brightness_1
Duk kuma wanda ya yi mummunan mafarki, ta hanyar ganin wani abu da ba ya so, ba ya kuma qauna. Shi kuma a sunnance, ana so ya aikata abubuwa kamar haka
Abin da Sunna ta yi tanadi a wannan babi shi ne abin day a zo a cikin wannan Hadisi:
An samo daga Abu Salma raliyallahu anhu, ya ce: “Da yawa nakan yi mafarkin da zai xaga mani hankali, ya ce: Har wata rana na haxu da Abu Qatadah, shi ma y ace yakan yi irin wannan mafarki mai xaga hankali. Ana nan kuma sai na ji Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Kyakkyawan mafarki daga Allah yake zuwa. To, idan xayanku ya yi mafarkin wani abu da yake so, kada ya labarta wa kowa shi, sai masoyinsa. Idan kuma ya yi wani mafarkin na abin da yake qi da qyama. To, sai ya yi toshi a vangarensa na hagu har sau uku, sa’annan ya nemi tsarin Allah Maxaukakin Sarki daga sharrin Shaixan da na mafarkin. Sa’annan kuma kada ya ba wa kowa labarinsa. Idan ya yi haka, ba zai cutar da shi da komai ba.
Abu Salmah ya ce: “da yawa na kan yi mafarki, in ji kamar ina xauke da abin da ya fi dutsi nauyi saboda damuwa. Ana nan cikin haka, sai na ji wannan Hadisi. Tun daga wannan lokaci ban qara kulawa da shi ba.” (Buhari:5747/ Muslimu:2261). A cikin wata riwayar kuma aka ce, cewa Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya yi: “Kyakkyawan mafarki daga Allah yake zuwa, shi kuwa mummunan mafarki daga Shaixan yake. Saboda haka, idan xayanku ya yi mummunan mafarki, wanda ya xaga masa hankali. To, sai ya yi tohi a vangarensa na hagu, sa’annan ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa. Ko shakka babu, idan ya yi haka, ba zai cutar da shi da komai ba.” (Buhari:3292/ Muslimu:2261).
A cikin Hadisin Jabir raliyallahu anhu kuma, wanda Muslimu ya riwaito, cewa aka yi, manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “… mutum ya nemi tsarin Allah daga Shaixan har sau uku. Sa’annan ya juya kwanci.” (Muslimu:2262).
A cikin Hadisin Abu Sa’id Alkhudrí raliyallahu anhu kuma aka ce, cewa Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya yi: “Idan xaya daga cikinku ya yi mafarkin abin da yake so, to, ya sani, ko shakka babu, da Allah Maxaukakin Sarki ne. saboda haka sai ya gode wa Allah Maxaukakin Sarki a kan haka.” (Buhari:7045).
Gaba xayan Hadisan da suka gabata, suna karantar da mu ne, cewa: Duk kuma wanda ya yi mummunan mafarki, ta hanyar ganin wani abu da ba ya so, ba ya kuma qauna. Shi kuma a sunnance, ana so ya aikata abubuwa kamar haka:
Na farko: Yin tohi a vangarensa na hagu har sau uku.
Na biyu: Neman tsari ga Allah Maxaukakin Sarki daga sharrin Shaixan da sharrin abin da ya gani a cikin mafarkin, har sau uku, ta hanyar cewa: “Aúzu billáhi min sharrish- Shaixáni wa min sharrihá.” (Ina neman tsari ga Allah daga sharrin Shaixan da sharrin wannan mafarki), har sau uku.
Na uku: Kada ya labarta wa kowa wannan mafarki. Idan ya kiyaye wannan qa’ida, to, mugun abin duk da yake cikin wannan mafarki ba zai cutar da shi, da komai ba, kamar yadda Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya bayar da labara. Idan ya tsaya a kan waxannan sharuxxa guda uku, sun wadatar. Idan kuma ya qara da na huxu, da na biyar, babu laifi, wato:
Na huxu: Juya kwanci ta hanyar barin sashen jikin da yake kwance a kansa ya koma kan xayan sashen. Idan kuma yana kwance ne rairan, to, sai ya koma a kan xayan sashen jikinsa. Haka haka dai; abin da ake so shi ne ya juya kwanci.
Na biyar: Ya tashi ya yi sallar nafila raka’a biyu rak.
Waxannan Hadisai da suka gabata, suna karantar da cewa: Mafarki duk da Musulmi zai yi, wani yanki ne na Annabta; tazarar da take tsakaninsu ba wani tsawo ne da ita ba. Duk kuma mutumin da ya fi kowa faxin gaskiya da rana, shi ne wanda mafarkinsa zai fi na kowa zama gaskiya. Wannan kuwa yana daga cikin tasiri da albarkar da gaskiya take da su a rayuwar musulmi, har a cikin bacci.