Sunna ce ga musulmi ya quma sakko idan zai je Masallaci domin yin sallar Asuba. Hujja a kan wannan Sunna kuwa ita ce, Hadisin Abu Hurairata raliyallahu anhu, inda ya ce: Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Da muslumi sun san alhairin da yake a cikin quma sakko don zuwa Masallaci, da sun yi rigyangyanton yin haka.” (Buhari:615/ Muslim:437).
Quma sakko na nufin: qoqarin rigan kowa Masallaci
Sunna ta tanadi cewa, idan musulmi zai tafi Masallaci domin sallar Asuba, ya yi cikakken tsarki. Hakan zai bayar da damar rubuta masa cikakkar lada a kan kowane takin qasa nasa. Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abu Hurairata raliyallahu anhu, inda ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Sallar da mutum zai yi a cikin jam’i, ta fi wadda za yi a gida da shagonsa lada sau ashirin da wani abu. Wannan lada kuma tana samuwa ne idan mutum ya yi arwalla ya kuma kyautata ta, sa’annan ya tasar wa Masallaci, bad a nufin komai fa, sai salla. To, Babu wani taki da zai yi wa qasa, face an xaukaka darajarsa saboda ita, an kuma shafe masa wani zunubi, har sai ya jefa qafarsa a cikin Masallaci. To, da zarar ya shiga cikin Masallacin, das hi da wanda yake tsaye yana sallar, duk ladarsu xaya, matuqar zaman sallar yake yi. Mala’iku kuma za su ci gaba da salati ga duk wanda ya ci gaba da kasancewa a wurin da ya yi salla, daga cikinku, suna cewa: Ya Ubangiji! Ka yi wa wannan bawa naka rahama. Ya Ubangiji! Ka yi wa wannan bawa naka gafara. Ya Ubangiji! Ka karvi tubar wannan bawa naka, matuqar bai cutar da kowa ba, bai kuma yi abin da zai kare masa arwalla ba.” (Muslimu:649).
An kuma so mutum ya fita a cikin natsuwa da kwanciyar hankali. Hujja a kan wannan Sunna kuma, ita ce, Hadisin Abu Huraira raliyallahu anhu, daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam, ya ce: “Idan kun ji an tayar da iqama, to, ku kama hanya ku nufi Msallaci, amma, ina horon ku da tafiya cikin natsuwa da kwanciyar hankali; kada ku sa gaugawa. Abin da kuka samu, ku sallace shi, wanda kuma ya kubce muku, sai ku cika.” (Buhari:636/ Muslimu:602).
Imamun-Nawawi rahimahullahu ya ce: “Kalimar ‘as-sakínah’ ta Larabci, wadda muka fassara da ‘natsuwa’ ya ce: tana nufin yanayin motsawar gavovin mutum a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Masallaci, da kuma nisantar kowace irin wasa. Kalimar ‘alwaqar’ kuma wadda muka fassara da kwanciyar hankali, na nufin idan zai yi wata magana a kan hanyar tasa, to, ya yi ta cikin kwanciyar hankali. Sa’annan kuma ya nisanci yawan waiwaye-waiwaye marasa dalili.” Don qarin bayani sai a duba: “Sharhu Muslim” wallafar Malamin, Hadisi mai lamba 602, babin da yake magana a kan mustahabbacin tafiya Masallaci cikin natsuwa da kwanciyar hankali, da hani da zuwansa cikin gaugawa.
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, hadisin Anas raliyallahu anhu, inda ya ce: “Yana daga cikin Sunna, idan za ka shiga Masallaci, ka shiga da qafarka ta dama. Idan kuma za ka fito, ka fito da ta hagunka.” (Hakim:1/338), ya kuma inganta shi bisa ma’aunan Imamu Muslim.
Karanta addu’ar da aka samo a Sunna a lokacin shiga Masallaci da fitowa daga cikinsa, yana daga cikin Sunna. Hujja kuwa ita ce, hadisin Abu Humaid, ko Abu Usaid, wanda ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Duk lokacin da xayanku zai shiga Masallaci, to, ya ce: “Alláhummaf-tahlí abwába rahmatika.” Wato: (Ya Ubangiji! Ka buxe mani qofofin rahamarka.) Idan kuma zai fito ya ce: Alláhumma inní as’aluka min fadhalika.” Wato: (Ya Ubangiji! Ina roqon ka wani abu daga cikin falalarka.) (Muslimu:713).
