languageIcon
(Hausa) هَوُسَ
(Hausa) هَوُسَ
አማርኛ
العربية
Azeri
বাংলা
Bosanski
Deutsch
English
Español
Filipino
فارسي
Français
हिन्दी
Indonesia
italiano
Қазақ тілі
தமிழ்
كوردی
नेपाली
Português
Pусский
සිංහල‎
Gjuha shqipe
Kiswahili
ภาษาไทย
Türkçe
Українська
اردو
Yorùbá
中文
search
search
Taka wa hamma burki ko rufe ta da hannu Sunna ne

Hujja a kan wannan Sunna:

Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abu Hurairah raliyallahu anhu, daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam, ya ce: “Haqiqa, Allah yana son attishaya, yana kuma qyamar hamma. Idan xayanku ya yi attishaya, ya kuma gode wa. To, wajibi ne a kan duk musulmin da ya ji shi, ya yi masa barka da arziki. Amma hamma, aba ce da take zuwa daga Shaixan. Saboda haka, musulmi ya yi qoqarin taka mata burki gwargwadon halinsa. Idan kuwa ya yi ta, to, ya sani Shaixan zai yi masa dariya.”  (Buhari:2663).

A wata riwaya kuma ta Muslimu, daga cikin Hadisan Abu Sa’id raliyallahu anhu, cewa Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya yi: “Idan xayanku ya yi hamma, to, ya xora hannunsa a kan bakinsa, don kada Shaixan ya shiga.” (Muslim:2995). Kenan Sunna tana son a taka wa hamma burki ne, ta yadda za a yi ta ba tare da an wangali baki sagaga ba. Ko dai a kantse lavvan baki, da hauru, ta yadda hammar za ta fita ba tar da an gane ba, ko a sa hannu a rufe bakin, ko dai wasu dabaru masu kama da waxannan.
 

 
Simple Audio Player
 
facebook googleplus twitter