Hujjojin da suke tabbatar da wannan Sunna ba su da iyaka. Daga cikinsu akwai: Hadisin Abu Huraira raliyallahu anhu, cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Haqqin kowane muslmi a kan xan’uwansa muslmi, shida ne.” Sahabbai suka ce: Waxanne haqqoqa ne waxannan ya Manzon Allah? sai ya karva musu da cewa: “Idan ka haxu da shi, ka yi masa sallama. Idan ya gayyace ka wata harka, ka tafi. Idan ya nemi wata nasiha daga gare ka, ka yi masa. Idan ya yi attishawa, ya kuma gode wa Allah, to, ka gai da shi. Idan ya yi rahsin lafiya, ka tafi duba shi. Idan kuma ya rasu ka rakki gawarsa maqabarta.” (Muslimu:2162).
Sai dai a kula, wajibi ne ga mutum idan aka gayar da shi, bayan ya yi attishaya, ya kuma gode wa Allah. wajibi ne ya karva wannan gaisuwa. Hujja kuma a kan wannan wajabci ita ce:
Faxar Allah Maxaukakin Sarki: “Kuma idan aka gayar da ku da wata gaisuwa. To, ku karva da mafi kyawonta, ko ku mayar da irinta. Lalle Allah, ya kasance a akn komai, mai qididdigewa ne.”
Zaman karvawar nan wajibi, shi ne hukunci na asali, matuqar wani dalili bai gitta ba, wanda zai canza wa hukuncin matsayi. An kuma samo da yawa daga cikin manyan Malamai, waxanda suka tafi a kan wajabcin karvawa xin. Daga cikinsu akwai: Ibn Hazmi, da Ibn abdil- Barr, da Shaikhu Taqiyyud- Din, rahimahumullahu jamí’an, da sauransu da dama. Don qarin bayani ana iya duba: “Al-ádábush- Shariyyah: 1/356” xab’in Mu’assasatur- Risálah.
Mafi icika da kamalar lafazin sallama da mayar da ita, shi ne: “Assalámu alaikun wa rahamatulláhi wa barakátuhú” Ko shakka babu wannan gaisuwa it ace mafi kyau da kammala.
Malam Ibnl- Qayyim rahimahullahu ya ce: “Karantarwar Annabi sallallahu alaihi wa sallam a cikin sha’anin gaisuwa, shi ne cika lafuzzan sallama tun daga farkonsu har qarshe. Wato, zuwa: “wa barakátuhú.” Domin qarin bayani ana iya duba: Zádul- mi’ádi:2/417”
Haka shi ma “yawaita sallama” Sunna ne. kai wuce nan ma, abu ne da Shari’a ta kwaxaitar da a yi, tare da bayyana irin ximbin falalar da take tattare da hakan. Hujja a kan haka kuwa ita ce: Hadisin Abu Huraira raliyallahu anhu, da ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Ina rantsuwa da wanda rayuwata take hannunsa, ba za ku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani. Ba kuma za ku yi imani har sai kun kasance masu so da qaunar junanku. To, me zai hana ku saurara in gaya muku abin da idan kuka tsare aikata shi, soyayya da qaunar za su dauwama a tsakaninku?! Ku yi ta yawaita sallama a tsakaninku.” (Muslimu:54)
Idan ya zaci cewa, wanda ya yi wa sallama bai ji ba, karo na farko da ya furta kalmomin. To, mustahabbi ne ya maimaita karo na biyu. Idan kuma ya tabbata bai jiya ba, to, sai ya sake maimaitawa karo na uku. Haka nan idan mutum ya iske wani taron jama’a, kamar a wata majalisa inda jama’a da dama suke taruwa. To, idan ya yi sallama daidai lokacin da ya isa. Amma, sai ya zamana waxanda suke kusa das hi sosai ne kawai suka ji. To, a irin wannan yanayi akwai bukatar ya maimaita sallamar har sau biyu; uku kenan, domin duk wanda yake zaune a majalisin, ya jiya.
