Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin da aka samo daga Umar xan Abu Salma raliyallahu anhu, wanda ya ce: “A matsayina na yaro qarami wanda yake dagwainiya a xakin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. wata rana ana cin abinci, hannuna yana kaiwa da komowa a cikin akushi. Sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, ya ce mani: “Ya kai wannan xan qaramin yaro! Ka ambaci sunan Allah, sa’annan ka ci da hannunka na dama, ka kuma ci abin da yake a gabanka.” (Buhari:5376/ Muslimu:2022).
Idan kuma mutum ya manta bai yi bisimillah ba a farkon cin abincinsa. To, ya samu a Sunnance, idan ya tuna, ya ce: “Bismilláhi awaluhú wa ákhiruhú.” (Da sunan Allah na qare, da shi kuma na fara).
Hujja a kan wannan kuwa ita ce, Hadisin Sayyida A’isha raliyallahu anha, cewa, tabbas! Manzon Allah sallallahu alaihiwa sallam ya ce: “Idan xayanku zai ci abinci, to, ya ambaci sunan Allah. Idan kuma ya manta bai ce bismilláhi ba a lokacin da zai fara cin abincin. To, a qarshe yana iya cewa: “Bismilláhi awaluhú wa ákhiruhú. (Da sunan Allah na qare, da shi kuma na fara). [Abu Dawuda:3767/ Tirmizi:1858]. Albani kuma ya inganta shi kamar yadda bayani ya gabata.
Wani abu kuma da wannan Hadisi yake karantarwa shi ne, bukatar da take akwai ta musukmi ya riqa cin abinci da hannun dama, don kada ya yi kama da Shaixan. Duk lokacin da musulmi ya qi ambaton sunan Allah Maxaukakin Sarki a lokacin da zai fara cin abinci. To, ya sani hannunsa fa hannun Shaixan a cikin wannan akushi; tare za su ci su kuma canye. Haka nan kuma idan ya ci da hannun hagu. To, dashi da Shaixan babu wani banbanci, saboda Shaixan shi yake cin abinci, yake kuma shan abin shad a hannun hagu.
Hujja a kan wannan Sunna:
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin abdullahi xan Umar raliyallahu anhu, cewa, ta tabbata Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Kada wanda ya kusura ya ci abinci da hannun hagu daga cikinku; kada kuma ya sha abin sha da shi. Ba don komai ba kuwa, sai don saboda Shaixan shi ne yake ci da shad a hannun hagu.” Mai riwaya ya ce, Nafi’u yakan qara a cikin wannan riwaya da cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya qara da cewa: “Kada kuma mutum ya karva, ko ya bayar da wani abu da hannun hagu.” (Muslimu:2020).
Wannan umarni na Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam kuwa, ya biyo bayan masaniyar da yake da ita a kan xabi’ar Shaixan, ta son kutsa kai a cikin gidajen mutane, domin yakwana a ciki, ya kuma ci abinci, ya sha abin sha, tare da masu gidajen. Hujja a kan hakan kuwa ita ce, abin da aka riwaito daga Jabiru raliyallahu anhuma, cewa, ko shakka babu, ya ji Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Idan xayanku ya shiga gidansa, ya kuma ambaci sunan Allah a lokacin da zai shiga xin, da kuma lokacin da zai fara cin abinci. Sai Shaixan ya ce: Tir! yau kam ba mu dace ba; ba mu da wurin kwana ba mu kuma da abincin dare. Ida mutum bai ambaci sunan Allah a lokacin da zai shiga ba, sai Shaixan ya ce: Madallah! Yau kam munsami wurin kwana. Idan kuma mutum bai ambaci sunan Allah ba a lokacin da zai fara cin abinci, sai Shaixan ya ce: Yauwa! Mun sami abin kalacin dare.” (Muslimu:2018).
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Umar xan abu Salmata raliyallahu anhu, wanda ya gabata, wanda a cikinsa ya ce, Annabi nsallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Ka kuma ci abin da yake gabanka.”
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin da aka samo daga Umar xan Abu Salma raliyallahu anhu, wanda ya ce: “A matsayina na yaro qarami wanda yake dagwainiya a xakin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. wata rana ana cin abinci, hannuna yana kaiwa da komowa a cikin akushi. Sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, ya ce mani: “Ya kai wannan xan qaramin yaro! Ka ambaci sunan Allah, sa’annan ka ci da hannunka na dama, ka kuma ci abin da yake a gabanka.” (Buhari:5376/ Muslimu:2022).
