languageIcon
search
search
brightness_1 Farawa da Bisimillah

Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin da aka samo daga Umar xan Abu Salma raliyallahu anhu, wanda ya ce: “A matsayina na yaro qarami wanda yake dagwainiya a xakin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. wata rana ana cin abinci, hannuna yana kaiwa da komowa a cikin akushi. Sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, ya ce mani: “Ya kai wannan xan qaramin yaro! Ka ambaci sunan Allah, sa’annan ka ci da hannunka na dama, ka kuma ci abin da yake a gabanka.”  (Buhari:5376/ Muslimu:2022).

Idan kuma mutum ya manta bai yi bisimillah ba a farkon cin abincinsa. To, ya samu a Sunnance, idan ya tuna, ya ce: “Bismilláhi awaluhú wa ákhiruhú.” (Da sunan Allah na qare, da shi kuma na fara).

Hujja a kan wannan kuwa ita ce, Hadisin Sayyida A’isha raliyallahu anha, cewa, tabbas! Manzon Allah sallallahu alaihiwa sallam ya ce: “Idan xayanku zai ci abinci, to, ya ambaci sunan Allah. Idan kuma ya manta bai ce bismilláhi ba a lokacin da zai fara cin abincin. To, a qarshe yana iya cewa: “Bismilláhi awaluhú wa ákhiruhú. (Da sunan Allah na qare, da shi kuma na fara). [Abu Dawuda:3767/ Tirmizi:1858]. Albani kuma ya inganta shi kamar yadda bayani ya gabata.

Wani abu kuma da wannan Hadisi yake karantarwa shi ne, bukatar da take akwai ta musukmi ya riqa cin abinci da hannun dama, don kada ya yi kama da Shaixan. Duk lokacin da musulmi ya qi ambaton sunan Allah Maxaukakin Sarki a lokacin da zai fara cin abinci. To, ya sani hannunsa fa hannun Shaixan a cikin wannan akushi; tare za su ci su kuma canye. Haka nan kuma idan ya ci da hannun hagu. To, dashi da Shaixan babu wani banbanci, saboda Shaixan shi yake cin abinci, yake kuma shan abin shad a hannun hagu. 

Hujja a kan wannan Sunna:

Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin abdullahi xan Umar raliyallahu anhu, cewa, ta tabbata Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Kada wanda ya kusura ya ci abinci da hannun hagu daga cikinku; kada kuma ya sha abin sha da shi. Ba don komai ba kuwa, sai don saboda Shaixan shi ne yake ci da shad a hannun hagu.”  Mai riwaya ya ce, Nafi’u yakan qara a cikin wannan riwaya da cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya qara da cewa: “Kada kuma mutum ya karva, ko ya bayar da wani abu da hannun hagu.”  (Muslimu:2020).

Wannan umarni na Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam kuwa, ya biyo bayan masaniyar da yake da ita a kan xabi’ar Shaixan, ta son kutsa kai a cikin gidajen mutane, domin yakwana a ciki, ya kuma ci abinci, ya sha abin sha, tare da masu gidajen. Hujja a kan hakan kuwa ita ce, abin da aka riwaito daga Jabiru raliyallahu anhuma, cewa, ko shakka babu, ya ji Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Idan xayanku ya shiga gidansa, ya kuma ambaci sunan Allah a lokacin da zai shiga xin, da kuma lokacin da zai fara cin abinci. Sai Shaixan ya ce: Tir! yau kam ba mu dace ba; ba mu da wurin kwana ba mu kuma da abincin dare. Ida mutum bai ambaci sunan Allah a lokacin da zai shiga ba, sai Shaixan ya ce: Madallah! Yau kam munsami wurin kwana. Idan kuma mutum bai ambaci sunan Allah ba a lokacin da zai fara cin abinci, sai Shaixan ya ce: Yauwa! Mun sami abin kalacin dare.”  (Muslimu:2018).

brightness_1 Godiya ga Allah Maxaukakin Sarki bayan qare cin abinci

Hujja a kan wannan Sunna:

Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Anas xan Maliku raliyallahu anhu, wanda ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Allah Maxaukakin kan yarda da bawansa, ya kuma amince da shi, saboda xai ya ci ya qoshi ya kuma gode masa a kan haka, ko ya sha ya qoshi ya kuma gode masa a kan haka.”  (Muslimu:2743).

Godiyar nan kuma, tana da sigogi daban-daban, da suka haxa da:

a) “Alhamdu lilláhi kasíran xayyiban mubárakan gaira makfíyin, walá muwadda’in, walá mustagnan anhu Rabbaná!” (Godiya mai tarin yawa, da tsarki, da albarka, ta tabbata ga Allah. Sarkin da ba shi da bukata ga wani abin halitta, babu kuma wani abin halitta da ba shi da bukata gare sh, ko wadatuwa daga gare shi, ya   Ubangijinmu!)

b) “Alhamdu lilláhillazí kafáná wa’arw’aná gaira makfíyin walá mukafúrin.” ((Godiya ta tabata ga Allah, Sarkin da ya qosar da mu, ya kuma kashe mana qishirwa; ba tare dam un raina ko mun kafirce ba.) (Buhari:5459).

