Ana yin asawaki ne kafin a fara arwalla, ko kafina fara kurkurar baki. Yin shi kafin a fara kurkurar baki xin nan, shi ne wuri na biyu da Sunna ta tanadi yin asawaki. Wuri na farko mun riga mun yi bayani a kansa a baya kaxan. To, Sunna ne ga wanda zai yi arwalla ya yi aswaki. Dalili kuwa shi ne abin da ya zo a cikin Hadisin Abu Hurairata raliyallahu anhu cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Ba don kada in tsananta wa al’umata ba, da na umarce su da yin asawaki a duk lokacin da za su yi arwalla.” (Ahmad:9928/ Ibn Huzaimah:1/73/140, ya kuma inganta shi/ Hakim:245/ Buhari ta’aliqan a cikin siga ta yanke magana, cikin Babin halascin Yin asawaki da Xanye ko Busasshen Icce ga Mai azumi).
Hujja ta biyu kuma ita ce Hadisin Sayyida A’ishah raliyallahu anha, inda ta ce: “Mu kan tanadar wa Manzon Allah asawaki da ruwansa na arwalla. Duk lokacin da Allah Maxaukakin Sarki ya nufa ya tashi a cikin dare, sai ya yi asawaki ya yi arwalla, ya kuma yi salla…” (Muslimu:746).
Hujja a kan wannan Sunna ita ce: Hadisin Sayyadi Usmanu raliyallahu anhu, inda ya bayar da hoton yadda Annabi sallallahu alaihi wa sallam yake yin arwalla, a aikace. A ciki yake cewa: “Sai Annabi ya nemi a kwao masa rowan arwalla. Ana kawowa kuwa sai ya wanke tafunan hannuwansa shuxi uku…” Sai kuma mai riwayar ya qara da cewa: “Kun ga yadda nake yin arwallar nan, to, haka naga Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya yi waccan arwallal da nake ba ku labara.” (Buhari:164/ Muslimu:226).
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Sayyida A’asha raliyallahu anha, inda ta ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yana matuqar sha’awar fara al’amari da hannun dama. Musamman, saka takalmi, da jefa qafa, da tsarki. Kai! da ma gaba xayan a’murran rayuwarsa.” (Buhari:167/ Muslimu:268).
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, wancan Hadisin Sayyadi Usmanu raliyallahu anhu inda yake sifanta yadda Annabi sallallahu alaihi wa sallam yake arwalla. Ya ce: “Sai ya kurkure baki, ya kuma fyace. Sa’annan ya wanke fuskarsa sau uku.” (Buhari:199/ Muslimu:226). Amma tattare da haka idan mutum ya jinkirta kurkurar baki da shaqa ruwa har sai bayan ya wanke fusakarsa, babu komai.
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Luqaixu xan sabrata raliyallahu anhu, cewa Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce masa: “Duk lokacin da za ka yi arwalla, to, ka yi ta da kyau, ta hanyar tsattsefe yatsunka sosai, da kuma kaiwa matuqa a cikin shaqa ruwa, in ba azumi kake yi ba.” (Ahmad:17846/ Abu Dawuda:142). Malam Ibn Hajar ya ce: “Wannan Hadisi ne ingantacce.” Isábah: (9/15). Cewar da Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya yi a cikin wannan Hadisi: “Duk lokacin da za ka yi arwalla, to, ka yi ta da kyau.” A nan ne aka xauki hannu, aka kuma fahimci cewa akwia bukatar a tsananta a cikin ‘kurkurar baki’
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Zaidu raliyallahu anhu, inda yake sifanta yadda Annabi sallallahu alaihi wa sallam yake arwalla, ya ce: “…. sai Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya saka hannunsa a cikin ruwa ya xebo. Sa’annan ya kai a baki ya kurkure, ya kuma shaqa sauran, duk da hannu xaya. Haka ya yi ta yi har sau uku. (Buhari:192/ Muslimu235).
Yadda ake sahafar kai a Sunnar idan ana arwalla, shi ne, mutum ya fara xora hannuwansa a kan goshinsa. Sa’annan ya shafa su zuwa baya har ya kai ga qeyarsa. Sai kuma ya sake shafowa gaba har zuwa inda ya fara. Mace ma haka za ta yi; ba za ta qi aikata wannan Sunna ba. Sauran kuma gshin da yake shimfixe a wuyan mace, ba lalle ne sai ta shafe shi ba.