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Jabiru raliyallahu anhu, wanda ya ce: “Na ji Annabi sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Lalle haqiqa, Shaixan yana kawo wa kowane daga cikinku hari a duk lokacin da yake wani abu na sha’anin rayuwa, har lokacin day a zauna zai ci abinci kuwa. Saboda haka idan lomar xayanku ta faxi qasa. To, ya kakkave qazantar da ta xauko, sa’annan ya jefa ta baka; kada ya bar wa Shaixan ita. Idan kuma ya qare cin abincin, ya tabbata ya lashe ‘yan yatsunsa, domin bai san a cikin wane sashe na abincin da ya ci, albarka take ba.” (Muslimu:2033).
Duk wanda ya kallai wannan Hadisi da idon basira, zai tattaba cewa, lalle abin da yake faxi gaskiya ne. Shaixan yana matuqar sha’awa da qoqarin tarayya da mutane a cikin gaba xayan al’amurransu. Ba kuwa don komai ba, sai don ya xebe musu albarkar da take cike da rayuwarsu, wanda hakan zai zama sanadin dagulewar da yawa daga cikin al’amurransu. Daga cikin abubuwan kuma da suke tabbatar da kwaxayi da qalailaicewarsa, Shaixan, a cikin kowane al’amari, shi ne faxar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam: ““Lalle haqiqa, Shaixan yana kawo wa kowane daga cikinku hari a duk lokacin da yake wani abu na sha’anin rayuwa.”
Lashe ‘yan yatsun hannu bayan qare cin abinci ta hanyar amfani da halshe, Sunna ne. Ko dai mutum ya yi da kansa, ko ya miqa wa matarsa ta yi masa, misali. Kai! a sunnance ma, ba a son mutum ya goge xan saurana bin day a laqe a hannunsa na abinci, da wani qyalle, ko wani abu mai kama da shi, sai bayan ya lashe su, sarai.
Hujja kan wannan Sunna, ita ce: Hadisin Jabiru raliyallahu anhu, wanda ya gabata.
Ya kuma zo a cikin ingantattun littafan nan na Hadisi guda biyu, daga cikin Hadisan xan Abbas raliyallahu anhuma cewa, Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Idan xayanku ya qare cin abinci, kada ya goge hannunsa har sai ya lashe ko ya tsoste shi sarai.” (Buhari:5456/ Muslimu:2033).
Abin da ake nufi da suxe akushi, shi ne tsabtace abin da mutum ya ci abinci a cikinsa, ko ma mene ne. Misali, idan mutum ya ci shinkafa, to, Sunna ta xora masa nauyin kada ya bar ko qwara xaya a cikin abin da ya ci shinkafar a cikinsa. A maimakon haka, sai ya yi qoqari iyakar yin sa, ya yaye komai da komai ya lankahe a cikin baki. Ba kuwa don komai Sunna ta xara masa wannan nauyi ba, sai don abu ne mai matuqar yiwuwa ya zamana albarkar abincin tana nan cikin na qarshen nan.
Hujja a kan wannan Sunna, ita ce: Hadisin Anasa raliyallahu anhu, wanda ya ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya umarce mu da suxe akussanmu.” (Muslimu:2034). A cikin wata riwayar kuma ta shi Musulimu xin, daga cikin Hadisan Abu Hurairah raliyallahu anhu, ya ce, cewa Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya yi: “Xayanku duk, ya tabbata ya suxe akushinsa.” (Muslimu:2035).
Malaminmu Ibn Usaimin rahimahullahu ya ce: “Abin da suxe akushi yake nufi, shi ne mutum ya bi diddigin duk sauran abin da ya lallaqe a yatsunsa, ya lashe shi sarai. Wannan Sunna kuwa, an wayi gari a yau ta zama xaya daga cikin Sunnonin da, da yawa daga cikin mutane suka fara mantawa da su. babban abin baqin ciki ma, hard a xaliban ilimi. Don qarin bayani ana iya duba: “Sharhu Riyadhus- Sálihína: 1/892”
Sunna ne idan mutum zai ci abinci, ya yi amfani da ‘yan yatsunsa guda uku, matuqar abin da zai ci xin nan yana xaukuwa da yatsa uku xin, kamar dabino. To, a sunnance an fi so ya riqa sa yatsunsa guda uku yana xakowa yana jefawa baka.