A qarqashin inuwar wannan “rashin bukata’  ga wani mahaliki ne, sifa wadda da Allah Maxaukakin Sarki ya kevanta da ita, yake ciyar da bayinsa ya kuma qosar da su. Saboda haka babu yadda za a yi su iya “wadatuwa” daga gare shi subhanahu wa ta’alah,  a matsayinsa na Sarkin da yake “Qosarwa”  da “Kashe musu qishirwa.”  Saboda haka ba za su zama daga cikin masu “kafirce wa”  falala da ni’imarsa ba subhanahu wa ta’alah.

 

brightness_1 Yaba abinci idan ya yi daxi

Sunna ce idan musulmi ya ci abinci, ya kuma ji ya yi masa daxi, ya yaba. Amma, kada ya wuce wuri ta hanyar qara wa kalmomin yabon nasa gishiri fiye da abin da abinci yake xauke da shi.

Hujja a kan wannan Sunnan, ita ce: Hadisin Jabiru xan Abdullahu raliyallahu anhu, cewa, wata rana Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya nemi iyalan gidansa su ba shi rovvi ya haxa da gurasa ya yi kalaci. Sai suka gaya masa cewa: “Rovvi kam ya qare, amma a kwai sauran rummace.” Sai ya ce, a kawo masa shi. Aka kuwo, ya mayar da hankali yana haxa gurasar nan das hi, yana lankahewa baka, yana kuma cewa: “Kai! rovvi da gurasa akwai daxi! Kai! rovvi da gurasa akwai daxi!!” (Muslimu:2052). Kalimar ‘khallu’ ta Larabci da muka fassara da ‘rovvi’ a cikin wannan Hadisi, wani nau’in mahaxin cin abinci ne a waccan zamani, mai daxin gaske, ba kuma mai nauyi da kabri ba kamar wanda muke da shi a yau.

Malaminmu Ibn Usaimin rahimahullahu ya ce: “Yaba abinci da Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yake yi idan ya burge shi, wata koyarwa ce tasa sallallahu alaihi wa sallam zuwa ga al’umarsa. Sadoda haka, yau da mutum zai yi kalaci da waina, ta ratsa shi iyakar zarafi. Sai ya kayar da baki ya ce: “Kai! wainar gidansu wance akwai daxi.”  Ko wani abu mai kama da haka. wanda duk ya yi irin haka, ya raya Sunna daga cikin Sunnonin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. Don qarin bayani sai a duba: “Sharhu Riyádhus- Sálihína: 2/1057)

Duk wanda ya kalli yanayin rayuwarmu na yau da kyau, zai fahimci irin yadda mutane suke yin nesa-nesa da Sunnanr Annabi sallallahu alaihi wa sallam. Wasu ma ba su tsaya a kan yin nesa-nesa da ita xin ba, har sava mata suke yi, ta hanyar aibanta wani abinci da suka ci, tare da kushe shi a wasu lokuta. Irin haka kuwa ya sava wa Sunna da koyarwar Annabi sallallahu alaihi wa sallam. Alhali kuwa, ya zo a cikin ingantattun littafan Hadisai guda biyu, daga cikin Hadisan Abu Huraira raliyallahu anhu, wanda ya ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam bai tava buxa baki ya kushe wani abinci ba. In dai ya ji yana sha’awarsa zai ci. Idan kuma ba ya sha’awarsa zai bar shi baki alaikum.” (Buhari:3563/ Muslimu:2063).

 

brightness_1 Mustahabbi ne idan mutum ya gama shan wani abu, ya fara miqa wa wanda yake dama gare shi kafin wanda yake haxu

Abin da ake nufi shi ne, yana daga cikin Sunna, a daidai lokacin da mutum ya qyanqyami wani abin shay a qoshi. To, idan ya xauke kansa daga kwatarnen, ya gaggauta miqa wa mutumin da yake dama gare shi, kafin wanda yake haxu gare shi.

Hujja a kan wannan Hadisi, ita ce: Hadisin Anas xan Maliku raliyallahu anhu, wanda ya ce: “Wata rana Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kai baqunci a gidanmu, ya kuma nemi wani xan abin da zai sha. Sai muka kama wata akuya muka tatso masa nononta, sa’nan na haxa masa da rowan rijiyar nan tawa.” Anas ya ci gaba da cewa: “Sai na miqa wa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, ya karva ya kafa kai, ya sha ya qoshi. Duk wannan abu da yake faruwa, Sahabi Abubakar raliyallahu anhu yana zaune hagu ga Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, umar kuma yana dabra da fuskarsa, a  yayin da wani balaraben qauye yake a damansa sallallahu alaihu wa sallam. Qarewarsa take da wuya, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, sai ya, sai Sayyadi Umar raliyallahu anhu ya muma nuna Abubakar raliyallahu anhu ya kuma ce wa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam: “Ga Abubakar nan ya Manzon Allah.” Amma, sai Manzon Allah ya miqa wa Balaraben qauyen nan, ya qyale Abubakar da Umar. Ya kuma qara da cewa musu sallallahu alaihi wa sallam: “A yi dama dai! A yi dama dai!! A yi dama dai!!!”  Anas ya ce: “Yin haka Sunne ne! Yin haka Sunne ne!! Yin haka Sunne ne!!!” (Buhari:2571/ Muslimu:2029).