Mun riga mun yi bayani a baya, a kan Sunnonin da suka shafi lolutan sallolin farilla, inda muka ga cewa, babu wata nafila ake yi kafin sallar La’asar
Hujja a kan haka kuwa ita ce, maganar Ibn Taimiyyah rahimahullahu da ya ce: “Amma kafin sallar La’asar, babu wanda ya riwaito wata ingantattar magana, cewa, Annabi sallallahu alaihi wa sallam yakan yi wata sallar nafila a ciki. Duk riwayoyin da suka ce yana yi, masu rauni ne. Mafi yawansu ma cike suke da kurakurai.” Don qarin bayani, sai a duba: Alfatáwá:23/125.”
Allah shi ne mafi sani: Amma dai ingantattar magana ita ce, babu wata salla ta nafila takamaimai, da Sunna ta yi umarni da a yi kafin wannan salla ta La’asar. Saboda haka, sai daia a bar al;amarin haka nan buxe; wanda ya ji yana da bukatar yi nafilar, yana iya yin raka’a biyu, ko fiye da haka, bisa la’akari da cewa, wannan ba lokaci ne da aka haramta yin wani aiki na taxauwu’í ba. Zai yi haka ne kamar yadda zai iya yin sallar nafila a sauran lokutan waxanda ban a haramci xin ba. Amma, kamar yadda aka ambata a sama kaxan, babu wani abu takamaimai day a shafi wannan, da aka qayyade wa wannan lokaci na kafin sallar La’asar.
Don Saduwa Da Mu
Da Mu
Muna Farin Ciki Da Samun Kiranka Da Tambayoyinka A Kowane Lokaci