Hujja a kan wannan Sunna, ita ce: Hadisin Ka’abu xan Maliku raliyallahu anhu, wanda ya ce: “manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yana cin abinci da ‘yan yatsu uku. Yakan kuma lashe hannunsa sarai, kafin ya goge da wasu tsumma.” (Muslimu:2032).
Idan mutum zai sha wani abin sha, Sunna ita ce, ya riqa yi yana xaukewa yana kuma numfasawa a wajjen qwaryar, har sau uku; yana yi yana numfasawa bayan kowace qyanqyama xaya.
Hujja a kan wannan Sunna, ita ce: Hadisin Anas raliyallahu anhu, wanda ya ce: manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yana numfasawa wajjen qwaryar shansa har sau uku, sa’annan ya ce: “Yin haka ya fi kashe qishirwa, da bayar da lafiya, ya kuma fi nagarta.” Anas raliyallahu anhu ya ci gaba da cewa: “Saboda haka nake numfasawa wajjen qwaryar shana har sau uku,” (Buhari:563/ Muslimu:2028).
Abin da ake nufi da cewa, Annabi sallallahu alaihi wa sallam yana numfasawa wajjen qwaryar shansa, shi ne, yana xauke kai ya karkata fuskarsa gefe xaya ya numfasa, sa’annan ya mayar ya ci gaba da qyanqyamar abin da yake sha. Yana yin haka ne sallallahu alaihi wa sallam, saboda numfasawa a cikin qwaryar sha xin, makaruhi ne a sunnance, kamar yadda Hadisin Abu Qatadah raliyallahu anhu, wanda yake a cikin ingantattun littafan Hadisi guda biyu, ya nuna, inda ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Idan xayanku zai wani abin sha, to, kada ya numfasa a cikin qwaryar,” (Buhari:5630/ Muslimu:267).
Hujja a kan wannan Sunna:
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Anas xan Maliku raliyallahu anhu, wanda ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Allah Maxaukakin kan yarda da bawansa, ya kuma amince da shi, saboda xai ya ci ya qoshi ya kuma gode masa a kan haka, ko ya sha ya qoshi ya kuma gode masa a kan haka.” (Muslimu:2743).
Godiyar nan kuma, tana da sigogi daban-daban, da suka haxa da:
a) “Alhamdu lilláhi kasíran xayyiban mubárakan gaira makfíyin, walá muwadda’in, walá mustagnan anhu Rabbaná!” (Godiya mai tarin yawa, da tsarki, da albarka, ta tabbata ga Allah. Sarkin da ba shi da bukata ga wani abin halitta, babu kuma wani abin halitta da ba shi da bukata gare sh, ko wadatuwa daga gare shi, ya Ubangijinmu!)
b) “Alhamdu lilláhillazí kafáná wa’arw’aná gaira makfíyin walá mukafúrin.” ((Godiya ta tabata ga Allah, Sarkin da ya qosar da mu, ya kuma kashe mana qishirwa; ba tare dam un raina ko mun kafirce ba.) (Buhari:5459).
A qarqashin inuwar wannan “rashin bukata’ ga wani mahaliki ne, sifa wadda da Allah Maxaukakin Sarki ya kevanta da ita, yake ciyar da bayinsa ya kuma qosar da su. Saboda haka babu yadda za a yi su iya “wadatuwa” daga gare shi subhanahu wa ta’alah, a matsayinsa na Sarkin da yake “Qosarwa” da “Kashe musu qishirwa.” Saboda haka ba za su zama daga cikin masu “kafirce wa” falala da ni’imarsa ba subhanahu wa ta’alah.
Yana daga cikin Sunna, idan musulmi za su ci abinci a wuri xaya, to, su haxu su ci tare da juna. Sunna ta qyamaci cin abinci rarrabe.
Hujja a kan wannan Sunna, ita ce: Hadisin Jabiru xan Abdullahi raliyallahu anhuma, wanda ya ce: “Na ji Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “abincin mutum xaya yana isar mutum biyu, na mutum biyu kuma yana isar mutum huxu, na huxu kuma yana isar takwas.” (Muslimu:2059).
