Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abu Musa raliyallahu anhu, wanda yake a cikin ingantaccin littafan Hadisai guda biyu, xauke da labarin abin da ya faru tsakaninsa abu Amir raliyallahu anhu. a lokacin da Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya jagorantar da shi a kan rundunar da ya tura zuwa Auxas. A cikin wannan Hadisi, aka ambaci cewa, an kasha Abu Amir raliyallahu anhu, amma kafin fitar rayuwarsa, ya ba wa Abu Musa saqon gaisuwa zuwa ga Annabi sallallahu alaihi wa sallam. Bayan gaisuwa kuma yana roqon alfarma ga Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya yi masa addu’a. Abu Musa ya ce: “Bayan da na labarta wa Annabi sallallahu alaihi wa sallam duk halin da muka kasance a ciki, a can, da kuma labarin abin day a faru ga Abu Amir. Na kuma gaya masa cewa, ya ce in gaya maka ka roqar masa gafarar Allah subhanahu wa ta’alah. Nan take sai Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya nemi a kawo masa ruwa. Da aka kawo, sai ya yi arwalla, sa’annan ya xaga hannuwansa zuwa sama, ya shiga cewa: “Ya Ubangiji! Ina roqon ka gafartawa wannan babban bawa naka; Abu Amirin.” Haka ya yi ta yi yana qara xaga hannuwansa zuwa sama, har sai da na hangi farin hamatarsa. Can kuma sai na ji ya canza lafuzza sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Ya Ubangiji! Ina roqon ka xaukaka darajarsa ranar Qiyama fiye da, da yawa daga cikin halittarka, ko daga cikin mutane.” (Buhari:4323/ Muslimu:2498).
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin da aka riwaito daga Abdullahi xan Abbas raliyallahu anhu, da ya ce: Sayyadi Umar xan Khaxxabi raliyallahu anhu ya ba ni labara cewa: A ranar yaqin Badar, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kalli dandazon mushirikai, su dubu. Sahabbansa kuma a hannu xaya, yawan adadinsu bai wuce xari uku da goma sha tara ba. Nan take sai Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya fuskanci alqibla, ya kuma xaga hannuwansa zuwa sama, ya shiga aika saqon addu’a zuwa ga Ubangijinsa yana cewa: “Ya Ubangiji! Ka cika mani alqawalin da ka yi mani. Ya Ubangiji! Ka kawo mani agajin da ka yi mani alqawali. Ya Ubangiji! Idan wannan rukuni na musulmi suka halaka, ba za a sake bauta maka ba a bayan qasa.” Haka ya ci gaba da aika wannan saqo zuwa ga Ubangijinsa, hannuwansa suna sama, yana akuma fuskantar alqibla, har mayafinsa ya baro kafaxunsa ya sauka qasa ya. Sai Sayyadi Abubakar raliyallahu anhu ya zo ya xauke mayafin ya nayar masa da shi a kan kafaxa, ya kuma ci gaba ada kasancewa a bayansa sallallahu alaihi wa sallam yana cewa masa: “ya Annabin Allah! ya isa haka nan; saqonka ya isa zuwa ga Ubangijin naka. Ko shakka babu, zai cika maka duk alqawulan da ya yi maka a wanan rana….” (Muslim:1763).
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, abin da Imamut- Tirmizi ya riwaito daga Fadhalah xan Ubaid raliyallahu anhu, wanda ya ce: “Wata rana Manzon Allah sallallahu alahi wa sallam yana zaune. Sai ga wani mutum ya shigo; ya kuma salla. Sa’annan ya qara da yi wa kansa addu’a da cewa: “Ya Ubangiji! Ka gafarta mani, ka kuma yi mani rahama.” Jin haka sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce masa: “Bawan Allah! ka yi gaggawa. Da gama sallarka! Idan ka qare salla, abin da ake so, shi ne ka zauna dangalgal, ka miqa godiya ga Allah ta hanyar duk wasu kalmomi da suka dace da shi. Sa’annan ka yi mani salati. Sa’annan sai ka roqi abin da kake so.” (Tirmizi:3476) Albani kuma ya ainganta a cikin: Sahíhul- Jámi’i: (1/172).
