brightness_1
Jiran Salla
Zaunawa Masallaci a jira kamawar lokacin wata salla, Sunna ce mai girma da take bayar da lada mai yawa.
Hujja a kan wannan Sunna:
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abu Huraira raliyallahu anhu, cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Zaman duk da xayanku zai jiran kamawar lokacin salla; babu abin day a hana shi komawa cikin iyalinsa sai sallar. To, kamar yana cikin sallar ne.” (Buhari:659/ Muslimu:649). Wannan jira da musulmi zai yin a kamawar lokacin salla, babu abin da ake rubuta masa sai ladar wanda yake salla.
Wata hujjar kuma ita ce, abin da aka riwaito daga Abu Huraira raliyallahu anhu, cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Mala’iku suna yin salati ga duk wanda yake zaune cikin Masallaci yana jiran kamawar lokacin sallah, matuqar bai yi magana ba, suna cewa: Allah ka yi gafara gare shi, ka kuma yi masa rahama. Zaman duk da xayanku zai jiran kamawar lokacin salla; babu abin day a hana shi komawa cikin iyalinsa sai sallar. To, kamar yana cikin sallar ne.” (Buhari:659/ Muslimu:649). Cewar da Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya yi: “Matuqar bai yi magana ba.” Ba magana kawai ba, hakan na nufin matuqar bai yi wani abu da zai walwale masa arwalla ba. Hujja a kan wannan fashin baqi ita ce, wata riwayar ta Muslim da take cewa, cewa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya yi:
“Matuqar bai cutar da wani a yayin zaman ba, bai kuma yi wani abu da zai walwale masa arwalla ba,” (649). Ma’ana, sharaxin samun wannan lada shi ne, kada ya cutar da wani abokin zamansa a cikin Masallacin, kada kuma arwallarsa ta walwale.