brightness_1
Taka wa hamma burki ko rufe ta da hannu Sunna ne
Hujja a kan wannan Sunna:
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abu Hurairah raliyallahu anhu, daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam, ya ce: “Haqiqa, Allah yana son attishaya, yana kuma qyamar hamma. Idan xayanku ya yi attishaya, ya kuma gode wa. To, wajibi ne a kan duk musulmin da ya ji shi, ya yi masa barka da arziki. Amma hamma, aba ce da take zuwa daga Shaixan. Saboda haka, musulmi ya yi qoqarin taka mata burki gwargwadon halinsa. Idan kuwa ya yi ta, to, ya sani Shaixan zai yi masa dariya.” (Buhari:2663).
A wata riwaya kuma ta Muslimu, daga cikin Hadisan Abu Sa’id raliyallahu anhu, cewa Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya yi: “Idan xayanku ya yi hamma, to, ya xora hannunsa a kan bakinsa, don kada Shaixan ya shiga.” (Muslim:2995). Kenan Sunna tana son a taka wa hamma burki ne, ta yadda za a yi ta ba tare da an wangali baki sagaga ba. Ko dai a kantse lavvan baki, da hauru, ta yadda hammar za ta fita ba tar da an gane ba, ko a sa hannu a rufe bakin, ko dai wasu dabaru masu kama da waxannan.