Raya waxannan Sunnoni guda biyu, yana matuqar taimakawa tare da bayar da kariya daga miyagun Aljannu da fanxararrun Shaixanu. Idan aka kankamta yara qanana a daidai farkon lokacin sallar Magariba, hakan zai zama wata kariya gare su, daga miyagun Shaixanun da suke kaiwa da komowa a daidai wannan lokaci. A yayin da shi kuwa rufe qofofi tare da ambaton Allah maxaukakin Sarki a lokaci da ake rufewar, hakan yake zama wani irin magani ga yaro da xakin da Shaixanu suka riga suka kai wa hari a daidai wannan lokaci. Kai ka san dai Musulunci ya yi matuqar kula da yara da kuma xakunanmu, kula irin wadda babu irinta.
Hujja a kan wannan Sunna:
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Jabir xan Abdullahi raliyallahu anhuma da ya ce: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Idan marece ya yi; dare ya kusa kawo jiki, ku kankamta yaranku qanana, saboda a lokacin ne Shaixan yake baje kolinsa. Bayan awa xaya kuma a cikin dare, sai ku sake su, ku kuma rurrufe qofofinku, sa’annan ku ambaci sunan Allah. Babu yadda za a yi Shaixanu su iya buxe qofar duk da aka rufe da sunan Allah.” (Buhari:3304/ Muslimu:2012).
Shi kankamta qananan yara xin nan, da ruxe qofofin xakuna, da magriba Sunna ce ta mustahabbi. Don qarin bayani ana iya duba: Fatáwá Lajnatud- Dáimah’ (26/317).
Rufe qofofi farkon almúru da ambaton Allah ta’alah

Nafila raka’a biyu kafin Magriba
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abdullahi xan Mugaffal raliyallahu anhu, daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam, ya ce: “Ku riqa yin sallar nafila kafin sallar Magariba.” Amm, a karo na uku ya ce: “… ga wanda ya so.” Sai dai ya faxi haka sallallahu alaihi wa sallam tsoron kada mutane su xauki abin na yi a kowane lokaci.” (Buhari:1183).
- Haka nan kuma Sunna ce a sallaci raka’a biyu tsakanin kowane kiran salla da iqáma:
Daxa raka’o’in nan biyu na sallar Asuba ne ko sallar Azuhur. To, ya riga yin wata salla ta farilla daga cikin waxannan biyu, kafin yin ta nafila xin, ba sai ya yi ta nafila xin ba; ta farillar ta isar masa. Kamar dai in yana zaune a cikin Masallaci, sai Ladan ya yi kiran salar La’asar ko Isha’i, to, Sunna ne ya tashi ya yi nafila raka’a biyu.
Hujja a kan wannan Sunna:
Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Abdullahi xan Mugaffalin raliyallahu anhu, wanda ya ce, Annabi sallallahu alaih wa sallam ya ce: “Sallah tsakanin kowaxanne kiran biyu Sunna ne.”Sai da ya maimaita wannan magana har sau uku. A cikin ta qarshe ya ce: “Amma ga wanda ya so.” (Buhari: 624/ Muslimu:838).
Ko shakka babu a kan cewa, sallar nafila raka’a biyu kafin sallar Magariba ko tsakanin kowaxanne kiran salla biyu, qarfinsu bai kai na waxanda ake yi tare da sauran sallolin farilla ba. Mutum ya ga dammar wani lokaci, ya qi yi abinsa. Hujja a kan haka kuma ita ce, cewar da Annabi sallallahu alaihi wa salami ya yi amjumlarsa ta qarshe:”Amma ga wanda ya so.”Ya kuma faxi haka ne sallallahu alaihi wa sallam don gudun kada mutane su xauki abin matsayin wata Sunna mai qarfi.
Karhancin kwana kafin sallar Isha’i
Hujj a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin Barzata xan Aslamí raliyallahu anhu, wanda ya ce: Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yana son ganin an jinkirta sallar Isha’i. Ya qara da cewa: “Yana kuma qyamar a yi kwana kafin ta, ko zaunawa hira bayan ta.” (Buhari:599/ Muslimu:647).
Baban dalilin kuma day a sa Sunna ta qyamaci yin kwana bayan sallar magariba, wato, kafin sallar Isha’ai, duk bai fi yiwuwar zaman hakan dalilin rasa samun sallar Isha’i ba.
Don Saduwa Da Mu
Da Mu
Muna Farin Ciki Da Samun Kiranka Da Tambayoyinka A Kowane Lokaci