Sunna ne ga duk wanda ya ji Ladan yana kiran salla ya maimata duk abin da yake faxa, amma, ban da wurare biyu. Nan kam sai dai ya ce: “Lá haula wa lá quwwata illá bil-láh.”
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abdullahu xan Amru xan Asi raliyallahu anhu, cewa, ya ji Annabi sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Idan kuka ji Ladan yana kiran salla, to, ku riqa maimaita duk abin da yake faxi….” (Muslim:384). Da kuma Hadisin Sayyadi Umar xan Khaxxabi raliyallahu anhu, inda ya ce: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Idan Ladan ya ce: Allahu Akbar Allahu Akbar, sai ku ce: Allahu Akbar Allahu Akbar. Idan kuma ya ce: Ash’hadu Alla’ilaha illallah, sai ku ce: Ash’hadu Alla’ilaha illallah. Idan kuma ya ce: Ash’hadu Anna Muhammadan Rasulallah, sai ku ce: Ash’hadu Anna Muhammadan Rasulallah. Idan kuma ya ce: Hayya alas-salah, sai ku ce: Lá haula wa lá quwwata illá bil-láh. Idan kuma ya ce: Hayya alal-falah, sai ku ce: Lá haula wa lá quwwata illá bil-láh. Idan kuma ya ce: Allahu Akbar Allahu Akbar, sai ku ce: Allahu Akbar Allahu Akbar. Idan kuma ya ce: La’ilaha illallah, sai ku ce: La’ilaha illallah. Duk wanda ya yi haka da zuciya xaya, zai shiga Aljanna.” (Muslimu:385).
A wajen farkar da mutane kuma, domin yin sallar Asuba, idan mutum yana maimaita kiran wannan salla, tare da Ladan, to, zai faxi kwatankwacin abin duk da Ladanin ya faxi ne. Idan ya ce: “assalatu khairun minan-naumi” shi ma sai ya ce: “assalatu khairun minan-naumi.”
Karanta wannan zikiri bayan kalimomin shahada guda biyu
Sunna ne idan Ladan ya qare faxar: “Ash’hadu anna Muhammadan Rasulallahi” ta biyu, wanda yake maimaita kiran sallar tare da shi, ya karanta zikirin nan day a zo a cikin Hadisin Sa’ad raliyallahu anu, wanda aka samo daga Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, cewa, ya ce: “Duk wanda ji Ladan na kiran salla, ya kuma karanta: Ash’hadu allá’iláha illal-láh, wahdahu lá sharíka lahú, wa annan Muhammadan Abduhu wa Rasúluhú. Radhitu billáhi Rabban, wa bi Muhammadin Rasulan, wa bil-Islámi dínan,”an gafarta masa zunubansa.” (Muslimu:376)
Yi wa Annabi sallallahu alaihi wa sallam salati bayan kiran sallar
Hujja a kan wannan Sunna kuma ita ce, Hadisin can na Abdullahi xan Amru raliyallahu anhuma, inda ya ce: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Idan kuka ji kiran salla, to, ku riqa maimaita duk abin Ladan ya faxi. Sa’annan ku yi salati gare ni. Domin duk wanda ya yi salati xaya a gare ni, Allah Maxaukakin Sarki zai yi masa salati goma. Bayan haka nan kuma, ku roqar mani Allah maxaukakin Sarki kusanci. Kusancin nan, wani matsayi ne a cikin Aljanna, wanda babu wanda yake samunsa sai wanda yake daga cikin bayin Allah. To, ina fatar ya kasance ni xin ne. Duk kuwa wanda ya roqar mani wannan matsayi, to, yana daga cikin waxanda zan ceta.” (Muslim:384).
Mafificin Salati kuma shi ne: ‘salatin Ibrahimiyyah.’ Wato, “Alláhumma salli alá Muhammadin, wa alá áli Muhammadin kama sallaita alá ibráhíma…..”
Karanta addu’ar da aka riwaito a bayan kiran sallar
Hujja a kan wannan Sunna kuwa, ita ce Hadisin Jabiru raliyallahu anhu, inda ya ce: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Duk wanda ya ji kiran salla, sa’nnan ya karanta: “Alláhumma Rabba házihid-da’awatit-támah, wa salátil-qá’imah, áti Muhammadanil-wasálata walfadhílata, wab’ashulláhu maqáman mahmúdanillazí wa’adtah. (Ya Ubangijina! Ubangijin waxannnan qasaitaccin kalmomi, da sallar da za a yi yanzu! Ka ba wa Muhammadu xaukaka da babban matsayin nan. Sa’annan ka tayar da shi a maxaukakin bagiren nan, na ko wane da wane, wanda ka yi masa alqawali.). Duk wanda ya faxi haka, in ji Annabi sallallahu alaihi wa sallam, zan cece shi ranar Alqiyama.” (Buhari:614).
Roqon Allah bayan kiran salla
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin can na Abdullahi xan Amru raliyallahu anhu, inda ya ce: “Wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah! Haqiqa Ladanai, sun dai fi mu matsayi. Sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya karva masa da cewa: “Ka faxi duk abin da Ladan ya faxa, sa’annan idan ka qare, ka roqi Allah, zai karva maka.” (Abu dawuda:524) Malam Ibnl-Hajar kuma ya ainganta shi a cikin: Natá’ijul-afkári:1/367), da kuma Albani a cikin: Sahihu kalimix-xayyib:73)
Wata hujjar kuma ita ce, Hadisin Anas raliyallahu anhu, inda ya ce: Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Duk addu’ar da aka yi tsakanin kiran salla da iqama, bat a faxuwa qasa banza.”(Nasa’i:9895) Ibn Khuzaimah kuma ya inganta shi:1/221/425).
Don Saduwa Da Mu
Da Mu
Muna Farin Ciki Da Samun Kiranka Da Tambayoyinka A Kowane Lokaci