Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abu Hurairah raliyallahu anhu, daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam, ya ce: “Haqiqa, Allah yana son attishaya, yana kuma qyamar hamma. Idan xayanku ya yi attishaya, ya kuma gode wa. To, wajibi ne a kan duk musulmin da ya ji shi, ya yi masa barka da arziki. Amma hamma, aba ce da take zuwa daga Shaixan. Saboda haka, musulmi ya yi qoqarin taka mata burki gwargwadon halinsa. Idan kuwa ya yi ta, to, ya sani Shaixan zai yi masa dariya.” (Buhari:2663).
A wata riwaya kuma ta Muslimu, daga cikin Hadisan Abu Sa’id raliyallahu anhu, cewa Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya yi: “Idan xayanku ya yi hamma, to, ya xora hannunsa a kan bakinsa, don kada Shaixan ya shiga.” (Muslim:2995). Kenan Sunna tana son a taka wa hamma burki ne, ta yadda za a yi ta ba tare da an wangali baki sagaga ba. Ko dai a kantse lavvan baki, da hauru, ta yadda hammar za ta fita ba tar da an gane ba, ko a sa hannu a rufe bakin, ko dai wasu dabaru masu kama da waxannan.
Sa’annan kuma mafi daraja da xaukaka daga cikin duk masu buxa baki su yi hamma
Sa’annan kuma mafi daraja da xaukaka daga cikin duk masu buxa baki su yi hamma, a idon Sunna, shi ne mutumin da ba zai xaga sauti ya waste baki ya yi hamma haaaaa! Ko ahhhhhh!! ba, ko wani abu mai kama da haka daga cikin sautuka irin na hamma. Ba kuwa don komai Sunna ta hana hakan ba, sai don kada Shaixan ya yi sami damar yi wa musulmi dariya.
Hujja a kan wannan karhaci:
Hujja a kan wannan karhanci ita ce, Hadisin Abu Hurairah raliyallahu anhu daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam, ya ce: “Hamma daga Shaixan take zuwa. Saboda haka idan xayanku zai yi hamma, to, ya kankanta bakinsa gwargwadon hali. Domin, da zarar xayanku ya wangale baki, ya ce: haaaaaa! To, sai Shaixan ya fashe da dariya.” (Buhari:3297/ Muslimu:2994).
Tunatarwa
Wasu mutane sun saba da yin ta’auwuzi, watau neman tsari daga Shaixan bayan sun qare hamma. To, a sani babu wani dalili na Shari’ah a kan haka. Hasali ma yin haka sava wa koyarwar Annabi sallallahu alaihi wa sallam ne. Tabbas sava mata ne, saboda mutum ya zo da wani zikiri, wanda Annabi sallallahu alaihi wa sallam bai yi ba a daidai wannan wuri.
Don Saduwa Da Mu
Da Mu
Muna Farin Ciki Da Samun Kiranka Da Tambayoyinka A Kowane Lokaci