Sunna tana so ne wanda yake salla, ya yi irin wannan zama bayan ya kamala raka’arsa ta biyu; ruku’u, da sujada, da tsuwa, da zamanta sun kamala. Daxa kuwa, sallar mai raka’a huxu ce, ko uku, ko biyu. Sharaxin dai shi ne, a cikin kowace raka’a ta biyu, wadda zaman “tahiyáh” ke biyowa bayanta. To, irin wannan zama ake so mai salla ya yi. Hujja a kan wannan Sunna kuwa ita ce, Hadisin Abu Humaidin Assá’idí raliyallahu anhu- marfú’an, wanda a cikinsa yake cewa: “Idan Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya zauna tsakanin sujada da sujada, yakan shimfixa qafarsa ta hagu ne, ya xora ta dama a kanta ya zauna.” (Buhari:828), da kuma Hadisin Sayyidah A’sha raliyallahu anha, inda take cewa: “Kuma Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance, yakan yi “tahiyáh” bayan kowaxanne raka’o’i biyu, ta hanyar shimfixa qafarsa ta dama tare da tokara ta hagu.” (Muslimu:498).
Dangane kuma da abin da ya shafi “tahiyáh” ta qarshe, wadda akan yi a cikin salla mai raka’a huxu ko uku, nan gaba kaxan za mu zo da bayanin Sunnonin da suke qunshe a cikinsu.
Xora tafukan hannuwa a kan cinai a lokacin da ake yin “tahiyáh” yana da yanaye-yanaye guda biyu. Ana kuma so ne, mai sallal ya riqa yi yana kaiwa da komowa a tsakanin waxannan sifofi guda biyu, da suka haxa da:
Sifa ta xaya: Xora hannuwa a kan cinai.
Sifa ta biyu: Xora hannuwa a kan guwai. Yadda kuma zai yi shi ne, ya saka hannunsa na haxu ya jimqe guiwar qafarsa da hagu da shi. Shi kuwa hannun dama, sai ya tayar da manuninsa, wato, kashedinsa. Nan gaba kaxan za mu kawo cikakken bayani a kan wannan Sunna ta tayar da manuni. Amma, shi hannun hagu yana nan koda wane lokaci shimfixe a kan guiwar qafar hagu.
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin xan Umar raliyallahu anhuma wanda ya ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance, idan ya zauna a cikin salla, yakan xora hannunsa na dama a kan cinyarsa ta dama tare da rumqe gaba xayan yatsunsa, ban da manuni; yatsan da yake kusa ga babban taysa. Shi kam yakan tayar da shi tsaye yana kallon alqibla. A yayin da shi kuwa hannun hagu yake xora shi a kan cinyar hagu.” (Muslimu:580). A cikin wata riwaya kuma ya ce: “Yana damqe guiwar qafarsa ta hagu da tafin hannunsa na hagu.” (579).
A Sunna, an fi so mutum ya riqa yi yana caccanza yanayin yadda yake xora yatsunsa a kan guwai a lokacin da yake yin “tahiyáh” tsakanin sifofi guda biyu, da aka riwaito a Sunna.
Sifa ta xaya: A wannan sifa mutum zai rumqe gaba xayan yatsun nasa ne, na hannun dama. Sa’annan ya tayar da manuni tsaye yana kallon alqibla. Shi kuwa hannun dama da yatsunsa, suna can shimfixe a kan guiwar qafarsa ta hagu.
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin xan Umar raliyallahu anhuma, wanda ya gabata, cewa: “… Annabi sallallahu alaihi wa sallam yana ruqe gaba xayan yatsun hannunsa na dama ne, sa’annan ya tayar da manuninsa, yatsan da yake kusa da babban yatsa, sama yana kallon alqibla…” (Muslimu:580).
