brightness_1
Neman Sahun Farko
Sunna ce idan mutum ya shiga Masallaci, ya yi qoqarin samun shiga sahun farko, musamman namiji. Domin sahun farko shi ne mafi girma da xaukaka, da dacewa da xa namiji. Su kuwa mata, sahun qarshe shi ya fi dacewa da su. Hujja a kan wannan sunna kuwa, ita ce Hadisin Abu Huraira raliyallahu anhu, inda ya ce, Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “mafi alhairin sahu ga maza, shi ne sahun farko. Mafi sharrisa kuma gare su, shi ne sahun qarshe. Mafi alhairin sahu kuma ga mata, shi ne sahun qarshe. Mafi sharrinsa kuma gare su, shi ne sahun farko.” (Muslimu:440/). Mafi alhairi na nufin: Mafifici lada da falala. Mafi sharri kuma na nufin: Mafifici qarancin lada da falala.
Sai dai a lura. Wannan Hadisi yana aiki ne, a idan maza da mata suka sami kansu a Masallaci xaya domin yin salla cikin jami’i, babu kuma wani shamaki na qyalle ko bango, ko wani abu mai kama da haka, a tsakaninsu. To, a nan ne ake cewa, mafi alhairin sahu ga mata, shi ne sahun qarshe. Ba kuwa don komai ba, sai don ya fib a su sutura da kariya daga idanun mazaje. Amma, idan akwai wani shamaki a tsakaninsu, na bango ko matara kama da shi. Ko kamar yadda take faruwa a mafi yawan Masallatanmu nay au, inda ake ware wa mata wurin sallarsu na musamman. To, a irin wannan hali, su ma mata, mafi alhairin sahu gare su, shi ne sahun farko, can a tsakaninsu. Saboda wancan dalili na zamansu kusa da maza, ya kau. Saboda a qa’idar tsago hukunce-hukunce, hukunci, kowane iri ne, yana samin gindin zama ne, ko rasa ta, gwargwadon wanzuwar dalilinsa ko rashinta. Wani dalilin kuma shi ne, falalar da take a cikin sahun farko xin, ta kowane hali, kamar yadda wasu Hadisai suka nuna.
Wata hujjar kuma ita ce Hadisin Abu Huraira raliyallahu anhu, har yau, inda ya ce, Annabi sallallahu alaihi wa sllam ya ce: “Inda mutane sun san alhairin da yake cikin kiran salla da sahu na farko, ya kuma zamana ba za su iya samun shiga cikinsa ba sai ta hanyar quri’a, wallahi, da sun yi ta. Inda kuma sun san alhairin da yake cikin quma sakko dimin zuwa Masallaci, da sun yi rigyangyanto yin sa. Inda kuma sun san alhairin da yake cikin sallar Isha’i da ta Subahin, wallahi da sun tafi wurin yin su ko dad a rairahe ne.” (Buhari:615/ Muslimu:437).