Idan mutum zai raya wannan Sunna, sai ya duba da kyau, ya kalli sunayen Allah Maxaukakin Sarki, ya zavi wanda ma’anarsa ta dace da bukatarsa ya xauka. Misali, idan zai roqi Allah subhanahu wa ta’alah arzikin duniya ne, sai ya riqa kiran: “Ya Razzáqu.” Idan kuma rahamar Allah Maxaukakin Sarki ce, yak enema, sai ya shiga kiran: “Ya Rahmánu. Ya Rahímu.” Idan kuma girma da xaukaka ne yake neman daga Allah Maxaukakin Sarki, sai ya xauki: “Ya Azízu.” Idan kuma yana so ne ya roqi Allah Maxaukakin Sarki gafara ne, ti, sai ya xauki: “Ya Gaffáru.” Haka kuma, idan waraka ce yake nema, to, sai ya xauki: “Ya Sháfí.”
Haka zai ci gaba da kallon bukatunsa da idon basira yana roqon Allah Maxaukakin Sarki da sun da ya dace da su. Hujja kuwa a kan wannan Sunna ita ce, faxar Allah Maxaukakin Sarki: “Kuma Allah yana da sunaye kyawawa, sai ku roqe shi da su.” {A’araf”180}
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin xan Abbas raliyallahu anhu wanda ya gaba, inda ya ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Ya Ubangiji! Ka cika mani alqawalin da ka yi mani. Ya Ubangiji! Ka kawo mani agajin da ka yi mani alqawali,” Haka ya ci gaba da aika wannan saqo zuwa ga Ubangijinsa, har mayafinsa ya baro kafaxunsa ya sauka qasa ya. Sai Sayyadi Abubakar raliyallahu anhu ya zo ya xauke mayafin ya nayar masa da shi a kan kafaxa, ya kuma ci gaba ada kasancewa a bayansa sallallahu alaihi wa sallam yana cewa masa: “ya Annabin Allah! ya isa haka nan; saqonka ya isa zuwa ga Ubangijin naka. Ko shakka babu, zai cika maka duk alqawulan da ya yi maka a wanan rana….” (Muslim:1763).
Wata hujjar kuma ita abin da ya zo a cikin ingantattun littafan Hadisai guda biyu, daga cikin hadisan Abu Hurairah raliyallahu anhu, a lokacin da Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya tashi yi wa Dausu addu’a, sai ya ce: “Ya Ubangiji! Ka shiryar da Dausu, ka kuma kawo mana su. “Ya Ubangiji! Ka shiryar da Dausu, ka kuma kawo mana su.” (Buhari:2937/ Muslimu:2524).
wata hujjar kuma ita ce, abin day a zo a cikin ingantaccen littafin Imamu Muslimu, a kan: “Mutumin nan da ya yo doguwar tafiya, har gashin kansa ya yi qutuu-qutut da qura, ya kuma shiga xaga hannuwansa sama, yana kiran ya Ubangiji! Ya Ubangiji!!) (Buhari:1015). Irin wannan maimaitawa xauke take da naciya da nuna tsananin bukata.
Abin da Sunna ta yi tanaadi a wannan babi shi ne, idan mutum zai roqi Allah Maxaukakin Sarki, to, ya maimaita kalmomin roqon har sau uku. Hujja kuwa ita ce, Hadisin xan Mas’udu raliyallahu anhu wanda yake cikin ingantattun littafan Hadisai guda biyu, da aka ce: “Haka nan kuma duk lokacin da Annabi sallallahu alaihi zai yi addu’a, yakan maimaita har sau uku, sa’annan ya ce: “Ya Ubangiji! Ina kai qarar Quraishawa a wurinka.” Shi ma wannan lafazin yakan maimaita shi har sau uku.” (Buhari:240/ Muslimu:1794).