Hujja a kan wannan Sunna, ita ce: Hadisin Anas raliyallahu anhu; daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam. Anas ya ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance idan ya yi Magana, yakan maimaita ta har sau uku, domin a gane haqiqanin abin da yake nufi. Haka nan idan ya taras da tarin jama’a a wuri xaya, idan zai yi musu sallama, yakan yi ta ne hae sau uku.” (Buhari:95)
Daga cikin darussan da za a koya daga wannan Hadisi na Anas raliyallahu anhu da ya gabata, shi ne, zaman maimaita Magana har sau uku, Sunna, idan akwai bukatar yin hakan. Wato, kamar inda mutum ya faxi wata magana, amma aka kasa fahimtarsa. To, Sunna ta xora masa nauyin maimaitawa karo na biyu. Idan kuma ba a fahimce ba, ya sake maimaitawa karo na uku.
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Amru raliyallahu anhuma, cewa: “Wani mutum ya tava tambayar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, cewa: “wane aiki ne ya fi kowane aiki zama alhairi a Musulunci? Sai ya karva masa da cewa: “Ciyar da abinci da yin sallama ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba.” (Buhari:12/ Muslimu:39).
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abu Hurairah raliyallahu anhu, da yake cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Wanda yake kana bin hawa ne zai fara yi wa wanda yake tafiya qasa, sallama. Wanda yake tafiya qasa kuma ya fara yi wa wanda yake zaune wuri xaya. rukunin mutanen da suke kaxan kuma, su fara yi wa wanda yake da yawa.” (Buhari: 6234)
Sai dai yana da kyau a kula cewa, sava wa wannan tsari a matsayinsa na mafi dacewa da cancanta, baa bin qyama ba ne a duniyar Sunna. Iyakar abin da za a ce, mutum ya far abin da yake shi ne mafifici. Wato, kamar a wayi gari babba ya zamana shi ne yake fara yi wa qarami sallam. Koko wanda yake tafiya qasa, ya fara yi wa wanda yake kan wani abin hawa, da matara kama da haka.
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Anas xan maliku raliyallahu anhu, cewa: “Wata rana yana tafiya tare da Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. Sai suka yi kicivis da wasu yara qanana, Manzon Allah kuma sallallahu alaihi wa sallam ya yi musu sallama.” (Buhari:6247/ Muslimu:2168).
Raya wannan Sunna ta yi wa qananan yara sallama, wani babban makami ne na yaqar girman kai da son zuciya, da kuma karantar da su yaran, wanann babbar Sunna, tare raya ta a cikin zukatansu.
Yin sallama idan za a shiga gida, wani babban rukuni ne na raya Sunnar sallama. Sai dai ana yin ta ne bayan an yi asawaki. Saboda yin asawaki idan za a shiga gida, Sunna ce tabbatatta, a matsayin gida wuri na huxu, inda Sunnar asawaki take da matuqar xarfi da nauyi, wato lokacin da mutum zai jefa qafarsa a cikin gida. Hujja a kan wannan Sunnan kuwa ita ce, Hadisin Sayyida A’isha ralyallahu anha, wanda yake a wurin Muslimu, inda ta ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance, duk lokacin da zai shiga gida, yakan fara da yin asawaki.” (Muslimu:253). Idan ya yaye kallabin shiga gidansa da asawaki, sallallahu alaihi wa sallam, sai kawai ya shiga tare da yi wa iyalinsa na wannan gida sallama. Bisa wannan dalili ne wasu Malamai suka dogara, suka yanke hukuncin cewa, Sunna ce mutum ya yi sallama idan zai shiga gida. koma wane irin gida ne; ko wanda babu kowa a cikinsa ne. Suka qarfafa wannan hukunci da faxar Allah Maxaukakin Sarki: “Kuma idan za ku shiga gidaje, to, ku yi wa kanku sallama; gaisuwa mai albarka mai tsarki, daga wurin Allah. kamar haka ne Allah yake bayyana ayoyi gare ku, tsammanin ku, za ku hankalta.” {Nur:61}
Malam Ibnl- Hajar rahimahullahu ya ce: “Bakandamen umarni da Sunna ta yi da yawaita sallama, ya haxa har da yi wa kai ita ga wanda zai shiga wurin da babu kowa a cikinsa. Hujja kuwa ita ce: faxar Allah Maxaukakin Sarki: “Kuma idan za ku shiga gidaje, to, ku yi wa kanku sallama…” Don qarin bayani ana iya duba: “Fathul- Bárí Hadisi mai lamba:6235: Babin Yawaita Sallama.”
