languageIcon
search
search
brightness_1 Yin sallama

Hujjojin da suke tabbatar da wannan Sunna ba su da iyaka. Daga cikinsu akwai: Hadisin Abu Huraira raliyallahu anhu, cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Haqqin kowane muslmi a kan xan’uwansa muslmi, shida ne.” Sahabbai suka ce: Waxanne haqqoqa ne waxannan ya Manzon Allah? sai ya karva musu da cewa: “Idan ka haxu da shi, ka yi masa sallama. Idan ya gayyace ka wata harka, ka tafi. Idan ya nemi wata nasiha daga gare ka, ka yi masa. Idan ya yi attishawa, ya kuma gode wa Allah, to, ka gai da shi. Idan ya yi rahsin lafiya, ka tafi duba shi. Idan kuma ya rasu ka rakki gawarsa maqabarta.”  (Muslimu:2162).

Sai dai a kula, wajibi ne ga mutum idan aka gayar da shi, bayan ya yi attishaya, ya kuma gode wa Allah. wajibi ne ya karva wannan gaisuwa. Hujja kuma a kan wannan wajabci ita ce:

Faxar Allah Maxaukakin Sarki: “Kuma idan aka gayar da ku da wata gaisuwa. To, ku karva da mafi kyawonta, ko ku mayar da irinta. Lalle Allah, ya kasance a  akn komai, mai qididdigewa ne.”

Zaman karvawar nan wajibi, shi ne hukunci na asali, matuqar wani dalili bai gitta ba, wanda zai canza wa hukuncin matsayi. An kuma samo da yawa daga cikin manyan Malamai, waxanda suka tafi a kan wajabcin karvawa xin. Daga cikinsu akwai: Ibn Hazmi, da Ibn abdil- Barr, da Shaikhu Taqiyyud- Din, rahimahumullahu jamí’an, da sauransu da dama. Don qarin bayani ana iya duba: “Al-ádábush- Shariyyah: 1/356” xab’in Mu’assasatur- Risálah.  

Mafi icika da kamalar lafazin sallama da mayar da ita, shi ne: Assalámu alaikun wa rahamatulláhi wa barakátuhú”  Ko shakka babu wannan gaisuwa it ace mafi kyau da kammala.

Malam Ibnl- Qayyim rahimahullahu  ya ce: “Karantarwar Annabi sallallahu alaihi wa sallam a cikin sha’anin gaisuwa, shi ne cika lafuzzan sallama tun daga farkonsu har qarshe. Wato, zuwa: “wa barakátuhú.”  Domin qarin bayani ana iya duba: Zádul- mi’ádi:2/417”

Haka shi ma “yawaita sallama” Sunna ne. kai wuce nan ma, abu ne da Shari’a ta kwaxaitar da a yi, tare da bayyana irin ximbin falalar da take tattare da hakan. Hujja a kan haka kuwa ita ce: Hadisin Abu Huraira raliyallahu anhu, da ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Ina rantsuwa da wanda rayuwata take hannunsa, ba za ku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani. Ba kuma za ku yi imani har sai kun kasance masu so da qaunar junanku. To, me zai hana ku saurara in gaya muku abin da idan kuka tsare aikata shi, soyayya da qaunar za su dauwama a tsakaninku?! Ku yi ta yawaita sallama a tsakaninku.”  (Muslimu:54)

brightness_1 Yin sallama idan za a shiga gida Sunna ne

Yin sallama idan za a shiga gida, wani babban rukuni ne na raya Sunnar sallama. Sai dai ana yin ta ne bayan an yi asawaki. Saboda yin asawaki idan za a shiga gida, Sunna ce tabbatatta, a matsayin gida wuri na huxu, inda Sunnar asawaki take da matuqar xarfi da nauyi, wato lokacin da mutum zai jefa qafarsa a cikin gida. Hujja a kan wannan Sunnan kuwa ita ce, Hadisin Sayyida A’isha ralyallahu anha, wanda yake a wurin Muslimu, inda ta ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance, duk lokacin da zai shiga gida, yakan fara da yin asawaki.” (Muslimu:253). Idan ya yaye kallabin shiga gidansa da asawaki, sallallahu alaihi wa sallam, sai kawai ya shiga tare da yi wa iyalinsa na wannan gida sallama. Bisa wannan dalili ne wasu Malamai suka dogara, suka yanke hukuncin cewa, Sunna ce mutum ya yi sallama idan zai shiga gida. koma wane irin gida ne; ko wanda babu kowa a cikinsa ne. Suka qarfafa wannan hukunci da faxar Allah Maxaukakin Sarki: “Kuma idan za ku shiga gidaje, to, ku yi wa kanku sallama; gaisuwa mai albarka mai tsarki, daga wurin Allah. kamar haka ne Allah yake bayyana ayoyi gare ku, tsammanin ku, za ku hankalta.” {Nur:61}  

Malam Ibnl- Hajar rahimahullahu ya ce: “Bakandamen umarni da Sunna ta yi da yawaita sallama, ya haxa har da yi wa kai ita ga wanda zai shiga wurin da babu kowa a cikinsa. Hujja kuwa ita ce: faxar Allah Maxaukakin Sarki: “Kuma idan za ku shiga gidaje, to, ku yi wa kanku sallama…”  Don qarin bayani ana iya duba: “Fathul- Bárí Hadisi mai lamba:6235: Babin Yawaita Sallama.”

.Darussa:  Abin da ya gabata yana karantar da cewa akwai Sunnoni uku a kan wanda zai shiga gida:  

Sunna ta farko: Ambaton Sunan Allah Maxaukakin Sarki, musamman idan da dare ne.

Hujja a kan wannan Sunna, ita ce: Hadisin Jabiru xan Abdullahi raliyallahu anhuma, cewa, ya ji Annabi sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Idan mutum zai shiga gidansa, ya ambaci Allah a lokacin shigar da lokacin da zai fara cin abinci. Sai Shaixan ya ce: Ya ku jama’ata! Ku sani yau kam, ba mu da wurin kwana ko abinci a cikin wannan gida. Idan kuwa ya shiga ba tare da ya ambaci suna Allah ba. Sai Shaixan ya ce: Ya ku jama’ata! Ku sani yau kam, mun sami wurin kwana a cikin wannan gida. Idan kuma bai ambaci Sunan Allah ba a lokacin da zai fara cin abinci. Shaixan ya ce: Ya ku jama’ata! Yau kam,  mun sami wurin kwana da abinci a cikin wannan gida.”  (Muslimu:2018).

Sunna ta biyu: Yin asawaki. Hujja a kan wannan Sunna kuwa ita ce: Hadisin Sayyida A’isha raliyallahu anha, wanda bayanin matani da isnadinsa suka gabata a baya kaxan.

Sunna ta uku: Yin sallama ga waxanda suke cikin gidan: