brightness_1
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْلَمْتُ وَجْهِي إِلَيْكَ، وَفَوَّضْتُ أَمْرِي إِلَيْكَ، وَأَلْجَأْتُ ظَهْرِي إِلَيْكَ، رَغْبَةً وَرَهْبَةً إِلَيْكَ. لاَ مَلْجَأَ وَلاَ مَنْجَا مِنْكَ إِلاَّ إِلَيْكَ، آمَنْتُ بِكِتَابِكَ الَّذِي أَنْزَلْتَ، وَبِنَبِيِّكَ الَّذِي أَرْسَلْتَ
“Alláhumma aslamtu wajhí ilaika, wa fauwadtu amrí ilaika, wa alja’atu zahrí ilaika, ragbatan wa rahbatan ilaika. Lá malja’a walá manjá illá ilaika. Ámantu bi kitábikallází anzalta, wa bi Nabiyyikal- lazí arsalta.” (Ya Ubangiji! Na miqa fuska gare ka, na kuma damqa al’amarina hannunka, sa’annan na jingina bayana gare ka, ina mai kwaxayin rahama da fargaban azabarka. Babu wata mafaka ko wata matsera, sai zuwa gare ka. Na yi imani da littafinka wanda ka saukar, da Annabinka wanda ka aiko.) [Buhari:247/ Muslimu:2710]…. A qarshen Hadisin, Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Mutum ya yi qoqari wannan addu’a ta zama qarshen abin da zai furta a wannan rana. idan Allah ya karvi rayuwarsa a wannan dare, to, ya mutu a kan aqidar Musulunci.” Imamu Muslimu kuma a cikin tasa riwaya, ya qara da cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya qara da cewa: “Idan kuma ya wayi gari, to, ya wayi gari a cikin alhairi.”
Wannan Hadisi kuma, ya zo da qarin bayani na wata Sunnar, wato: qoqarin ganin ba a qara furta wata kalima ba bayan wannan addu’a kafin a kwanta bacci. Yin haka kuma yana qunshe da wata barrar garavasa; idan an karvi rayuwar mutum a cikin wannan dare, to, ya mutu a kan aqida ta Musulunci; addinin Annabi brahima alaihissalamu, wanda bai tava yi wa Allah Maxaukakin Sarki kishiya ba. Idan kuma an wayi gari yana cikin rayayyu, to, zai sami yalwar arziki da wadata. Wannan addu’a, bakandamiya ce; ta haxa duk abin da waxanda suka gabace ta suka qunsa.
Akwai kuma wani qasaitaccen ‘zikiri’ wanda yake zama sanadin samun qasaitacciyar lada da fafa, wanda Allah Maxaukakin ya yi ni’imsarsa ga mutane. Zikiri, wanda ya kamata mai karatu ya lura da shi, shi ne zikirin nan ya zo a cikin Sahíhul- Buhari daga cikin Hadisan Sahaddad xan Aus raliyallahu anhu, daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam, cewa: “Mafi girma da xaukakar kowane irin istigfari, shi ne mutum ya ce: “Alláhumma Anta Rabbí lá’iláha illá anta. Khalaqtaní, ana abduka, wa ana alá wa’adika mas’taxa’tu. Aúzu bika min sharri má sana’atu, abú’u laka bi ni’imatika, wa abú’u laka bi zanbí. Fagfir lí, fa innaú lá yagfiruz- zunúba illá anta.” (Ya Allah! Kai ne Ubangijina. Babu wani abin bauta da gaskiya sai kai. Kai ka halicce ni, ina nan kuma a kan alqawalin da na xauko tsakanina da kai, gwargwadon ikona. Ina neman tsarinka daga sharrin duk abin da na aikata. Ina godiya gare ka a kan ni’imar da ka yi mani, ina kuma kai qarar zunubaina zuwa gare ka. Ina roqon ka gafarta mani. Saboda babu wanda yake gafarta zunubai sai kai.) Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Duk wanda ya karanta wannan addu’a da rana yana mai imani da ita. To, idan ya mutu a wannan rana, kafin marece, yana daga cikin ‘yan Aljanna. Wanda kuma ya karanta da dareyana mai imani da ita. To, idan ya mutu kafin a wayi gari, yana daga cikin ‘yan Aljanna.” (Buhari:6306).
.......