Wannan wata mahada ce da take kokarin yada shiriyar Manzon Allah (S.A.W) da sunnoninsa. Yayin da ya zamana musulmai suna da bukata mai tsanani ga wani aiki da zai bayyana musu sunnonin Annabi (S.A.W) da zikiransa na yau da kullum, a bisa dalilai ingantattu, tare da hotunan da zasu bayyana komai, sai aka samar da wannan tsari mai suna “Sunan” don a samar da bayanin shiriyar Manzon Allah Muhammad (S.A.W) ta hanya mai sauki, wadda zata taimaki musulmi ya yi ibadarsa ta yau da kullum akan siffa ingantacciya, tare da nisantar bidi’o’in da suka yadu a cikin musulmi a yau. An samar da wannan tsari don yi wa musulmi hidima da yare daban daban, kamar yadda mahadar (Iqtida) take maraba da duk wata fadakarwa ko nasiha ko shawara don kyautata wannan aiki da ci gabansa, ana iya turo sakon ta kan wuraren da aka ware don haka.