brightness_1
Farawa da Bisimillah
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin da aka samo daga Umar xan Abu Salma raliyallahu anhu, wanda ya ce: “A matsayina na yaro qarami wanda yake dagwainiya a xakin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. wata rana ana cin abinci, hannuna yana kaiwa da komowa a cikin akushi. Sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, ya ce mani: “Ya kai wannan xan qaramin yaro! Ka ambaci sunan Allah, sa’annan ka ci da hannunka na dama, ka kuma ci abin da yake a gabanka.” (Buhari:5376/ Muslimu:2022).
Idan kuma mutum ya manta bai yi bisimillah ba a farkon cin abincinsa. To, ya samu a Sunnance, idan ya tuna, ya ce: “Bismilláhi awaluhú wa ákhiruhú.” (Da sunan Allah na qare, da shi kuma na fara).
Hujja a kan wannan kuwa ita ce, Hadisin Sayyida A’isha raliyallahu anha, cewa, tabbas! Manzon Allah sallallahu alaihiwa sallam ya ce: “Idan xayanku zai ci abinci, to, ya ambaci sunan Allah. Idan kuma ya manta bai ce bismilláhi ba a lokacin da zai fara cin abincin. To, a qarshe yana iya cewa: “Bismilláhi awaluhú wa ákhiruhú. (Da sunan Allah na qare, da shi kuma na fara). [Abu Dawuda:3767/ Tirmizi:1858]. Albani kuma ya inganta shi kamar yadda bayani ya gabata.
Wani abu kuma da wannan Hadisi yake karantarwa shi ne, bukatar da take akwai ta musukmi ya riqa cin abinci da hannun dama, don kada ya yi kama da Shaixan. Duk lokacin da musulmi ya qi ambaton sunan Allah Maxaukakin Sarki a lokacin da zai fara cin abinci. To, ya sani hannunsa fa hannun Shaixan a cikin wannan akushi; tare za su ci su kuma canye. Haka nan kuma idan ya ci da hannun hagu. To, dashi da Shaixan babu wani banbanci, saboda Shaixan shi yake cin abinci, yake kuma shan abin shad a hannun hagu.
Hujja a kan wannan Sunna:
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin abdullahi xan Umar raliyallahu anhu, cewa, ta tabbata Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Kada wanda ya kusura ya ci abinci da hannun hagu daga cikinku; kada kuma ya sha abin sha da shi. Ba don komai ba kuwa, sai don saboda Shaixan shi ne yake ci da shad a hannun hagu.” Mai riwaya ya ce, Nafi’u yakan qara a cikin wannan riwaya da cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya qara da cewa: “Kada kuma mutum ya karva, ko ya bayar da wani abu da hannun hagu.” (Muslimu:2020).
Wannan umarni na Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam kuwa, ya biyo bayan masaniyar da yake da ita a kan xabi’ar Shaixan, ta son kutsa kai a cikin gidajen mutane, domin yakwana a ciki, ya kuma ci abinci, ya sha abin sha, tare da masu gidajen. Hujja a kan hakan kuwa ita ce, abin da aka riwaito daga Jabiru raliyallahu anhuma, cewa, ko shakka babu, ya ji Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Idan xayanku ya shiga gidansa, ya kuma ambaci sunan Allah a lokacin da zai shiga xin, da kuma lokacin da zai fara cin abinci. Sai Shaixan ya ce: Tir! yau kam ba mu dace ba; ba mu da wurin kwana ba mu kuma da abincin dare. Ida mutum bai ambaci sunan Allah a lokacin da zai shiga ba, sai Shaixan ya ce: Madallah! Yau kam munsami wurin kwana. Idan kuma mutum bai ambaci sunan Allah ba a lokacin da zai fara cin abinci, sai Shaixan ya ce: Yauwa! Mun sami abin kalacin dare.” (Muslimu:2018).