.Darussa: Abin da ya gabata yana karantar da cewa akwai Sunnoni uku a kan wanda zai shiga gida:
Sunna ta farko: Ambaton Sunan Allah Maxaukakin Sarki, musamman idan da dare ne.
Hujja a kan wannan Sunna, ita ce: Hadisin Jabiru xan Abdullahi raliyallahu anhuma, cewa, ya ji Annabi sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Idan mutum zai shiga gidansa, ya ambaci Allah a lokacin shigar da lokacin da zai fara cin abinci. Sai Shaixan ya ce: Ya ku jama’ata! Ku sani yau kam, ba mu da wurin kwana ko abinci a cikin wannan gida. Idan kuwa ya shiga ba tare da ya ambaci suna Allah ba. Sai Shaixan ya ce: Ya ku jama’ata! Ku sani yau kam, mun sami wurin kwana a cikin wannan gida. Idan kuma bai ambaci Sunan Allah ba a lokacin da zai fara cin abinci. Shaixan ya ce: Ya ku jama’ata! Yau kam, mun sami wurin kwana da abinci a cikin wannan gida.” (Muslimu:2018).
Sunna ta biyu: Yin asawaki. Hujja a kan wannan Sunna kuwa ita ce: Hadisin Sayyida A’isha raliyallahu anha, wanda bayanin matani da isnadinsa suka gabata a baya kaxan.
Sunna ta uku: Yin sallama ga waxanda suke cikin gidan:
Haka Annabi sallallahu alaihi wa salam ya kasance yana yi, kamar yadda ya zo a cikin hadisin Miqdad xan Aswad raliyallahu anhu, wanda a cikinsa yake cewa: “Mun kasance mukan tatso nono, kowa daga cikinmu ya sha gwargwadon rabonsa. Shi ma Annabi sallallahu alaihi wa sallam, mu kai masa nasa rabo.” Miqdad ya ci gaba da cewa: “Idan a cikin dare ne sallallahu alaihi wa sallam ya zo, sai mu ji ya yi sallama cikin sassauqar murya irin yadda ba zai tayar da wanda yake bacci ba. Amma, kuam duk wanda yake farke sai ya ji shi.” (Muslimu:2055).
Isar da saqon sallama Sunna ne. Kamar wani ya gaya maka cewa: “Ka ce ina gaida wane.” To, isar da wannan saqo na gaisuwa zuwa ga wanda aka ce a kai wa shi, Sunna ne.
Hujja a kan wannan Sunna, ita ce: Hadisin Sayyidah A’isha raliyallahu anha, cewa, Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya tava gaya mata cewa: “Mala’ika Jibrilu ya ce yana gaida ke.” Ta ce: “Sai na ce masa: ka gaya masa: ina amsawa: (wa alaihisalámu wa rahamatulláhi.) (Muslimu:2447).
Wannan Hadisi yana karantar da cewa, isar da saqon sallama ga wanda aka aika was hi, Sunna ne, kamar yadda Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya isar da saqon sallamar Mala’ika Jibrilu zuwa ga Sayyidah A’isha raliyallahu anha. Haka kuma wannan Hadisi day a gabata, ya isa hujja a kan cewa, bayar da saqon sallam ta hannun wani zuwa ga wani, Sunna ne.
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abu Hurairah raliyallahu anhu, wanda ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Idan xayanku ya kai wani wuri da mutane suka zama, to, ya yi sallama. Idan kuma ya yi nufin tashi, ya yi sallama. Wadda ya yi can farko, ba ta fi wannan da zai yi qarshe muhimmanci ba.” (Ahmad:9664/ Abu dawuda:5208/ Tirmizi:2706). Albani kuma ya inganta shi: Sahíhul- Jámi’i: (1/132).
Idan haxuwa ce aka yi za a yi wa juna sallama, Sunna ne a haxa hannuwa a yi musáfahá. Wananna shi ne abin da Sahabbai raliyallahu anhum suka kasance suna yi. Hujja kuma a kan haka, ita ce: Hadisin Qatadah raliyallahu anhu, inda ya ce: “Na ce wa Anas: Shin ko Sahabban Annabi sallallahu alaihi wa sallam kan yi musfaha a lokacin rayuwarsu? Sai ya karva mani da cewa: “Tabbas! suna yi.” (Buhari:6263).