Hujja a Kan Wannan Sunna:
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin abdullahi xan Zaidu raliyallahu anhu, shi ma, inda yake bayar da sifar yadda Annabi sallallahu alaihi wa sallam yake arwalla, ya ambaci cewa: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya fara da shimfixa hannuwansa ne a kan goshinsa. Sa’annan ya shafa su zuwa qeyarsa. Sa’annan ya dawo da su zuwa wurin day a fara shafar.” (Buhari:185/ Muslim:235)
Wanki na farko wajibi ne. Shi kuwa na biyu da na uku sunna ne. Ba kuma za a qara a kan wankin nan na uku ba.
Hujja a kan wannan Sunna:
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, tabatattar magana a wurin Imamul-Buhari rahimahullahu, daga cikin Hadisan xan Abbas raliyallahu anhuma cewa: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam kan yi arwalla ta hanyar wanke gavovin jikinsa shuxi xaya-xaya.” (Buhari:157). Wata maganar kuma da ta tabbata a wurin Imamul-Buhari xin, daga cikin Hadisan Abdullahi xan zaidu raliyallahu anhu, ita ce cewa: Annabi sallallahu alaihi wa sallam kuma a wani lokacin yakan yi arwallalr shuxi biyu-biyu.” (Buhari:158). Ya kuma tabbata a cikin ingantattun littafan Buhari da Muslimu daga cikin Hadisan Sayyadi Usmanu raliyallahu anhu cewa, Annabi sallallahu alaihi wa sallam, yakan kuma yi arwallar shuxi uku-uku.” (Buhari:159). Saboda haka abin ya fi shi ne yi kamar yadda ya yi sallallahu alaihi wa sallam, wato, xaya-xaya, ko biyu-biyu, ko uku-uku xin. Ko kuma wani lokacin ya ma sassava a cikin arwallal xaya. Wato, kamar ya wanke fuska sau uku, hannuwa kuma sau biyu, qafa kuma sau xaya, kamar yadda ya zo a cikin ingantattun littafan nan na Buhari da Muslimu xin daga cikin Hadisan abdullahi xan Zubairu raliyallahu anhu, a cikin wata riwayar. Don qarin bayani sai a duba littafin: Zadul-Mi’ad (1/192). Sai dai mafi cika da kamalar sifa ga arwalla, shi ne mutum ya yawaita yin wanki uku-uku. Wannan shi ne Sunnar Annabi sallallahu alaihi wa sallam.
Hujja a kan wannan Sunna ita ce abin da aka samo daga Sayyadi Umar raliyallahu anhu, ya ce: Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Babu wani daga cikinku da zai yi arwalla kamar yadda ya kamata. Sa’annan ya karanta: “Ash-hadu an lá’iláha illalláhu, wa anna Muhammadan Abduhú wa Rasúluhú,” (Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa.) Ba zai faxi haka ba, face an buxe masa qofofin Aljanna guda takwas hayan-hayan, ya shiga ta duk wadda ya ga dama daga cikinsu.” (Muslimu:234)
Ko kuma abin da ya zo a cikin Hadisin Abi Sa’id raliyallahu anhu-marf”u’an: “Duk wanda ya yi arwallal, ya kuma qare arwalarsa, sa’annan ya karanta: “Subhánakal-láhumma wa bihamdika. Ash-hadu allá iláha illá anta. Astagfiruka wa a túbu ilaika,” (Tsarki ya tabbata gare ka ya Ubangijina! Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai kai. ina neman gafararka, ina kuma tuba gare ka) [face Allah Maxaukakin Sarki ya buga masa hatiminsa mai alfarma] sa’annan a aika da ita zuwa qarqashin al’arshi; ba tare da ta samu wani tasgaro ba har zuwa ranar Alqiyama.” (Nisa’a:147- a cikin Babin Ayyukan Yini da Dare/ Hakim:752- Malam Ibn Hajar rahimahullahu kuma ya kyautata danganensa. Domin qarin bayani sai a duba littafin Natá\ijul-afk”ar: 1/246) Sai dai Malamin ya bayyana cewa, idan cewar da aka yi Hadisin ‘marfú’i’ ne, hakan bat a inganta ba, to, ya zama ‘mauqúfí’ kenan. Sai dai hakan ba zai rage shi da komai ba, saboda hukuncinsu xaya da ‘marfú’i’ xin saboda Hadisi ne shi da babu dammar cece-ku-ce a kansa.