brightness_1
Jinkirta sallar Azuhur saboda zafin rana
Hujja a kan wannan Sunna:
Hujja a kan wannan Sunna ta jinkirta sallar azuhur saboda zafin rana, har zuwa lokacin da ya rage kaifi, ita ce, Hadisin Abu Hurairah raliyallahu anhu- marfú’í, cewa: “Idan zafin rana ya tsananta ku kirdadi lokacin da take da sanyi, ku yi salla cikinsa. Saboda tsananin zafin rana daga numfashin Jahannama ne.” (Numfashin Jahannama yana watsuwa ne tare da cika duniya, sakamakon irin yadda take vavvaki das akin dogayen halsunanta.) [Buhari:533,534/ Muslimu:610].
Malaminmu Malam Usaimin rahimahullahu ya ce: “Idan muka qaddara, a misalce, cewa rana a lokacin bazaar tana barin tsakiyar samaniya daidai qarfe goma sha biyu. A yayin ita kuwa sallar La’asar tana kamawa kusan qarfe huxu da rabi. To, lokacin da ya kamata a kirdada, na sanyi ga sallar La’asar xin nan, shi ne misalign qarfe huxu.” Don qarin bayani sai a duba: “Al-mumti’u:2/104”.
Wannan Sunna ta kirdadon lokacin sanyin rana domin yin salla, dama ce da shari’ah ta ba wa mai yin salla shi kaxai, da masu yin ta cikin jam’i, bisa ingantaccen zance. Wannan matsayi kuma shi, Malaminmu Ibn Usaimin rahimahullahu ya rayu ya kuma mutu a kai. Bisa wannan ma’auni kuma, har mata sun shiga ciki. Su ma Sunna tana son, duk sallar da za su yi, su kirdadi sanyin rana. Dalili kuwa shi ne yadda wannan hukunci ya taho ba tare da wata togiya ba, a cikin Hadisin Abu Hurairah raliyallahu anhu.