura, ya kuma shiga xaga hannuwansa sama, yana kiran ya Ubangiji! Ya Ubangiji!!) (Buhari:1015). Irin wannan maimaitawa xauke take da naciya da nuna tsananin bukata.
Abin da Sunna ta yi tanaadi a wannan babi shi ne, idan mutum zai roqi Allah Maxaukakin Sarki, to, ya maimaita kalmomin roqon har sau uku. Hujja kuwa ita ce, Hadisin xan Mas’udu raliyallahu anhu wanda yake cikin ingantattun littafan Hadisai guda biyu, da aka ce: “Haka nan kuma duk lokacin da Annabi sallallahu alaihi zai yi addu’a, yakan maimaita har sau uku, sa’annan ya ce: “Ya Ubangiji! Ina kai qarar Quraishawa a wurinka.” Shi ma wannan lafazin yakan maimaita shi har sau uku.” (Buhari:240/ Muslimu:1794).