languageIcon
search
search
brightness_1 Maimaita addu’ah da nacewa

Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin xan Abbas raliyallahu anhu wanda ya gaba, inda ya ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Ya Ubangiji! Ka cika mani alqawalin da ka yi mani. Ya Ubangiji! Ka kawo mani agajin da ka yi mani alqawali,”  Haka ya ci gaba da aika wannan saqo zuwa ga Ubangijinsa, har mayafinsa ya baro kafaxunsa ya sauka qasa ya. Sai Sayyadi Abubakar raliyallahu anhu ya zo ya xauke mayafin ya nayar masa da shi a kan kafaxa, ya kuma ci gaba ada kasancewa a bayansa sallallahu alaihi wa sallam yana cewa masa: “ya Annabin Allah! ya isa haka nan; saqonka ya isa zuwa ga Ubangijin naka. Ko shakka babu, zai cika maka duk alqawulan da ya yi maka a wanan rana….” (Muslim:1763).

Wata hujjar kuma ita abin da ya zo a cikin ingantattun littafan Hadisai guda biyu, daga cikin hadisan Abu Hurairah raliyallahu anhu, a lokacin da Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya tashi yi   wa Dausu addu’a, sai ya ce: “Ya Ubangiji! Ka shiryar da Dausu, ka kuma kawo mana su. “Ya Ubangiji! Ka shiryar da Dausu, ka kuma kawo mana su.”  (Buhari:2937/ Muslimu:2524).

wata hujjar kuma ita ce, abin day a zo a cikin ingantaccen littafin Imamu Muslimu, a kan: “Mutumin nan da ya yo doguwar tafiya, har gashin kansa ya yi qutuu-qutut da qura, ya kuma shiga xaga hannuwansa sama, yana kiran ya Ubangiji! Ya Ubangiji!!) (Buhari:1015). Irin wannan maimaitawa xauke take da naciya da nuna tsananin bukata.

Abin da Sunna ta yi tanaadi a wannan babi shi ne, idan mutum zai roqi Allah Maxaukakin Sarki, to, ya maimaita kalmomin roqon har sau uku. Hujja kuwa ita ce, Hadisin xan Mas’udu raliyallahu anhu wanda yake cikin ingantattun littafan Hadisai guda biyu, da aka ce: “Haka nan kuma duk lokacin da Annabi sallallahu alaihi zai yi addu’a, yakan maimaita har sau uku, sa’annan ya ce: “Ya Ubangiji! Ina kai qarar Quraishawa a wurinka.” Shi ma wannan lafazin yakan maimaita shi har sau uku.” (Buhari:240/ Muslimu:1794).

 

brightness_1 Qarin Haske

Tana yiwuwa wani ya yi tambaya a cikin ransa cewa:  me ya kamata in faxa idan zan roqi Allah? Amsa a kan haka ita ce: Abin day a kamata muslmi ya roqi Allah Maxaukakin Sarki shi ne, alhairan duniya da na Lahira. Sa’annan kuma Sunna tana son a riqa mayar da hankali ga dunqulallun kalmomi; ba sai an tsay yi wa Allah subhanahu wa ta’alah, kwatta-kwatta ba. Yin addu’a ta hanyar amfani da kalmomin dunqulalli kuma kammalalli, wanda ya haxa da roqon alhairan duniya da Lahira, shi ne abin da Alqur’ani da Sunna suka zo da shi. An tava yi wa Annabi sallallahu alaihi wa sallam irin wannan tambayar. Sai ya karva da cewa, a kula da amfani da manya-manyan kalmomi, game-gari; irin waxanda ke kawo wa muslmi alhairin duniya da na Lahira. Kai ka san babu busharar da ta kai wanna girma da yawan kawo kyakkyawan sakamako a matsayinta na mafi girman kyauta. Saboda haka yana da kyau musulmi su kula, su kuma riqa ta da hannu biyu-biyu.

An samo daga Abi Malik Al’ashja’í raliyallahu anhuma, cewa: “Ya ji Annabi sallallahu alaihi wa sallam wata rana, da wani mutum ya zo wurinsa, ya ce masa: “Ya Manzon Allah me ya kamata in faxa idan zan roqi Allah Ubangijina?” Sai ya karva masa da cewa: “Ka ce: Alláhummg- fir lí, warhamní, wa áfiní, warzuqní.” (Ya Ubangiji! Ka gafarta mani, ka yi mahi rahama, ka ba ni lafiya, ka kuma arzuta ni.)  Yana yi yana harhaxe ‘yan yatsunsa a jikin banbansu. Ya kyma qara da gaya masa cewa: “Ka ga waxannan kalmomi, babu abin dab a za su lamunce maka ba, na duniya da Lahirarka.” (Muslimu:2697).

A cikin wata riwaya kuma ta shi Muslimu xin, ya ce: “Duk lokacin da wani mutum ya karvi Musulunci,sai Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya koya masa yadda ake salla. Sa’annan ya umarce da ya riqa roqon Allah Maxaukakin Sarki da waxannan kalmomi: “Alláhummg- fir lí, warhamní, wahdiní, wa áfiní, warzuqní.” (Ya Ubangiji! Ka gafarta mani, ka yi mahi rahama, ka shiryar da ni, ka ba ni lafiya, ka kuma arzuta ni.)  [Muslimu:2697]