languageIcon
search
search
brightness_1 Mafi girma da xaukakar zikiri kuwa, shi ne: Karatun Littafin Allah Maxaukakin Sarki

Mafi girma da xaukakar zikiri kuwa,  shi ne: Karatun Littafin Allah Maxaukakin Sarki, Alqur’ani. Saboda haka ne Littafin yake hana idanun magabata na gari runtsawa cikin dare, tare da qaurace wa shimfixunsu. Tabbacin wannan kuwa shi ne faxar Allah Maxaukakin Sarki: “Sun kasance kaxan daga cikin, suke runtsawa. A lokutan Asuba kuma, suna ta yin istigfari.” {zariyat:117-18}. Kenan, a cikin dare babu abin da suke yi sai karatun littafin Allah Maxaukakin Sarki, da sauran zikirora irin waxanda aka riwaito daga Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. Kai! madalla da irin wannan dare, wanda babu abin da yake faranta wa irin waxannan bayin Allah rai, illa su raya shi. Mu kuwa dab a mu damu da raya darare da lokutan Asuba xin mu da irin waxannan ibadoji ba, babu shakka mun yi babbar hasara, mun kuma tave. Babu abin da ya dace da mu, sai jaje da tanzanko. In ma waxannan lokuta sun tsira daga cika su da savon Ubangijinmu, to, mun yi sa’a. Ba kuwa kowa ne daga cikinmu yake samun irin wannan sa’a ba. sai wanda ya yi gamon katari da rahama da jinqayi irin na Allah Maxaukakin Sarki.

Hujja a kan wannan Sunna kuwa ita ce, abin da aka riwaito daga Hammad xan Zaidu, daga Axa’u xan Sab’ibin, cewa, Aba Abdar- Rahman ya ce: “Mutanen da muka gadi Alqur’ani daga hannuwansu, sun ba mu labarin cewa, sun kasance idan suka karanci aya goma daga cikinsa, ba za su qara gaba zuwa ga waxansu ayoyi goma ba, sai sun aikace abin da yake qunshe a cikin waxannan. Mun kuma muka wayi gari muna xaukar darasin karatun Alqur’ani xin da kuma aiki da shi. To, na gaba kaxan wasu mutane za su gadi Alqur’ani daga hannuwanmu, da za su riqa shan sa kamar yadda ake shan ruwa; bay a wuce maqogarinnensu.” Don qarin bayani sai a duba: “Siyaru A’alámin- Nubalái: (4/269).

 

brightness_1 Wuraren da Allah Maxaukakin Sarki ya kwaxaitar da a ambace shi a cikinsu, suna da yawa

Wuraren da Allah Maxaukakin Sarki ya kwaxaitar da a ambace shi a cikinsu, suna da yawa. Ga kaxan daga cikinsu:

1/  Allah Maxaukakin Sarki ya kwaxaitar da bayinsa muminai a kan yawaita ambatonsa, da cewa: “Yak u waxanda suka yi imani! ku ambaci Allah, Ambato mai yawa. Ku kuma tsarkake shi, safiya da marece.” {Ahzab:41-42}.

2/ Allah Maxaukakin Sarki ya yi wa masu ambatonsa, maza da mata, alqawalin gafara da lada mai tarin yawa, da cewa: “Da masu ambton Allah maza, da masu ambaton Allah mata. Allah ya yi musu tanadin gafara da lada mai girma.” {Ahzab:35}.

3/ Allah Maxaukakin Sarki ya yi mana kashedi da hali irin na munafukai; suna ambatonsa Maxaukakin Sarki, amma da walákin. Allah Maxaukakin Sarki ya bayyana irin nasu ambaton da cewa: “Haqiqa, munafukai suna yaudarar Allah ne, Shi kuwa yana mayar musu da sakamakon yaudararsu. Idan suka tashi zuwa salla, sai su tahsi cikin kasala; don kawai mutane su gani. Ba su kuma ambaton Allah sai kaxan.” {Nisa’i:14}.

4/  Allah Maxaukakin Sarki ya yi mana kashedi da shagaltuwa da dukiya, da ‘yaya, tare da yin ko oho da ambaonsa Maxaukakin Sarki, ya ce: “Ya ku waxanda suka yi imani! Kada dukiyoyinku, da ‘ya’yanku su shagaltar da ku daga ambaton Allah. Duk wanda ya aikata haka, to, waxannan suna daga ciki masu hasara.” {Munafiqun:9}.    

