brightness_1
Yin sallama
Hujjojin da suke tabbatar da wannan Sunna ba su da iyaka. Daga cikinsu akwai: Hadisin Abu Huraira raliyallahu anhu, cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Haqqin kowane muslmi a kan xan’uwansa muslmi, shida ne.” Sahabbai suka ce: Waxanne haqqoqa ne waxannan ya Manzon Allah? sai ya karva musu da cewa: “Idan ka haxu da shi, ka yi masa sallama. Idan ya gayyace ka wata harka, ka tafi. Idan ya nemi wata nasiha daga gare ka, ka yi masa. Idan ya yi attishawa, ya kuma gode wa Allah, to, ka gai da shi. Idan ya yi rahsin lafiya, ka tafi duba shi. Idan kuma ya rasu ka rakki gawarsa maqabarta.” (Muslimu:2162).
Sai dai a kula, wajibi ne ga mutum idan aka gayar da shi, bayan ya yi attishaya, ya kuma gode wa Allah. wajibi ne ya karva wannan gaisuwa. Hujja kuma a kan wannan wajabci ita ce:
Faxar Allah Maxaukakin Sarki: “Kuma idan aka gayar da ku da wata gaisuwa. To, ku karva da mafi kyawonta, ko ku mayar da irinta. Lalle Allah, ya kasance a akn komai, mai qididdigewa ne.”
Zaman karvawar nan wajibi, shi ne hukunci na asali, matuqar wani dalili bai gitta ba, wanda zai canza wa hukuncin matsayi. An kuma samo da yawa daga cikin manyan Malamai, waxanda suka tafi a kan wajabcin karvawa xin. Daga cikinsu akwai: Ibn Hazmi, da Ibn abdil- Barr, da Shaikhu Taqiyyud- Din, rahimahumullahu jamí’an, da sauransu da dama. Don qarin bayani ana iya duba: “Al-ádábush- Shariyyah: 1/356” xab’in Mu’assasatur- Risálah.
Mafi icika da kamalar lafazin sallama da mayar da ita, shi ne: “Assalámu alaikun wa rahamatulláhi wa barakátuhú” Ko shakka babu wannan gaisuwa it ace mafi kyau da kammala.
Malam Ibnl- Qayyim rahimahullahu ya ce: “Karantarwar Annabi sallallahu alaihi wa sallam a cikin sha’anin gaisuwa, shi ne cika lafuzzan sallama tun daga farkonsu har qarshe. Wato, zuwa: “wa barakátuhú.” Domin qarin bayani ana iya duba: Zádul- mi’ádi:2/417”
Haka shi ma “yawaita sallama” Sunna ne. kai wuce nan ma, abu ne da Shari’a ta kwaxaitar da a yi, tare da bayyana irin ximbin falalar da take tattare da hakan. Hujja a kan haka kuwa ita ce: Hadisin Abu Huraira raliyallahu anhu, da ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Ina rantsuwa da wanda rayuwata take hannunsa, ba za ku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani. Ba kuma za ku yi imani har sai kun kasance masu so da qaunar junanku. To, me zai hana ku saurara in gaya muku abin da idan kuka tsare aikata shi, soyayya da qaunar za su dauwama a tsakaninku?! Ku yi ta yawaita sallama a tsakaninku.” (Muslimu:54)