Sunna ce ga wanda ya yi attishaya ya ce: “Alhamdu lilláhi.”
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abu Hurairah raliyallahu anhu, daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam, ya ce: “Idan xayanku ya yi attishaya, to, ya ce: Alhamdu lilláhi (Godiya ta tabbata ga Allah). Xan’uwansa ko wanda yake kusa da shi kuma, ya ce masa: Yarhamukalláhu (Allah ya yi maka rahama). Idan ya ce masa: Yarhamukalláhu, sai shi kuma ya mayar masa da cewa: Yahdí kumulláhu wa yuslih bálakun (Allah ya shiryar da ku, ya kuma tsarkake zukatanku.). (Buhari:6224).
Haka nan kuma, inda mutum zai canza wanna lafazi wata lokaci, idan ya yi attishaya xin, ce: “Alhamdu lilláhi alá kulli hálin,” Sunna ta fi son haka. Hujja kuwa ita ce, wata riwaya da aka samo daga Abu dawuda, da take cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Idan xayanku ya yi attishaya, to, ya ce: Alhamdu lilláhi alá kulli hálin.” (Abu Dawuda:50311). Malam Ibnl- Qayyim rahimahullahu ya bayyana wannan Hadisi, a cikin: Zádul Mi’ád da cewa: “Danganensa ingantacce ne.”
Shi kuwa wanda yake kusa da mai attishaya xin nan, idan zai yi masa barka da arziki, a Sunnance, sai ya ce: “Yarhamukalláhu (Allah ya yi maka rahama). Shi kuma wanda ya yi attishaya xin, Sunna ta xora masa nauyin karvawa da cewa: “Yahdí kumulláhu wa yuslih bálakun (Allah ya shiryar da ku, ya kuma tsarkake zukatanku.) Hujja a kan gaba xayan waxannan Sunnoni, ita ce, Hadisin Abu Huraira raliyallahu anhu, wanda ya gabata.
Sunna ta ce, idan mai attishaya bai gode wa Allah ba, kada a gaida shi
Idan wanda ya yi attishaya bai yi godiya ga Allah Maxaukakin Sarki ta hanyar cewa: ‘alhadu lilláhi’ ba. To, wanda ya gai da shi, ta hanyar cewa: ‘yarhamukalláhu’ ya yi bidi’a. Abin da yake Sunna a nan, shi ne, kada a ce masa qanzil. Hujja a kana wannan Sunna ita ce, Hadisin Anas raliyallahu anhu, da ya ce: “Wasu mazaje biyu sun yi attishaya a wurin Annabi sallallahu alaihi wa sallam. Sai ya yi wa xaya barka da arziki, bai yi wa xaya ba. jin haka sai xaya daga cikinsu, ya ce: “Ya Manzon Allah! ka gai da wannan, ni kuma ba ka gai da ni ba?” Sai ya karva masa da cewa: “Ai wannan ya yi godiya ga Allah ne, kai kuma ba ka yi ba.” (Buhari:6225). Dama kuma irin haka Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yakan yi; ajiye komai a wurinsa munásibí. Imamu Muslim kuma ya riwaito wata magana tasa sallallahu alaihi wa sallam, daga abu Musa raliyallahu anhu, wanda ya ce, na ji Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Idan xayanku ya yi attishaya, ya kuma gode wa Allah. To, ku yi masa barka da arziki. Idan kuma bai gode masa ba, to, kada ku ce masa qanzil.” (Muslimu:2992).
Amma, idan al’amarin ya shafi karantarwa ne. Wato, tsakanin kamar mahaifi xansa, ko malami da almajirinsa, ko wani yanayi mai kama da waxannan, wanda ake iya bayyanawa da matakin karantarwa. To, sai a gaya wa wanda ya yi attishaya xin, ya kuma kama bakinsa cewa, ce: “Alhamdu lilláhi” mana. Za a gaya masa haka ne, domin a korantar das hi raya wannan Sunna, domin abau ne mai matuqar sauqi, ya zamana bai san haka al’amarin yake ba.
Haka nan kuma wanda yake fama da lalurar ‘mura.’ Ba lalle ne sai ya yi ta faxar ‘alhamdu lillahi’ xin ba duk lokacin da ya yi attishaya. Idan ya yi sau uku yana godiya, ya isa. Saura kuma, ba sai ya ce komai ba.
Hujja a kan wannan Sunna, ita ce: Abin da Abu dawuda ya riwaito a cikin Sunan nasa, daga Abu Huraira raliyallahu anhu- mauqúfan wa marfú’an-, cewa, manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Ka yi wa xan’uwanka barka da arziki har sau uku. Abin day a haura a kan haka kuma, mura ce.” (Abu dawuda:5034) malam Albani rahimahullahu ya ce: “Hadisi ne kyakkyawa, amma, mai gajeren asuli, a wani qauli kuma, mai dogon asuli.” (Sahíhu Abi Dáwuda: 4/308).
Wata hujjar kuma, da take qarfafa wannan, ita ce, abin da Imamu Muslim ya riwaito a cikin ingantaccen littafinsa, daga cikin Hadisan Salmata xan Akwa’in raliyallahu anhu, cewa, ya ji Annabi sallallahu alaihi wa sallam, da wani mutum ya yi attishaya gabanasa, sai y ace masa: “Yarhamukalláhu,”ya kuma sake yin wata. Sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Wannan mutum yana fama da mura ne.” (Muslim:2993).
Abubuwan da suka gabata suna karantar da cewa, akwai waxansu halaye guda biyu, da ba a yi wa mai attishaya barka da arziki a cikinsu:
1/ Idan bai gode wa Allah Maxaukakin Sarki ba.
2/ Idan ya yi attishaya fiye das au uku; ya zama mai mura kenan.
Don Saduwa Da Mu
Da Mu
Muna Farin Ciki Da Samun Kiranka Da Tambayoyinka A Kowane Lokaci