5/  Yana da kyau kowane musulmi ya kalli muhimmanci da girman da ambaton Allah Maxaukakin Sarki yake da shi a wurinsa, hard a ya ce: “Ku ambace ni, in ambace ku.”  ya kuma ce a cikin Hadisi Qudusí: “Ina nan inda bawana yake zatona. Ina kuma tare da shi, idan ya ambace ni. idan ya ambace ni a cikin ransa, zan ambace shi a cikin raina. Idan kuma ya ambace ni a cikin wata jama’a, zan ambace shi a cikin jama’ar da ta fi wannan girma da xaukaka.”  (Buhari:7405/ Muslimu:2675), daga cikin Hadisan Abu Huraira raliyallahu anhu.

 

brightness_1 Nau’ukan zikiri kuma, waxanda suka zo a cikin Sunnar Annabi suna da yawa. Ga kaxan daga cikinsu:(1)

Nau’ukan zikiri kuma, waxanda suka zo a cikin Sunnar Annabi sallallahu alaihi wa sallam suna da yawa. Ga kaxan daga cikinsu:

1. An samo daga Abu Hurairah raliyallahu anhu cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Duk wanda ya ce: Lá’iláha illalláh wahdahú lá sharíka lahú. Lahul- hamdu wa lahul- mulku wa huwa alá kulli shai’in qadír.(Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai shi ke; ba shi da abokin tarayya. Mulki da godiya sun tabbata gare shi. Mai kuma iko ne shi a kan duka komai.) Duk wanda ya karanta wannan zikiri sau xari safiya da marece. To, za a rubuta masa ladar wanda ya ‘yanta kuyanga goma, a kuma rubuta masa ladar kyakkyawan aiki goma, a kuma shafe masa zunubin mummunan aiki goma. Za ta kuma zama katangar qarfe tsakaninsa da Shaixan a tsawon wannan rana, har zuwa marece. Babu kuma wanda ya yi wani aiki fiye da nashi a wannan rana, sai wanda ya faxi hiyaka da abin da ya faxa. Duk kuma wanda ya karanta: “Sunhanalláhi wa bi hamdihi” (Tsarki ya tabbata ga Allah, tare da godiya a gare shi.) Duk wanda ya karanta wannan zikiri qafa xari, to, an gafarta masa gaba xayan zunubansa, ko sun kai yawan kumfan teku.” (Buhari3293/ Muslimu:2691).

2. An kuma samo daga Abi Ayyuba raliyallahu anhu, wanda ya ce: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: ““Duk wanda ya ce: Lá’iláha illalláh wahdahú lá sharíka lahú. Lahul- hamdu wa lahul- mulku wa huwa alá kulli shai’in qadír.(Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai shi ke; ba shi da abokin tarayya. Mulki da godiya sun tabbata gare shi. Mai kuma iko ne shi a kan duka komai.) Duk wanda ya karanta wannan zikiri qafa goma. To, za a rubuta masa ladar wanda ya ‘yanta bawa huxu daga cikin jikokin Annabi Isma’ila.” (Buhari:6404/ Muslimu:2693).  

brightness_1 Nau’ukan zikiri kuma, waxanda suka zo a cikin Sunnar Annabi suna da yawa. Ga kaxan daga cikinsu:(2)

Nau’ukan zikiri kuma, waxanda suka zo a cikin Sunnar Annabi sallallahu alaihi wa sallam suna da yawa. Ga kaxan daga cikinsu:

3. An kuma samo daga Sa’id xan Abi Waqqas raliyallahu anhu, wanda ya ce: “Wata rana muna wurin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, sai ya ce: “Ya za a yi xayanku ya kasa cin nasarar samun ladar kyakkyawan aiki dubu a kowace rana?”  Sai wani daga cikin waxanda suke zaune a wurin ya tambaye shi: “Ya kuwa za a yi xayanmu ya iya cin nasarar samun ladar kyakkyawan aiki dubu a kowace rana? Sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya karva masa da cewa: “Idan xayanku ya yi tasbihi xari, to, za a rubuta masa ladar kyakkayawan aiki dubu xaya, ko a shafe masa zunubi dubu.”  (Muslimu:2697).