Hujja a kan wannan Sunna kuma ita ce, faxar Allah Maxaukakin Sarki: “Ku roqi Ubangijinku kuma masu qanqan da kai da asirtawa.” {A’araf:55}. Asirta addu’a xin nan kuma, shi ne mafi zama kusa ga tsarkin zuciya. Bisa wannan dalili ne, Allah Maxaukakin Sarki ya yabi Annabi Zakariyya alaihissalam da cewa: “A lokacin da ya kira Ubangijinsa, kira abin voyewa.” {Maryam:3}. Jigajigan Malaman tafsiri sun bayyana cewa, Annabi Zakariyya ya asirta addu’arsa ne domin neman qarin ikhlasi da kiran Allah Maxaukakin Sarki da zuciya xaya
Tana yiwuwa wani ya yi tambaya a cikin ransa cewa: me ya kamata in faxa idan zan roqi Allah? Amsa a kan haka ita ce: Abin day a kamata muslmi ya roqi Allah Maxaukakin Sarki shi ne, alhairan duniya da na Lahira. Sa’annan kuma Sunna tana son a riqa mayar da hankali ga dunqulallun kalmomi; ba sai an tsay yi wa Allah subhanahu wa ta’alah, kwatta-kwatta ba. Yin addu’a ta hanyar amfani da kalmomin dunqulalli kuma kammalalli, wanda ya haxa da roqon alhairan duniya da Lahira, shi ne abin da Alqur’ani da Sunna suka zo da shi. An tava yi wa Annabi sallallahu alaihi wa sallam irin wannan tambayar. Sai ya karva da cewa, a kula da amfani da manya-manyan kalmomi, game-gari; irin waxanda ke kawo wa muslmi alhairin duniya da na Lahira. Kai ka san babu busharar da ta kai wanna girma da yawan kawo kyakkyawan sakamako a matsayinta na mafi girman kyauta. Saboda haka yana da kyau musulmi su kula, su kuma riqa ta da hannu biyu-biyu.
An samo daga Abi Malik Al’ashja’í raliyallahu anhuma, cewa: “Ya ji Annabi sallallahu alaihi wa sallam wata rana, da wani mutum ya zo wurinsa, ya ce masa: “Ya Manzon Allah me ya kamata in faxa idan zan roqi Allah Ubangijina?” Sai ya karva masa da cewa: “Ka ce: Alláhummg- fir lí, warhamní, wa áfiní, warzuqní.” (Ya Ubangiji! Ka gafarta mani, ka yi mahi rahama, ka ba ni lafiya, ka kuma arzuta ni.) Yana yi yana harhaxe ‘yan yatsunsa a jikin banbansu. Ya kyma qara da gaya masa cewa: “Ka ga waxannan kalmomi, babu abin dab a za su lamunce maka ba, na duniya da Lahirarka.” (Muslimu:2697).
A cikin wata riwaya kuma ta shi Muslimu xin, ya ce: “Duk lokacin da wani mutum ya karvi Musulunci,sai Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya koya masa yadda ake salla. Sa’annan ya umarce da ya riqa roqon Allah Maxaukakin Sarki da waxannan kalmomi: “Alláhummg- fir lí, warhamní, wahdiní, wa áfiní, warzuqní.” (Ya Ubangiji! Ka gafarta mani, ka yi mahi rahama, ka shiryar da ni, ka ba ni lafiya, ka kuma arzuta ni.) [Muslimu:2697]
Wani Qarin Haske: Sunna ne mutum ya yi wa xan’uwansa addu’a a bayan idonsa. Irin wannan addu’a kuwa, babu shamaki tsakaninta da Allah Maxaukakin Sarki; karvavva ce, da yardarm Allah. Wanda kuma ya yi wannan addu’a shi ma Allah Maxaukakin Sarki zai ba shi lada mai yawa. Hujja a kan wannan Sunna kuwa ita ce, abin da Imamu Muslimu ya riwaito a cikin ingataccen littafinsa, daga Abud- Darda’i raliyallahu anhu, wanda ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Addu’ar duk da musulmi zai yi wa xan’uwansa muslmi a bayan idonsa, karvavva ce a wurin Allah. Akwai mala’ika a daidai kansa, da yake wakiltar Allah Maxaukakin Sarki. Duk lokacin day a yi wa wani xan’uwa nasa muslmi addu’a bayan idonsa, sai wannan mala’ika ya ce: “amin, kai ma kana da irin duk abin da ka roqa masa.” (Muslim:2733).