Sifa ta biyu: A wannan sifa kuma. Mutum zai qulla hoton wani abu ne mai kama da hamsin da uku a lissafi, ta hanyar rumqe qaramin yatsansa da wanda yake bi masa. Sa’annan ya riqa mommotsa babban yatsa tare da na tsakiya. A yayin das hi kuwa manuni, zai tayar das hi tsaye yana kallon alqibla. Shi kuwa hannun hagu yana can shimfixe a kan guiwar hagu.
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin can na xan Umar raliyallahu anhu wanda ya gabata, wanda a cikinsa yake cewa: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance, idan ya zauna zai yi “tahiyáh” yakan xora hannunsa na hagu a kan qafarsa ta hagu. Hannunsa na dama kuma, sai ya xora shi a kan qafarsa ta dama. Sa’annan ya qulla hoton talatin da biyar ta lissafi. Manuninsa kuma, sai ya tayar da shi sama yana kallon alqibla.” (Muslimu:850).
Sunna ce ga mutum ya riqa caccanza sigogin “tahiyáh” waxanda aka riwaito a Sunna; isan ya yi wannan yau, gobe kuma ya yi waccan. Daga cikin waxannan sigogi akwai:
a) “Attahiyyátu lilláhi, was- salawátu, wax- xayyibátu, assalámu alaika ayyuhan- Nabiyyu wa rahamatulláhi wa barakátuhu. Assalámu alainá wa alá ibádilláhis- sálihína. Ash- hadu allá’iláha illalláhu, wa ash- hadu anna Muhammadan Abduhú wa Rasuluhú.” (Tsarkakan kalmomin gaisuwa, da salati, sun tabbata ga Allah. Aminci kuma, da rahamar Allah da albarkarsa, su tabbata gare ka ya kai wannan Annabi. Muma aminci ya tabbata a gare mu, da kuma ga sauran bayin Allah na qwarai. Ana shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Ina kuma shaida cewa, lalle Muhammadu Bawansa ne kuma Manzonsa ). [Buhari:1202/ Muslimu:402], daga cikin Hadisan xan Mas’ud raliyallahu anhu.
b) a) “Attahiyyátul- mubárakátu, was- salawátux- xayyibátu lilláhi. Assalámu alaika ayyuhan- Nabiyyu…” (Tsarkakkakn kalmomin gaisuwa masu albarka, da salati, sun tabbata ga Allah. Aminci kuma ya tabbata gare ka ya kai wannan Annabi….). Sai kuma a cika har qarshe kamar yadda yake a sama. [Muslimu:403] daga cikin Hadisan xan Abbas raliyallahu anhuma
c) a) “Attahiyyátux- xayyibátus- saláwátu lilláhi. Aassalámu alaika ayyuhan- Nabiyyu….” (Tsarkakan kalmomin gaisuwa da salati, sun tabbata ga Allah. Aminci kuma, ya tabbata gare ka ya kai wannan Annabi…) Sai kuma a cika har qarshe kamar yadda yake a can farko. (Muslimu404), daga cikin Hadisan Abu Musa raliyallahu anhu.
Abin da Sunna ta tanada idan mutum zai zauna domin yin “tahiyáh” ta qarshe, shi ne, ya zauna dangalgal a kan qasa, idan sallar mai raka’a huxu ce ko uku. Wato, ya zauna a kan xuwainiyarsa ta hagu. Irin wannan zama kuwa, na ‘dangalgal’ yana da siga fiye da xaya. Saboda da haka, ana so mai salla ya yi qoqarin riqa caccanzawa yau da gobe.
Daga cikin waxannan sigogi akwai:
a) Shimfixa qafar hagu tare da fitar da ita vangaren dama. Sa’annan a tokara ta hagu ga qasa:
Hujja a kan wannan siga ita ce, abin da Buhari rahimahullahu ya riwaito daga Abu Humaidin As- Sa’idí raliyallahu anhu: (Buhari:828).
b) Simfixa dukan qafafu tare da fitar da su a vagaren dama. Sa’annan a tokara su ga qasa.