Sunna ce idan musulmi ya ci abinci, ya kuma ji ya yi masa daxi, ya yaba. Amma, kada ya wuce wuri ta hanyar qara wa kalmomin yabon nasa gishiri fiye da abin da abinci yake xauke da shi.
Hujja a kan wannan Sunnan, ita ce: Hadisin Jabiru xan Abdullahu raliyallahu anhu, cewa, wata rana Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya nemi iyalan gidansa su ba shi rovvi ya haxa da gurasa ya yi kalaci. Sai suka gaya masa cewa: “Rovvi kam ya qare, amma a kwai sauran rummace.” Sai ya ce, a kawo masa shi. Aka kuwo, ya mayar da hankali yana haxa gurasar nan das hi, yana lankahewa baka, yana kuma cewa: “Kai! rovvi da gurasa akwai daxi! Kai! rovvi da gurasa akwai daxi!!” (Muslimu:2052). Kalimar ‘khallu’ ta Larabci da muka fassara da ‘rovvi’ a cikin wannan Hadisi, wani nau’in mahaxin cin abinci ne a waccan zamani, mai daxin gaske, ba kuma mai nauyi da kabri ba kamar wanda muke da shi a yau.
Malaminmu Ibn Usaimin rahimahullahu ya ce: “Yaba abinci da Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yake yi idan ya burge shi, wata koyarwa ce tasa sallallahu alaihi wa sallam zuwa ga al’umarsa. Sadoda haka, yau da mutum zai yi kalaci da waina, ta ratsa shi iyakar zarafi. Sai ya kayar da baki ya ce: “Kai! wainar gidansu wance akwai daxi.” Ko wani abu mai kama da haka. wanda duk ya yi irin haka, ya raya Sunna daga cikin Sunnonin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. Don qarin bayani sai a duba: “Sharhu Riyádhus- Sálihína: 2/1057)
Duk wanda ya kalli yanayin rayuwarmu na yau da kyau, zai fahimci irin yadda mutane suke yin nesa-nesa da Sunnanr Annabi sallallahu alaihi wa sallam. Wasu ma ba su tsaya a kan yin nesa-nesa da ita xin ba, har sava mata suke yi, ta hanyar aibanta wani abinci da suka ci, tare da kushe shi a wasu lokuta. Irin haka kuwa ya sava wa Sunna da koyarwar Annabi sallallahu alaihi wa sallam. Alhali kuwa, ya zo a cikin ingantattun littafan Hadisai guda biyu, daga cikin Hadisan Abu Huraira raliyallahu anhu, wanda ya ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam bai tava buxa baki ya kushe wani abinci ba. In dai ya ji yana sha’awarsa zai ci. Idan kuma ba ya sha’awarsa zai bar shi baki alaikum.” (Buhari:3563/ Muslimu:2063).
Hujja a kan wannan Sunna, ita ce: Hadisin Abdullahi xan Busrin raliyallahu anhu, wanda ya ce: “Wata rana Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya baqunci mahaifina. Sai muka kawo masa abinci da dabino. Qare cin abincin nasa yake da wiya, sai muka qara kusanto masa da watarnen dabinon nan. Bai yi wata-wata ba kuwa ya shiga tsinta yana ci, yana kuma jefar da qwallayensa ta tsakiyar ‘yan yatsunsa sallallahu alaihi wa sallam, tare da gwama manunin da xan tsakiyar yatun nasa. Daga nan kuma aka kawo masa abin sha, ya karva ya sha, sa’annan ya miqa wa wanda yake zaune a damansa. Kafin ya kama hanyar komawa, sai mahaifina ya kama ragwamar dabbar da ya zo a kanta sallallahu alaihi wa sallam, ya ce: “Ka roqar mana Allah kafin ka wuce ya Manzon Allah!” Sai Annabi sallallahu alaihi wa salam ya ce: “Alláhumma bárik lahum fímá razaqtahum, wagfir lahum, warhamhum.” (Ya Ubangiji! Ka sanya albarka a cikin abin duk da ka arzuta su das hi, ka kuma gafarta musu. Sa’annan ka yi musu rahama.) (Muslimu:2042). Kalimar “waxbah” ta Larabci a cikin wannan Hadisi ce, muka fassara da ‘kwatarne’
Abin da ake nufi shi ne, yana daga cikin Sunna, a daidai lokacin da mutum ya qyanqyami wani abin shay a qoshi. To, idan ya xauke kansa daga kwatarnen, ya gaggauta miqa wa mutumin da yake dama gare shi, kafin wanda yake haxu gare shi.