3. An kuma samo daga Abu Hurairah raliyallahu anhu, cewa, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: Duk kuma wanda ya karanta: “Sunhanalláhi wa bi hamdihi” (Tsarki ya tabbata ga Allah, tare da godiya a gare shi.) Duk wanda ya karanta wannan zikiri qafa xari a yini, to, an gafarta masa gaba xayan zunubansa, ko sun kai yawan kumfan teku.” (Buhari:6405/ Muslimu:2692). A cikin wata riwaya kuma ta Imamu Muslimu, cewa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya yi: “Duk kuma wanda ya karanta: “Sunhanalláhi wa bi hamdihi” (Tsarki ya tabbata ga Allah, tare da godiya a gare shi.) Duk wanda ya karanta wannan zikiri qafa xari, a lokacin day a wayi gari ya kuma maraita. To, babu wanda zai zo da wani aiki a ranar Qiyama, da ya fi wanda ya je da shi girma da xaukaka, sai wanda ya faxi daidai abin day a faxa xin nan, ko fiye da shi.”  (Muslimu:2692).

Hadisan da suke magana a kan nau’ukan zikirora daban-daban suna da yawa matuqa. Waxannan da muka ambata a sama, su ne mafi shahara da inganci daga cikin zikiroran da suke da falala. Amma, akwai wasu masu yawa da daman gaske da aka riwaito a Sunna, waxanda ba waxannan ba. Tabbacin hakan kuwa shi ne, abin da aka riwaito daga Abu Musa Al’ash’arí raliyallahu anhu, da ya ce: “Wata rana Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce mani: “Ko kana son in nuna maka wata taska daga cikin taskokin Aljanna?”  Sai na ce masa: Eh!. Sai ya ce: “Ka ce: Lá haula walá quuwata illá billáh.”  (Buhari:4202/ Muslim:2704).

An kuma samo daga Abu Hurairah raliyallahu anhu, wanda ya ce: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “In buxa baki in faxi: Sybhanalláhi, wal hamdu lilláhi, wa lá’iláha illalláhu, walláhu akbar.” (Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya kuma ta tabbata ga Allah, babu kuma abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah kuma shi ne mai girma). In buxa baki in faxi waxannan kalmomi, ya fiye mani duniya da abin duk da yake cikinta.” (Muslimu:2695).

brightness_1 Nau’ukan zikiri kuma, waxanda suka zo a cikin Sunnar Annabi suna da yawa. Ga kaxan daga cikinsu:(3)

Haka nan shi ma istigfári yana da sigogo da dama. An riwaito daga Agarrin Almuzní raliyallahu anhu, wanda ya ce, Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Tabbas! babu rayayyar zuciya kamar tawa. Saboda babu ranar dab a na neman gafarar Allah sau xari.”  (Muslim:2702).

Da ma haka Manzon Allah  sallallahu alaihi ya saba, wato karantarwa a cikin hikima, tare da bayyana wa duniya yadda yake waxansu ibadoji domin a koya, kamar yadda ya kayar da neman gafarar Allah a cikin wannan Hadisi. Akwai kuma wata riwayar a cikin ingantaccen littafin Muslimu, wadda aka samo daga shi Agarrin xin xan Almuní raliyallahu anhu, wanda ya kuma ce, Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Yak u mutane! Ku tuba zuwa ga Allah, domin tabbas! ni, ina tuba gare shi sau xari a kowace rana.”  (Muslimu:2702).

Wata riwayar kuma ta Buhari, aga cikin Hadisan abu Huraira raliyallahu anhu, wanda ya ce: “Na ji Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Wallahi! Ni xin nan da kuke gani, nakan nemi gafarar Allah, in kuma tuba zuwa gare shi fiye das au sabain a cikin yini xaya.”  (Buhari:6307/). Saboda haka ya kamata ga kowane bawa na Allah, ya mayar da hankali ga raya wannan Sunna ta yawaita istigfari.

A nan ne kuma zan dasa aya a cikin zancen Zikiri da Sunnoninsa, da kuma sauran Sunnonin yau da kullum. Zan rufe waxannan darussa ne da kawo wani qasaitaccen zikiri, wanda yake a cikin ingantattun littafan Buhari da Muslimu. Wato, Hadisin Abu Hurairah raliyallahu anhu, wanda ya ce, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Akwai waxansu kalmomi guda biyu,masu sauqin faxi ga halshe, masu kuma nauyi a kan mizani, sa’annan masu tsananin matsayi a wurin Allah. waxannan kalmomi su ne: Subhánalláhi wa bi hamdihí, Subhánalláhil- azim.” (Tsarki da godiya sun tabbata ga. Tsarki ya tabbata ga Allah mai girma.) (Buhari:6406/ Muslimu:2694).

Godiya ta tabbata ga Allah, Sarkin da said a yardarsa ne duk wani aiki na qwarai yake kammala.