Hujja a kan wannan siga kuma ita ce, abin da Abu Hurairah raliyallahu anhu ya riwaito (231), da Ibn Hibbán (1867), da Baihaqí (2/128), daga cikin Hadisan Abu Humaidin As- sa’idi raliyallahu anhu, wanda kuma Albani ya inganta, rahimallahul jamí’i.
Sai dai yana da kyau a sani cewa, irin wannan zama na dangaldal, ba a cikin kowane zaman tahiya na qarshe, Sunna ta ce ayi shi ba. Ana yinsa ne a cikin zaman tahiya na qarshe a cikin salla mai raka’a uku, ko huxu, amma, ban da mai raka’a biyu.
Sunna ce mutum ya riqa yi yana kaiwa da komwa a tsakanin sigogin salati ga Annabi sallallahu alaihi wa salla, da aka riwaito; idan ya yi wannan yau, gobe ya yi wancan. Daga cikin waxannan sigogi akwai:
a) Alláhumma salli alá Muhammadin, wa alá áli Muhammadin, kamá sallaita alá Ibrahíma, wa alá áli Ibráhima innaka hamídun Majídun. Alláhumma bárik alá áli Muhammadin, kamá bárakta alá Ibráhíma. Innaka Hamídun Majid. (Ya Ubangiji! Ka daxa tsira ga Annabi Muhammadu, da alayen Annabi Muhammadu, kamar yadda ka yi tsira ga Annabi Ibrahima da alayen Annabi Ibrahima. Lalle kai abin godiya ne, abin kuma giramamawa. Ya Ubangiji! Ka daxa aminci ga Annabi Muhammadu, da alayen Annabi Muhammadu, kamar yadda ka daxa aminci ga Annabi Ibrahima da alayen Annabi Ibrahima. Lalle kai abin godiya ne, abin kuma giramamawa.) [Buhari:3370] daga cikin Hadisan Ka’abu xan Ujrah raliyallahu anhu.
b) Alláhumma salli alá Muhammadin, wa alá áli Muhammadin, kamá sallaita alá áli Ibráhima. Wa bárik alá Muhammadin wa alá áli Muhammadin, kamá bárakta alá áli Ibráhíma, fil álamína Innaka Hamídun Majid. (Ya Ubangiji! Ka daxa tsira ga Annabi Muhammadu, da alayen Annabi Muhammadu, kamar yadda ka yi tsira ga alayen Annabi Ibrahima. Ka kuma yi albarka ga Annabi Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka ga alayen Annabi Ibrahima, a cikin talikai. Lalle kai abin godiya ne, abin kuma giramamawa.) [Muslimu:305] daga cikin Hadisan Abu Ms’ud Al- Ansárí raliyallahu anhu.
a) Alláhumma salli alá Muhammadin, wa alá azwájihí wa zurriyátihí, kamá sallaita alá áli Ibrahíma, wa bárik alá áli Muhammadin, wa alá azwájihí wa zurriyátihí, kamá bárakta alá áli Ibráhíma. Innaka Hamídun Majid. (Ya Ubangiji! Ka daxa tsira ga Annabi Muhammadu, da matansa da zuri’arsa, kamar yadda ka yi tsira ga alayen Annabi Ibrahima. Ka kuma yi albarka ga Annabi Muhammadu, da matansa da zuri’arsa kamar yadda ka yi albarka ga alayen Annabi Ibrahima. Lalle kai abin godiya ne, abin kuma giramamawa.) [Buhari:3369/ Muslimu:407] daga cikin Hadisan Abu Humaidin As- Sá’idí raliyallahu anhu.
Sunna ta bukaci mai salla, kafin ya sallame, ya nemi tsarin Allah Maxaukakin Sarki daga sharrin abubuwa guda huxu. Bakin gaba xayan mafi yawan Malamai rahimahumullahu ya haxu a kan haka. Hujja a kan wannan Sunna kuwa ita ce, Hadisin Abu Hurairah raliyallahu anhu cewa, Annabi sallallahu alaihi wa salla ya ce: “Duk lokacin da xayanku ya qare karatun tahiyáh ta qarshe. To, ya nemi tsarin Allah daga sharrin abubuwa guda huxu; azabar qabari, da azabar Jahannama, da miyagun qaddarorin rayuwa, da na mutuwa, da kuma sharrin Dujjal, korarrae daga rahamar Allah.” (Muslimu:588/ Buhari832).