Hujja a kan wannan Hadisi, ita ce: Hadisin Anas xan Maliku raliyallahu anhu, wanda ya ce: “Wata rana Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kai baqunci a gidanmu, ya kuma nemi wani xan abin da zai sha. Sai muka kama wata akuya muka tatso masa nononta, sa’nan na haxa masa da rowan rijiyar nan tawa.” Anas ya ci gaba da cewa: “Sai na miqa wa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, ya karva ya kafa kai, ya sha ya qoshi. Duk wannan abu da yake faruwa, Sahabi Abubakar raliyallahu anhu yana zaune hagu ga Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, umar kuma yana dabra da fuskarsa, a yayin da wani balaraben qauye yake a damansa sallallahu alaihu wa sallam. Qarewarsa take da wuya, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, sai ya, sai Sayyadi Umar raliyallahu anhu ya muma nuna Abubakar raliyallahu anhu ya kuma ce wa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam: “Ga Abubakar nan ya Manzon Allah.” Amma, sai Manzon Allah ya miqa wa Balaraben qauyen nan, ya qyale Abubakar da Umar. Ya kuma qara da cewa musu sallallahu alaihi wa sallam: “A yi dama dai! A yi dama dai!! A yi dama dai!!!” Anas ya ce: “Yin haka Sunne ne! Yin haka Sunne ne!! Yin haka Sunne ne!!!” (Buhari:2571/ Muslimu:2029).
Sunna ne wanda yake shayar da mutane wani abin sha, ya kasance shi ne wanda zai sha abin bayan kowanensu y agama sha.
Hujja a kan wannan Sunna, ita ce: Hadisin nan na mai tsawo na Abu Qatadah raliyallahu anhu, wanda a cikinsa yake cewa: “… sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya shiga zuba ruwa a kofi ni kuwa ina miqa wa mutane suna sha. Har sai da kowa ya sha ya qoshi, sai ni kawai das hi Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam muka rage, waxanda ba su sha ba.” Anas raliyallahu anhu ya ci gaba da cewa: “Sa’annan Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya sake zubawa, ya ce mani: “karvi ka sha, Anas.” Ni kuwa na ce masa: “Ba zan sha bay a Manzon Allah, sai ka sha.” Sai ya karva mani da cewa: “Ai, wanda yake shayar da mutane, shi ya kamata ya sha qarshe.” Ansa ya ce: “To, sa’annan sai na karva na sha, Manzon Allah kuma ya sha….” (Muslimu:681).
Darasi: Wani darasi kuma da yake cikin wannan babi, shi ne bukatar da take akwai a sunnance, ta kurkure baki da ruwa ga wanda ya sha nono, domin ya kawar da masqin da yake da shi, wanda ya kama bakinsa. Hujja a kan wannan Sunna kuwa, ita ce: Hadisin xan Abbas raliyallahu anhuma, da ya ce: “Ta tabbata cewa, wata rana Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya sha nono. Sai ya nemi a kawo masa ruwa, ya kurkure baki, ya kuma ce: “Na yi haka ne domin nono yana da masqi.” (Buhari: 211/ Muslimu: 358).
Sunna ce idan dare ya kawo jiki, a rufe gaba xayan qoran da ake da su a gida, waxanda suke buxe, a kuma rufe riyoji idan suna da marafe, a kuma tabbata an ambaci suna Allah a duk lokacin da za a raya wannan Sunna.
Hujja a kan wannan Sunna, ita ce: Hadisin Jabiru xan Abdullahi raliyallahu anhuma, wanda ya ce: “Na ji Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Ku rufe qorai, ku saya riyoji, domin a cikin kowace shekara a kwai daren da alloba take sauka a cikinsa, wadda ba za ta shuxe a kan duk wata qwarya da wara rijiya, waxanda ba rufe ba, face wani abu daga cikin wannan alloba ya sauka a cikinsu.” (Muslim:2014). A riwayar Buhari kuma, daga cikin Hadisan Jabiru raliyallahu anhuma, cewa aka yi Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Ku tottoshe bakunan shnatullanku, ku kuma ambaci sunan Allah. Sa’annan ku xaukar wa qoranku mataki, ko da ta hanyar yafa wani abu a kansu ne; ku kuma ambaci sunan Allah.” (Buhari:5623).