Sunna ne kuma idan ya shiga Masallaci kuma, ya sallaci raka’a biyu a matsayin gaisuwar Masallaci, idan Allah ya sa ya isa da wuri; kada ya zauna sai ya yi waxannan raka’o’i. Hujja a kan wannan Sunna kuwa, ita ce, Hadisin Abu Qatadah raliyallahu anhu, inda ya ce, Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Idan xayanku ya shiga Masallaci, kada ya zauna sai ya sallaci raka’a biyu.” (Buhari:1163/ Muslimu:714).
Idan kuma sallar da mutum ya tafi Masallacin domin yi, tana da raka’o’in nafila na Sunna da ake yi kafinta, kamar na kafin sallar Asuba xin can, da Azuhur, ko sallar Dhuha; idan saboda ita ne aka je Masallacin, ko ta Wuturi idan a Masallaci aka yanke shawarar yin ta, ko kuma wata salla ta farilla. To, idan mutum ya yi waxannan, ba sai ya yi na gaisuwar Masallaci xin nan ba; sun wadatar. Saboda ba komai ake nufi da Gaisuwar Masallaci xin ba, illa hana mutum ya zauna ba tare da ya yi sujada ga Ubangiji ba. Domin hakan wata hanya ce ta raya Masallatai da salloli; ba a son mutum ya shiga ba tare da ya yi wata salla ba.
Sunna ce idan mutum ya shiga Masallaci, ya yi qoqarin samun shiga sahun farko, musamman namiji. Domin sahun farko shi ne mafi girma da xaukaka, da dacewa da xa namiji. Su kuwa mata, sahun qarshe shi ya fi dacewa da su. Hujja a kan wannan sunna kuwa, ita ce Hadisin Abu Huraira raliyallahu anhu, inda ya ce, Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “mafi alhairin sahu ga maza, shi ne sahun farko. Mafi sharrisa kuma gare su, shi ne sahun qarshe. Mafi alhairin sahu kuma ga mata, shi ne sahun qarshe. Mafi sharrinsa kuma gare su, shi ne sahun farko.” (Muslimu:440/). Mafi alhairi na nufin: Mafifici lada da falala. Mafi sharri kuma na nufin: Mafifici qarancin lada da falala.
Sai dai a lura. Wannan Hadisi yana aiki ne, a idan maza da mata suka sami kansu a Masallaci xaya domin yin salla cikin jami’i, babu kuma wani shamaki na qyalle ko bango, ko wani abu mai kama da haka, a tsakaninsu. To, a nan ne ake cewa, mafi alhairin sahu ga mata, shi ne sahun qarshe. Ba kuwa don komai ba, sai don ya fib a su sutura da kariya daga idanun mazaje. Amma, idan akwai wani shamaki a tsakaninsu, na bango ko matara kama da shi. Ko kamar yadda take faruwa a mafi yawan Masallatanmu nay au, inda ake ware wa mata wurin sallarsu na musamman. To, a irin wannan hali, su ma mata, mafi alhairin sahu gare su, shi ne sahun farko, can a tsakaninsu. Saboda wancan dalili na zamansu kusa da maza, ya kau. Saboda a qa’idar tsago hukunce-hukunce, hukunci, kowane iri ne, yana samin gindin zama ne, ko rasa ta, gwargwadon wanzuwar dalilinsa ko rashinta. Wani dalilin kuma shi ne, falalar da take a cikin sahun farko xin, ta kowane hali, kamar yadda wasu Hadisai suka nuna.
Wata hujjar kuma ita ce Hadisin Abu Huraira raliyallahu anhu, har yau, inda ya ce, Annabi sallallahu alaihi wa sllam ya ce: “Inda mutane sun san alhairin da yake cikin kiran salla da sahu na farko, ya kuma zamana ba za su iya samun shiga cikinsa ba sai ta hanyar quri’a, wallahi, da sun yi ta. Inda kuma sun san alhairin da yake cikin quma sakko dimin zuwa Masallaci, da sun yi rigyangyanto yin sa. Inda kuma sun san alhairin da yake cikin sallar Isha’i da ta Subahin, wallahi da sun tafi wurin yin su ko dad a rairahe ne.” (Buhari:615/ Muslimu:437).