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abu Zarrin raliyallahu anhu, da ya ce: “Wata rana Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce mani: “Kada ka yi wa aikin alhairi kallon hadarin kaji, komai qanqantarsa; ko da ka saki fuska ne a lokacin da ka haxu da xan’uwanka.” (Muslimu:2626). Riwayar Tirmizi kuma, daga Abu Zarrin xin raliyallahu anhu, cewa ta yi: Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Murmushin da za ka yi wa xan’uwanka idan kun haxu, sadaqa ne.” (Tirmizi:1956). Albani kuma ya inganta shi a cikin: As- Sahíhát:572).
Yi wa xan’uwa musulmi, wanda aka haxu da shi kan hanya, ko ake zaune wuri xaya tare da shi, ko ake cikin halin wani aiki. Yi masa kyakkawar magana Sunna ne, saboda hukuncin da aka yanke mata na zaman sadaka.
Hujja a kan wannan Sunna, ita ce: Hadisin Abu Huraira raliyallahu anhu wanda ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Kyakkyawar magana sadaqa ce.” (Buhari:2989/ Muslimu:1009).
Rashin niyyar raya wannan Sunna, ya sa da yawa mutane suke ta musayar kyawawan kalmomi a tsakaninsu, waxanda, inda sun yi hakan da nufin neman lada ga Allah Maxaukakin Sarki, da sun kwashi gagarumar garavasa da babban rabo a kan wanann sadaka da suke ta yi ba tare da sun sansance ba.
Malaminmu Ibn Usaimin rahimahullahu ya ce: “Kyakkyawar magana ita ce, kamar ka ce wa xan’uwanka: Ya kake? Wace ake ciki? A sauran dangi?
Ya iyalinka? Da sauran kalmimi masu kama da waxannan. Duk, kyawawan kalmomi ne saboda irin yadda suke sanya farin ciki da jin daxi a cikin ran wanda aka yi wa su a matsayinsa na xan’uwa. Babu wata kalima irin wannan kyakkyawa, da za ta fito daga bakin musulmi, face Allah Maxaukakin Sarki ya ba shi lada da sakamako irin na wanda ya yi sadaka, a kanta. Don qarin bayani ana iya duba: “Sharhu Riyádhus- Sálihína wallafar Malamin nanu: 2/996” babin da yake magana a kan mustahabbancin furta kyakkyawan magana da sakin fuska a lokacin da aka haxu da juna.
Hadisan da suke magana da kwaxaitarwa a kan kafa wuraren zama, inda za a riqa ambaton Allah Maxaukakin Sarki, suna da matuqar yawa. Daga cikin irin waxannan Hadisai akwai Hadisin Abu Huraira raliyallahu anhu da ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Lalle Allah Maxaukakin Sarki yana da waxansu mala’iku da suke kaiwa da komowa a saqo-saqo da lungu-lungu, suna nema da cigiyar masu ambaton Allah. idan suka taras da wasu mutane suna zikirin Allah, sai su buxa baki su yi yekuwa, su ce musu: maza ku taho! Allah ya karva bukatunku. Ya ce: “Sai nan take mala’ikun su lulluve mutanen da fikafikansu, su cira da su zuwa samar duniya….” (Buhari:6408/ Muslimu:2689).
Hujja a kan wannan Sunne ita ce, Hadisin Abu Hurairah raliyallahu anhu, da ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Duk wanda ya zauna a wata Majalisa, ya miqe qafa ya yi ta sharholiya son ransa. Amma, kafin ya bar wurin sai ya karanta: “Subhánakalláhumma wa buhamdika, ash’hadu allá’iláha illá anta, astagfiruka wa a túbu ilaika. (Tsarki da gogiya sun tabbata gare ka, tare ka ya Ubangiji! Ina shaida babu abin bautawa da gaskiya sai kai. Ina neman gafararka, ina kuma tuba zuwa gare ka.) Ba wanda zai faxi wannan addu’a, face Allah Maxaukakin Sarki ya gafarta masa zunuban duk day a xauka a wannan Majalisa.” (Tirmizi:3433). Albani kuma ya ainganta shi a cikin: “Sahíhul- Jámi’i:2/1065”