languageIcon
search
search
brightness_1 Nafila raka’a biyu kafin Magriba

Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abdullahi xan Mugaffal raliyallahu anhu, daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam, ya ce: “Ku riqa yin sallar nafila kafin sallar Magariba.” Amm, a karo na uku ya ce: “… ga wanda ya so.”  Sai dai ya faxi haka sallallahu alaihi wa sallam tsoron kada mutane su xauki abin  na yi a kowane lokaci.” (Buhari:1183).

- Haka nan kuma Sunna ce a sallaci raka’a biyu tsakanin kowane kiran salla da iqáma:

Daxa raka’o’in nan biyu na sallar Asuba ne ko sallar Azuhur. To, ya riga yin wata salla ta farilla daga cikin waxannan biyu, kafin yin ta nafila xin, ba sai ya yi ta nafila xin ba; ta farillar ta isar masa.  Kamar dai in yana zaune a cikin Masallaci, sai Ladan ya yi kiran salar La’asar ko Isha’i, to,  Sunna ne ya tashi ya yi nafila raka’a biyu. 

Hujja a kan wannan Sunna:

Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abdullahi xan Mugaffalin raliyallahu anhu, wanda ya ce, Annabi sallallahu alaih wa sallam  ya ce: “Sallah tsakanin kowaxanne kiran biyu Sunna ne.” Sai da ya maimaita wannan magana har sau uku. A cikin ta qarshe ya ce: “Amma ga wanda ya so.” (Buhari: 624/ Muslimu:838).

Ko shakka babu a kan cewa, sallar nafila raka’a biyu kafin sallar Magariba ko tsakanin kowaxanne kiran salla biyu, qarfinsu bai kai na waxanda ake yi tare da sauran sallolin farilla ba. Mutum ya ga dammar wani lokaci, ya qi yi abinsa. Hujja a kan haka kuma ita ce, cewar da Annabi sallallahu alaihi wa salami ya yi amjumlarsa ta qarshe:”Amma ga wanda ya so.” Ya kuma faxi haka ne sallallahu alaihi wa sallam don gudun kada mutane su xauki abin  matsayin wata Sunna mai qarfi.