languageIcon
search
search
brightness_1 Maimaita kiran salla tare da Ladan

Sunna ne ga duk wanda ya ji Ladan yana kiran salla ya maimata duk abin da yake faxa, amma, ban da wurare biyu. Nan kam sai dai ya ce: “Lá haula wa lá quwwata illá bil-láh.”

Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abdullahu xan Amru xan Asi raliyallahu anhu, cewa, ya ji Annabi sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Idan kuka ji Ladan yana kiran salla, to, ku riqa maimaita duk abin da yake faxi….”  (Muslim:384). Da kuma Hadisin Sayyadi Umar xan Khaxxabi raliyallahu anhu, inda ya ce: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: Idan Ladan ya ce: Allahu Akbar Allahu Akbar, sai ku ce: Allahu Akbar Allahu Akbar. Idan kuma ya ce: Ash’hadu Alla’ilaha illallah, sai ku ce: Ash’hadu Alla’ilaha illallah. Idan kuma ya ce: Ash’hadu Anna Muhammadan Rasulallah, sai ku ce: Ash’hadu Anna Muhammadan Rasulallah. Idan kuma ya ce: Hayya alas-salah, sai ku ce: Lá haula wa lá quwwata illá bil-láh. Idan kuma ya ce: Hayya alal-falah, sai ku ce: Lá haula wa lá quwwata illá bil-láh. Idan kuma ya ce: Allahu Akbar Allahu Akbar, sai ku ce: Allahu Akbar Allahu Akbar. Idan kuma ya ce: La’ilaha illallah, sai ku ce: La’ilaha illallah. Duk wanda ya yi haka da zuciya xaya, zai shiga Aljanna.”  (Muslimu:385).

A wajen farkar da mutane kuma, domin yin sallar Asuba, idan mutum yana maimaita kiran wannan salla, tare da Ladan, to, zai faxi kwatankwacin abin duk da Ladanin ya faxi ne. Idan ya ce: “assalatu khairun minan-naumi”  shi ma sai ya ce: “assalatu khairun minan-naumi.”