Akwai kuma waxansu addu’o’in na daban da suka Sunna ta zo da su, waxanda ba waxannan ba, da take kuma da bukatar mai salla ya riqa caccanza hannu a tsakaninsu, kafin ya sallame sallarsa. Daga cikinsu akwai:
1/ “Alláhumma inní a’uzu bika minal- ma’asami wal- magrami.” (Ya Ubangiji! Ina roqon tsarika daga ayyukan savo da na zunubi.) (Buhari:832/ Muslimu:589)..
2/ “Alláhumma inní as’alukal- Jannata wa aúzu bika minan- Nári.” (Ya Ubangiji! Ina roqon ka sadakar Aljanna, ina kuma neman tsarinka daga Wuta.) [Abu Dawuda:792] Albani kuma ya inganta danganensa: (Sahíhu Abi Dawuda:3/377).
3/ “Alláhumma inná zalamtu nafsí zulman kasíran, wa lá iagfiruz- zuna illá anta. Fagfir lí magfiratan min indika, war- hamná, innaka antal- Gafúrur- Rahím.” (Ya Ubangiji! Na zalunci kaina, zalunci mai yawa, babu kuma mai gafarar zunubai sai kai. Ka gafarta mani, gafara ta musamman daga wajjenka, ka kuma yi mani rahama. lalle kai, mai yawan gafara ne, mai kuma yawan jinqayi.) [Buhari:6326/ Muslimu:2705].
4/ “Alláhumma a’inní alá zikrika, wa shukrika, wa husni ibádatika.” (Ya Ubangiji! Ka taimake ni in riqa ambatonka, in riqa kuma godiya a gare ka, sa’annan in rika kyautata bautarka.) [Ahmad:22119/ Abu Dawuda:522/ Nasa’i:1304[, Albani kuma ya ainganta shi: (Sahíhul- Jámi’i:2/1320).
5/ “Alláhumma inní a’úzu bika minal- bukhuli, wa a’úzu bika minal- jubuni, wa a’úzu bika an uradda ilá arzalil- umri, wa a’úzu bika min fitnatid- duniya, wa a’úzu bika min azábil qabri.” (Ya Ubangiji! Ina neman tsarinka daga sharrin rowa, ina kuma neman tsarinka daga zama matsoraci, ina kuma neman tsarinka daga a mayar da ni zuwa mafi qasqancin shekaru, ina kuma neman tsarinka daga fitinonin xakin duniya, ina kuma neman tsarinka daga azabar qabari.) [Buhari:6370].
6/ “Alláhumma hásibní hisában yasírá.” (Ya Ubangiji! Ina roqon ka yi mani hisabi mai sauqi.) [Ahmad:24215] Albani kuma ya inganta shi a cikin: ‘Tahqiqu mishkátul- Masábíh:3/1544
Daga nan daxa, sai mutum ya sallame sallarsa ta hanyar yuja kansa. juya kai domin sallama Sunna ne. haka nan kaiwa matuqa a cikin juyawa xin, shi ma Sunna ne. dalili kuwa shi ne, irin yadda ta tabbata cewa, Annabi sallallahu alaihi wa sallam yakan juya kansa sosai domin sallam har sai an hango kaye-kayin kundukukinsa daga bayansa, sallallahu alaihi wa sallam. Hujja a kan wannan Sunna kuwa ita ce, Hadisin da aka riwaito daga Sa’ad xan Abi Waqqas raliyallahu anhu, inda ya ce: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yana juya kansa dama da hagu domin yin sallama, har in hangi katekayin kundukukinsa.” (Muslimu:582).