languageIcon
(Hausa) هَوُسَ
(Hausa) هَوُسَ
አማርኛ
العربية
Azeri
বাংলা
Bosanski
Deutsch
English
Español
Filipino
فارسي
Français
हिन्दी
Indonesia
italiano
Қазақ тілі
தமிழ்
كوردی
नेपाली
Português
Pусский
සිංහල‎
Gjuha shqipe
Kiswahili
ภาษาไทย
Türkçe
Українська
اردو
Yorùbá
中文
search
search
sonnaImg
Xora tafukan hannuwa a kan cinai

Xora tafukan hannuwa a kan cinai a lokacin da ake yin “tahiyáh”  yana da yanaye-yanaye guda biyu. Ana kuma so ne, mai sallal ya riqa yi yana kaiwa da komowa a tsakanin waxannan sifofi guda biyu, da suka haxa da:

Sifa ta xaya: Xora hannuwa a kan cinai.

Sifa ta biyu: Xora hannuwa a kan guwai. Yadda kuma zai yi shi ne, ya saka hannunsa na haxu ya jimqe guiwar qafarsa da hagu da shi. Shi kuwa hannun dama, sai ya tayar da manuninsa, wato, kashedinsa. Nan gaba kaxan za mu kawo cikakken bayani a kan wannan Sunna ta tayar da manuni. Amma, shi hannun hagu yana nan koda wane lokaci shimfixe a kan guiwar qafar hagu.

Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin xan Umar raliyallahu anhuma wanda ya ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance, idan ya zauna a cikin salla, yakan xora hannunsa na dama a kan cinyarsa ta dama tare da rumqe gaba xayan yatsunsa, ban da manuni; yatsan da yake kusa ga babban taysa. Shi kam yakan tayar da shi tsaye yana kallon alqibla. A yayin da shi kuwa hannun hagu yake xora shi a kan cinyar hagu.” (Muslimu:580). A cikin wata riwaya kuma ya ce: “Yana damqe guiwar qafarsa ta hagu da tafin hannunsa na hagu.” (579).

 

 
Simple Audio Player
 
facebook googleplus twitter