brightness_1
Wanke Kowace Gava Sau Uku
Wanki na farko wajibi ne. Shi kuwa na biyu da na uku sunna ne. Ba kuma za a qara a kan wankin nan na uku ba.
Hujja a kan wannan Sunna:
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, tabatattar magana a wurin Imamul-Buhari rahimahullahu, daga cikin Hadisan xan Abbas raliyallahu anhuma cewa: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam kan yi arwalla ta hanyar wanke gavovin jikinsa shuxi xaya-xaya.” (Buhari:157). Wata maganar kuma da ta tabbata a wurin Imamul-Buhari xin, daga cikin Hadisan Abdullahi xan zaidu raliyallahu anhu, ita ce cewa: Annabi sallallahu alaihi wa sallam kuma a wani lokacin yakan yi arwallalr shuxi biyu-biyu.” (Buhari:158). Ya kuma tabbata a cikin ingantattun littafan Buhari da Muslimu daga cikin Hadisan Sayyadi Usmanu raliyallahu anhu cewa, Annabi sallallahu alaihi wa sallam, yakan kuma yi arwallar shuxi uku-uku.” (Buhari:159). Saboda haka abin ya fi shi ne yi kamar yadda ya yi sallallahu alaihi wa sallam, wato, xaya-xaya, ko biyu-biyu, ko uku-uku xin. Ko kuma wani lokacin ya ma sassava a cikin arwallal xaya. Wato, kamar ya wanke fuska sau uku, hannuwa kuma sau biyu, qafa kuma sau xaya, kamar yadda ya zo a cikin ingantattun littafan nan na Buhari da Muslimu xin daga cikin Hadisan abdullahi xan Zubairu raliyallahu anhu, a cikin wata riwayar. Don qarin bayani sai a duba littafin: Zadul-Mi’ad (1/192). Sai dai mafi cika da kamalar sifa ga arwalla, shi ne mutum ya yawaita yin wanki uku-uku. Wannan shi ne Sunnar Annabi sallallahu alaihi wa sallam.