languageIcon
search
search
brightness_1 Wanke Kowace Gava Sau Uku

Wanki na farko wajibi ne. Shi kuwa na biyu da na uku sunna ne. Ba kuma za a qara a kan wankin nan na uku ba.

Hujja a kan wannan Sunna:

Hujja a kan wannan Sunna ita ce, tabatattar magana a wurin Imamul-Buhari rahimahullahu, daga cikin Hadisan xan Abbas raliyallahu anhuma cewa: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam kan yi arwalla ta hanyar wanke gavovin jikinsa shuxi xaya-xaya.” (Buhari:157). Wata maganar kuma da ta tabbata a wurin Imamul-Buhari xin, daga cikin Hadisan Abdullahi xan zaidu raliyallahu anhu, ita ce cewa: Annabi sallallahu alaihi wa sallam kuma a wani lokacin yakan yi arwallalr shuxi biyu-biyu.” (Buhari:158). Ya kuma tabbata a cikin ingantattun littafan Buhari da Muslimu daga cikin Hadisan Sayyadi Usmanu raliyallahu anhu cewa, Annabi sallallahu alaihi wa sallam, yakan kuma yi arwallar shuxi uku-uku.” (Buhari:159). Saboda haka abin ya fi shi ne yi kamar yadda ya yi sallallahu alaihi wa sallam, wato, xaya-xaya, ko biyu-biyu, ko uku-uku xin. Ko kuma wani lokacin ya ma sassava a cikin arwallal xaya. Wato, kamar ya wanke fuska sau uku, hannuwa kuma sau biyu, qafa kuma sau xaya, kamar yadda ya zo a cikin ingantattun littafan nan na Buhari da Muslimu xin daga cikin Hadisan abdullahi xan Zubairu raliyallahu anhu, a cikin wata riwayar. Don qarin bayani sai a duba littafin: Zadul-Mi’ad (1/192). Sai dai mafi cika da kamalar sifa ga arwalla, shi ne mutum ya yawaita yin wanki uku-uku. Wannan shi ne Sunnar Annabi sallallahu alaihi wa sallam.

 

brightness_1 Karanta Addu’ar da ta zo a Sunnan Bayan Qare Arwalla

Hujja a kan wannan Sunna ita ce abin da aka samo daga Sayyadi Umar raliyallahu anhu, ya ce: Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Babu wani daga cikinku da zai yi arwalla kamar yadda ya kamata. Sa’annan ya karanta: “Ash-hadu an lá’iláha illalláhu, wa anna Muhammadan Abduhú wa Rasúluhú,” (Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa.) Ba zai faxi haka ba,  face an buxe masa qofofin Aljanna guda takwas hayan-hayan, ya shiga ta duk wadda ya ga dama daga cikinsu.” (Muslimu:234) 

Ko kuma abin da ya zo a cikin Hadisin Abi Sa’id raliyallahu anhu-marf”u’an: “Duk wanda ya yi arwallal, ya kuma qare arwalarsa, sa’annan ya karanta: “Subhánakal-láhumma wa bihamdika. Ash-hadu allá iláha illá anta. Astagfiruka wa a túbu ilaika,” (Tsarki ya tabbata gare ka ya Ubangijina! Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai kai. ina neman gafararka, ina kuma tuba gare ka) [face Allah Maxaukakin Sarki ya buga masa hatiminsa mai alfarma] sa’annan a aika da ita zuwa qarqashin al’arshi; ba tare da ta samu wani tasgaro ba har zuwa ranar Alqiyama.” (Nisa’a:147- a cikin Babin Ayyukan Yini da Dare/ Hakim:752- Malam Ibn Hajar rahimahullahu kuma ya kyautata danganensa. Domin qarin bayani sai a duba littafin Natá\ijul-afk”ar: 1/246) Sai dai Malamin ya bayyana cewa, idan cewar da aka yi Hadisin ‘marfú’i’ ne, hakan bat a inganta ba, to, ya zama ‘mauqúfí’  kenan. Sai dai hakan ba zai rage shi da komai ba, saboda hukuncinsu xaya da ‘marfú’i’ xin saboda Hadisi ne shi da babu dammar cece-ku-ce a kansa.